TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Ga kuma problem din Ruqayyah. Duk da wani bangare na zuciyarsa wanda yake cike da sonta kullum yana yi mata uzuri amma kaso mafi yawa na tunanin sa yafi karkatuwa ga karbar gaskiyar magana. Gaskiyar magana kuma shine bai yi dace da mace ta gari ba. Lokuta da dama yakan samu kansa da tambayar kansa shin ina wannan Hassanar daya aura take? Anya ba’a chanja masa da wata ba kuwa? Ina wannan karamar yarinyar nan data dora rayuwarsa a saman tata ta ceto shi daga bakin bindiga take, ina yarinyar nan yar gidan malamai mai cike da tarbiyya, kunya da ilimin addini? Ina yarinyar da bata saba da kyale kyalen duniya ba? Dan yasan ba ita bace wannan wadda last week ta hana masa sakat a gidan sa da mitar Hussain ya sake wa Fatima mota ita banda ita ba, dan waccan yarinyar babanta ko keke bashi dashi.
Yanzu gidan sa ya koma abin gudu a gurinsa, wannan yasa kullum yana office, har weekend zuwa yake yi yayi ta aiki shi kadai musamman tunda yanzu Hussain ya tattara harkar kamfanin yayi watsi da ita. Shi kuma sai ya dauki aikin yake tayi da iya kacin karfinsa dan yana so ya rage wa kansa tunani kuma ya nesanta kansa da fada da kuma mitar Ruqayyah. Yau ma kafin ya fito sai data saka shi a gaba da zancen tana son ya bata kudi ta tafi Dubai siyayyar haihuwa.
Hussain yana komawa gida yayi wa Fatima alkawarin ta lissafa masa dream countries din da take son zuwa a rayuwarta shi kuma zai kaita. Ta bude baki cikin murna “lah! Na dauka yanzu baka son fita” yace “yanzu ina so, so nake mu fita mu samu good quality time daga ni sai ke sai baby” ai kuwa nan take ta fara lissafa masa duk inda take son zuwa, shi kuma ya ware wasu kudade masu kyau daga cikin personal kudinsa ya fara shirya musu tafiyar. Kafin wani lokaci komai ya kammala, suka shirya suka tafi and they spent the best days of their lives together. A lokacin ne ciwon Hussain yafi karfin drugs din da ya ke sha har Fatima ta fara fahimtar bashi da lafiya, amma sai ya gaya mata cewa ulcer ce take damunsa, ta nemi suje asibiti sai ya shiga drug store kawai ya siyi magani ba tare da ya bari an wani do ba shi sosai ba. A lokacin ne labarin haihuwar Ruqayyah ya same su, ta haifi danta namiji kuma kowa ya kira sai ya gaya musu irin tsananin kamar da yaron yake yi da Hussain. Kuma Hassan ya rada masa suna Hussain duk da cewa bashi da abokin tagwaitaka. Wannan yasa hankalinsu kuma yayo gida dan itama Fatima nata cikin ya kai wata bakwai kenan, tace “naga alama dai gidan nan sai maza ake ta haifa, ni kam nafi son mace dan ta zama kawata amma ko namijin nema ina sonsa shima”.
Hussain shima ba wai ya damu da lallai sai namiji ba, kawai dai yana ganin kamar namijin zai fi jan nasabarsa sosai akan mace, tunda ita mace in tayi aure ta haihu yayanta da gidan baban su zasu yi tutiya ba da shi ba, amma a yanzu yadda yake jin ya matsu yaga abinda zai haifa ko macen cema yana so sosai. Sai suka shirya dawowa Nigeria dan ayi sunan takwaran Hussain dasu, kafin su taho sai Hussain ya dauke ta zuwa asibiti inda ya nemi ayi musu 4d scan na babyn cikinta. Tayi ta mamakin dalilinsa nayin hakan bayan da yace ko gender baya son sani, ta tambayeshi dalili sai yace “I changed my mind, ina tsananin son ganin abinda yake cikin ki ko da a hoto ne” ita bata taba sanin cewa 4d pregnancy scan is possible ba sai yau, lallai technology babu abinda ya bari rai ne kawai Allah bai bawa turawa ikon hurawa jiki ba, babyn da yake kwance a cikinta sai gashi suna ganinsa clearly a jikin screen a kwance a cikin amniotic fluid yana ta tsotsar hannunsa, idanuwan sa tar a bude. Ba sai Doctor ya gaya musu ba su da kansu suka gani cewa namiji ne, ta juyo da sauri ta kalli Hussain sai taga hankalinsa yana kan screen din yana kallon babyn, and she saw a tear in his eyes but sai yayi sauri ya mayar da ita a hankali yace “bai yi miki kara ba, kamar mu daya” ta turo baki “ai dama hada baki kuke yi kullum in kana yi masa hira, a lokacin kukayi meeting kuka ware ni” ya danyi dariya, tace “amma ai kalar fata ta ce dashi, bai kai ka haske ba” yace “waya gaya miki? ai hoton black and white ne kuma yayi duhu ba zaki gane kalar fata ba”.
Sun jima suma kallon babyn su for 30 minutes wanda shine medically advisable sannan aka kashe, Hussain yaji kamar an kashe wani part na zuciyarsa ya daina amfani, sai dai kawai jin dadin sa shine an musu record na scan din a CD aka basu. At least ya samu abin gani kafin babyn yazo, that’s in babyn zai zo ya tarar da shi.
Kwana biyu bayan nan suka dauki hanyar Nigeria. Suna sauka suka je suka ga jaririn Ruqayyah, Fatima tana jin kamar ta sace shi saboda kamannin da taga yana yi da Hussain.
Bayan an kammala suna ne Hussain ya koma Abuja gurin Doctor din da yake dubashi yayi requesting ya bashi wasu magungunan da suka fi wadancan karfi, amma sai Doctor din ya nuna masa cewa babu sama da wadannan, from kallon da Doctor din yake yi masa yasan cewa lokacin da ya rage masa bashi da yawa, amma sai yaji har cikin zuciyarsa baya jin tsoro kawai dai yana bakin cikin rabuwa da masoyansa ne. A ranar bayan ya koma gida ya dauko diary dinsa wanda har ya kusa cika shi da rubutu ya rubuta..
Dear baby
Duk rubutun da zan yi maka daga yanzu zai iya zama abu na karshe da zan gaya maka. Rayuwa ta kadai ta isa nasiha a gare ka akan cewa babu wani abu da yake da tabbas, lokaci ne kawai yake da tabbas sai dai mu bamu da tabbas din kaiwa zuwa lokacin, an rigaan kayyade wa kowa iya kacin adadin seconds da zai yi a duniya kuma duk yawan kudin daka tara, duk kyawun fuskarka, duk yawan masoyanka da makiyanka, duk martabar ka, duk yawan ibadarka da rokon Allahn da zana yi akan ya kara maka kwanaki a duniya ba zaka wuce wadannan seconds din ba. Kowanne dan Adam yana tafiya ne akan nasa lokacin, dan wani yayi kudi da wuri ya sayi katon gida da manyan motoci ya auri kyakykyawar mace yar nasaba ba lallai ne shine successful man a duniya ba, maybe shi kwanaki kadan aka kayyade masa da kuma arziki da yawa, wannan shi yasa yayi arziki da wuri dan ya cinye arzikin sa kafin lokacin sa ya cika.
Wani kuma sai yayi ta neman kudin da karfin sa da kwakwalwar sa amma sai ya dauki dogon lokaci bai samu ba kuma zata iya yiwuwa shi mai tsahon rai ne, dan haka yake cin arzikin sa kadan kadan. Wani kuma a wahala zai fara kuma a wahala zai kare saboda tasa kaddarar kenan. Babu wanda yake sauri babu kuma wanda yake lakaki, kowa yana tafiya ne akan lokacin sa.
Shi arziki ba komai bane ba illa wata hanya da ubangiji yake jarabtar bayinsa, sai ya baka kudi yaga abinda zaka yi dashi ko kuma ya hana ka yaga abinda zaka yi. Ida har ka nemi kudi ka samu to Allah ne ya baka, idan kuma baka samu ba to shine ya hanaka. Idan ka samu dama ka nemi kudi ta hanyar halak, idan zaka kashe su ka kashe su ta halak. Idan kana dashi ka taimaka wa wanda bashi dashi, idan baka dashi ka nemi na kanka ta hanyar halak kar ka zama mai matacciyar zuciya ko mai roko a gurin mutane.
A duk lokacin da dama ta same ka tayin wani abu to kayi shi a lokacin kar ka jira sai wani lokaci, dan ba kai kake da lokacin ba. Duk abinda kaji kana son yi to kayi abinka, as long as bai sabawa ubangijin ka ba kuma ba zai zamanto cutarwa ga wani abin halitta ba ba to kayi abinka kar ka damu da abinda mutane zasu ce dan su mutane ba’a taba iya musu, in kabi ta tasu ba zaka yi achieving komai ba.