GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shamsiyya da Mabaruka har a ka gama masifar suna bacci sai da Uwa! ta shiga d’akin tana kwashe sauran kud’in tanayi tana zage-zage sannan ne suka tashi, Shamsiyya tace”wai menene ina bacci ina jin hayaniya a gidan sama-sama, na d’auka ma mafarki nake”

Nan Uwa! ta kwashe komai ta fad’a musu, suka had’u da ita suna zagin Baban na su.

Balaraba kuwa wanka tayi a gurguje ta sanya doguwar riga ta atamfa, me kalar blue da yellow mayafi mai girma ta yafa ta sanya takalmi plate mai a don duwatsu, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ta kuzo a gani ba, su Sadiya sun shirya tsaf cikin uniporm dinsu na makaranta, ta hada musu shayi mai kauri ta basu sannan ta dafa musu indomee cikin kula, tare suka futo ta kulle d’akin ta nufi d’akin Iya, tana kwance kan katifa, da alamar ta fara samun saukin jikin ta, suka gaisa cikin mutumci Balaraba tace”Iya jiki yayi sauk’i ko”

“Alhamdulilahi jiki yayi sauk’i Balaraba, Allah yayi miki albarka, ta cigaba da cewa, kin futo to Allah ya bada sa’a”

“Ameen Iya nagode, yanzu ba kasuwa zani ba,zanje in ciro kud’i a banki zan sa a fara neman min gidan haya, ko a bayan layi ne,domin bana so in yi nesa dake”

” Yanzu ashe baki bar wannan k’udirin naki ba, Balaraba”
Iya tafad’a cikin jimami

“Iya kiyi min addu’a kawai zaman gidan nan nagaji dashi wallahi,gwara in tafi in bar musu”

“Shikkenan Allah yasa haka shiyafi alkairi”

“Ameen sai nadawo”
Balaraba tafad’a tana k’okarin tafiya, ta jiyo mitar Lantana, ko waiwaya batai ba, ta futa daga gidan.


Kwana yayi yana tunanin ta ina zai fara bunkican Asalin Balaraba, ga Moddibo yau yak’i kwana a shashen sa, ya gudu nasa sabuda tunda ya dawo nan yake kwana, dole gobe kafin ya futa,ya nemi Moddibo a kan al’amarin domin shi kam bai san ta inda zai fara ba, kwana yayi yana mafarkin da yasa bayi kullum, asubar fari ya tashi, yana had’a gumi, mafarkin yau yafi na kullum bashi tsoro, yau ganinshi yayi tare da yarinyar nan mai kama da budurwar Moddibo, yana tara da ita kamar matarsa, abunda bai tab’ayi ba kenan, tunda yake bai tab’a mafarkin wata “ya mace ba, ya san dai shi mutum ne mai yawan sha’awa shine dalilin da yasa ma yake yawaita azimi, domin tsare kanshi, kuma baya tab’a yadda ya keb’ance da mace ko wace iri ce mutukar ba muharramarsa bace, sosai ya ganshi a mafarkin tare da yarinyar suna mu’amula irin ta ma’aurata, jikinshi a mutukar sanyaye ya mik’e ya shiga toilet domin ya tsarkake jikinshi, dole sai yayi wanka, kamar yadda addini ya tanada, bayan ya gama ya d’aura alwala ya futo, jikinshi d’aure da wani k’aton towol mai kauri da tsane ruwa, wani k’arami ne a hannushi yana tsane kanshi dashi, farar jallabiya mai yankakken hannu ya saka ajikinshi had’e da gajeran wando, ya sanya hula irin ta larabawa, a kanshi sai ya zama tamkar wani balaraben kasar Saudia,kalar fatarshi ta futo sosai, ya zura wani farin takalmi ruffafe mai mutuk’ar kyau a kyawawan k’afafunshi, ya nufi massalaci cikin nutsuwa.

Muje zuwa

Comment
Vote and Share
[17/07, 21:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????

Bisimillahir-rahamanir-rashim

????52

Tare suka futo daga massalaci da Maimartaba, cikin nutsuwa suke tafiya tamkar wasu abokai yayin da wasu fadawa suke take musu, baya Waziri da Shamaki ne a bayansu, Shamaki ya kalli Waziri cikin sigar munafuci yace”Allah ya taimake ka, wai yaya kasake har haka tafaru? tuntuni tane fad’a maka wannan shak’uwar dake tsakanin Maimarta ba da yaron nan tayi yawa,kamata yayi ka d’auki mata, a matsayin ka na k’ani gare shi, ka lura da kyau, sam baya baka kulawa kamar yadda yake kula da d’anshi, ko wani abu ne ya faru, in ka lura Maimarta ba baya zartar da wani hukunci sai yasa anyi masa kiransa, kuma duk gaku a zaune a fada, kai da Ciroma da Galadima baku da amfani, nine Shamakin Maimarta ba,nafi kowa sanin shi, tunda kusan kullum tare muke yini a fada, kwanciya bacci ne kawai yake rabamu da shi, ina mai tabbatar maka da cewar in bakai da gaske ba, sai dai kaga wannan Yaro wata rana yana mulkar ka, Allah shi taimakake kayi tunani kan maganar da nafad’a maka”
Shamaki ya k’arasa maganar yana sunkuyar da kai, cikin munafurci

Ajiyar zuciya Waziri yayi yana kallon Maimarta ba tare da Sarki! suna tafiya a nutse hatta da tafiyar su iri daya ce sai dai kasaitar Sarki! har tafi ta mahaifin nashi,

“Akwai abunda nake shiyarwa,domin
Ni kaina wannan abu yana damuna Shamaki, tare nake so mu had’a baki da Ciroma amma yak’i bani goyan baya a kan k’udirina kansu,to amma yanzu na samo mafuta, kwananan buk’ata zata biya kan Yaron shiyasa duk wata giggiwa da yake nake d’aga masa k’afa sabuda nasa ta lokaci kad’ance, zai shafe a duniya kamar ba’ata b’ayin sa ba a doran duniya”
Waziri ya k’arasha maganar yana kallon su ganin yadda hadimai suke zubewa k’asa suna kwasar gaisuwa,wasu tun daga nesa in sun hangosu suke zubewa k’asa kansu a sunkuye, had’e da daga hannu, alamun girmamawa har sai Maimarta ba ya shige suke mike wa tsaye, wannan abu yana mugun b’atawa Waziri rai, shima suna gaishe suna bashi girma a matsayinsa na Waziri,amma baya gani, yafi son suyi masa gaisuwa wacce tafi ta Maimartaba da d’anshi Sarki!

Maganar da suke tattauna tsakanin Maimarta ba da Sarki! yana sanar dashi cewar zai fara bunkice da ya umarce shi, amma yana neman alfarmar ya barshi ya futa da Normal kaya,domin yin basaja, kuma bayaso a had’ashi da kowane bawa, in ba Direba ba, wato mai janshi a mota

Maimarta ba,yace”wannan tunanin naka yayi kyau sosai sabuda idanun jama’a wani ma in ya lura ga daga inda yasa ake bunkicen zai iya fad’in k’arya a kan yarinyar, dan haka duk in da ka tsara kaje kayi, Allah ya kiyaye hanya”

Sarki! yaji Dad’in amuncewar da Maimarta ba yayi, domin a k’aidar masarautar su, basa futa da Tufafi dole sai na sarauta in kagansu da Normal tufafi to a cikin gida suke.

Tare suka shiga b’angaran Mama Fulani domin yau Maimarta ba a gurin ta yake, ta k’ofar baya ya shiga, shi kuma Sarki! ya shiga ta k’ofar da kowa yake shiga,

Tana zaune kan wata katuwar daddamu, ja mai adon fulawa, gefan tumtum ne manya-manya guda uku, gabanta kuwa shak’e da kayan marmari, tana sanye da wata lifaya mai tsananin kyau da tsad’a hannuta rik’e davwani k’aramin carbi mai kyau sai kyalli yake, tayi kyau har tagaji Mama Fulani kenan mace mai karamci da karramawa, mace mai kaunar talakawa da nakassau, Jakadiya Shafa’atu ce zaune a gabanta,da mufuci a hannuta duk da safiya ce amma fiffita take mata, cikin sakin fuska tace”Shafa’atu wai ke bakya gajiya ne”?

” Yaya za’ayi in gaji da hidima da uwar d’akina”
Jakadiya Shafa’atu tafad’a tana sunkyar da kai,

Shiru Fulani tayi kawai tana mamakin karamcin Jakadiya Shafa’atu, macace mai dattako da sanin ya kamata, duk wasu munafurce munafurce da ake a gidan babu ruwanta, an sha had’a baki da ita, domin cutar da ita, tana kare ta, domin farat d’aya bata ce musu bazata yi ba, ko magani suka bata sukace ta sanya mata a abunci sai ta karb’a da yarjejeniyar zata aikata, tana ganin sunbar gurin zataje ta zubar,kuma tazo ta fad’a mata cewar ta dage da addu’a, tana da mak’iya sosai a gidan, ko Waziri yaso ya had’a kai da ita lokacin cikin Sarki! tak’i yadda , shiyasa sam batada farin jini a cikin “yan uwanta har kullum suna kiranta da munafuka, ta sha hak’o tarin layu da hade da bak’in gashi irin na bunsuru, a harabar shashen Fulani sai dai kawai taje ta k’ona, ko kuma ta kaisu can wajan dukonan gidan suyi masu futsari, a kwai lokacin da Uwar gidan Maimartaba ta aiko Jakadiyar ta da wata bak’ar kaza, an cire mata kai, sai digar jini take, gashi an farka cikinta, anzuba layo suma an d’inke su da bak’ar fata, an saka a cikin kazar an d’inke da bakin zare, can wani lambu taga ta nufa, sai ta bita a baya tana kallonta tana tona rami, mai zurfi tayi saurin sa kazar a ciki ta mayar da k’asar ta rufe gurin, sauri-sauri tabar shashan dan kar a ganta ko gama futa batai ba taje ta tone gurin ta futo da kazar, ta bude cikin ta ta zazzago layun, nan ta tara ice ta had’a ta kone su tass! yana mamakin rashin imani irin na Uwar gidan Sarki, wato Kululu mai d’akin kudu, haka suke kiranta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button