GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi Maimarta ba yayi ya mika masa hannu suka musabaha, yace”ai tunda naga kana farin ciki nasan maganar ta shafe ka”

“Kwarai kuwa”
Waziri yafada shima yana murmushi, amma fa ta ciki na ciki

Sarki! ne ya matso sosai kusa da mahaifin nasa, kanshi a kasa yace”barka da asubah”
Hannunshi Maimarta ba ya riko fuskarshi a sake yace”kai kayi min laifi, kwana biyu baka zuwa fada,bazan karbi gaisuwar ka b

Sosa kai yayi na sabo,yayi kasa da kanshi yana murmushi yace”tuba nake ranka shi dade, tunda mukaje can gwarzo na dawo bana jin dadi jikina,wallahi”

“Me yasa baka kawo uzirin ka ba”

Shiru yayi sai faman sosa kai yake

Waziri Zayyanu yace”wannan sharme ne, mu me yasa muke futowa fada, kullum kuma ai tare mukaje can Garzon ko ba haka ba ne, wannan yana nuna mana cewar sam baza ka iya wakiltar jama’a ba.
Cikin fada ya karashe maganar,

A nutse Sarki ya dago kai yana kallonshi,ya wani hade fuska sam ba ya so yana shiga lamarin shi,shi kuma yaki ya gane,
Ganin yadda Sarki! ya hade fuska ne yasa Waziri saurin sunkyar da kansa, sabuda wani irin kwarjini da Allah yayi masa,

Wannan abun da Waziri yayi masa yasa ya fasa gaida shi,kawai ya dauke kanshi,jira kawai yake Maimarta ba ya mike shima ya samu damar tafiya,
Maddibo ne ya karaso kusa da Maimarta ba ya gai dashi, ya gaida Mahaifin shi Waziri Zayyanu,

Maimarta ba ya mike cikin nutsuwa, suma suka mike suka biyo bayanshi lokacin gari ya soma washe wa, Wasu fadawa ne guda Uku tsaye bakin massalacin sune suka rufa musu baya,har sai da Maimar taba,ya shiga Shashenshi,sannan kowa yayi nasa ban garan,

Sai wajejen Goma da wani abu sannan Waziri ya samu Maimar taba,bangaran Fulani, nan suka zauna a ke bantaccan falo wanda yake zama domin sirri irin wannan,

Gyara zama yayi sosai yace”ranka ya dade magana ce daga Sarkin garin Yalwa, kasan tare mukayi karatu dashi,sosai har yanzu alakar mu dashi tanan, to shine yake neman wata alfarma a gare ka, wato ya naso ya hada jini da kai, wai yarinyar shi Azima tana son Auran Almansor,, shine ya aiko min da sako, a kan hakan, Allah shi tai makeka kaji abunda yake tafe dani”
Waziri ya kare maganar yana sauke ajiyar zuciya
Kanshi a kasa yana sauraron abunda Maimar taba zai ce

Minti biyu a tsakani, Maimarta ba yace”wannan ba hurumi na ba ne,domin bazan iya tilas ta Sarki! ya je ya nemi auran yarinyar nan ba, abunda zakayi kawai ka nemi shi kafada masa zan can, sannan yarinyar tazo ya gan ta in yaga tayi masa shikkenan,ni dan addu’a ne, sai a hada da Halisa kawai”

Comment
Vote and Share
[08/07, 13:24] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????

            _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDIGATED
TO
{ RAHAMA ALIYU}

????42

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Shiru Waziri Zayyanu yayi na minti biyu kana ya dago kanshi yana kallon Maimartaba yace”Allah shi taimake ka ina ganin yaron nan zai bamu kunya domin kasan halinshi da baudaddan ra’ayi, ina ganin kai ne zaka tilas tashi ya amunce da buk’atar mu,domin lokacin maganar Halisa ma haka muka dinga dauki ba dadi a kansa, Zai iya bujerewa bukatar mu, Azo a samu matsala game da dan gartakarmu da Sarkin Yalwa, Maimar taba Sarki Alkassim”

Cikin Mamaki Maimarta ba yake kallon Waziri jin abunda yace, gyaran murya yayi a nutse yace”maganar in tilas ta Sarki! ya nemi auran yarinyar da kake magana sam! bata taso ba, domin babu wanda zai zauna masa da ita,sai shi,idan na tilas tashi yaje ya dauko yarinyar mutane, yazo yayi mata rikon sakainar kashi,in ce me? ko kai kace me, abunda nakeso ka fahimta shine, ba wai ina biye wa yaron da duk abunda yake so ba, ina neman zaman lafiya da kwanciyar hankali, ko yau Sarki! yace yana so ya auri mace hudu ni mai daura masa aure ne,sabuda nasan da amuncewar sa kuma ba kowa ne zai zauna masa da suba sai shi, sabuda haka ka aika ai maka kiranshi,sai ka zube masa maganar in ya amunce shikkenan nima na amunce, Allah ya tabbatar da alkairi”
Ya karashe maganar yana duba wani karamin littafin husunul-musul wanda yake karantawa shi kullum da safe,

Jikin Waziri Sanyi kalau ya dago kansa yana kallon Maimartaba yayi tunanin zai samu nasara gurinshi sai yaga sab’anin haka, a gurinshi, jiki a sanyaye yace”duk yadda kace haka za’ayi Allah shi taimake ka zan sanya a kira min shi yanzu kafin mu zauna a fada”

Cikin sakin fuska Maimarta ba ya mika masa hannu sukai musabaha yace”masha Allah, ina sauraron ka duk yadda kukayi dashi sai ka same ni a shashenan domin tattauna maganar”

“Insha Allahu, A tashi lafiya”
Waziri yafada kanshi a kasa ya futa daga dakin.

Sarki! kuwa ko da ya koma bangaran shi, kai tsaye bedroom dinshi ya nufa domin wani irin bacci ne yake damunshi, jallabiyar dake jikinshi kawai ya cire baya son zafi ko kadan, shiyasa kafin ya kwanta sai da yakara karfin AC sabuda baya son ya kwanta zafi ya ta dashi daga bacci, Kwanciya yayi kan bed dinshi,wanda yaji shimfudu na alfarma, wayoyinshi ya kunna ya zube su a gefanshi, nan take sakkoni suka da dinga shigowa, ko daya bai duba ba, kawai yana kwance ya zubawa rufin dakin ido, daka gani akwai abunda yake damun zuciyarshi, wanda shi kadai ne ya sanshi sai kuma mahallincin shi, wannan abu na damunshi, sosai in dai zai rufe idonshi da nufin yin bacci,sai Allah ya nuna masa wata mata, tana kuka sosai gata a durkushe a gabanshi ita da wata yarinya matashi budurwa itama tana kuka suna rokanshi wani abu,wanda ya kasa fahimtar menene shi,abun mamaki matar in ta tashi tafiya,cikin mafarkin sai ta zo ta hada hannunshi da wannan matashiyar yarinyar tace”ga amana na baka, daga haka sai ta tafi har ya daina ganinta, ita kuma wannan matashiyar yarinyar kuka take sosai tana kokarin kwace hannuta daga nasa, abun mamaki shi kuma sai ya rike hannun tamau! yaki saki a haka yake farkawa, in ya tashi yai taso ya tunano fuskar wannan matashiyar yarinyar amma sai ya kasa haka zai bi hannushi da kallo wanda ya rike nata, ya kan dade bai dai na jin dumin hannuta a nasa ba,
Wannan mafarki yana damun rayuwar shi a kalla ya kai shekara biyar yana wannan mafarki, babu wanda ya sani da gashi sai mahaliccin sa, ko mahaifiyar shi bata sani ba,

Wayarshi ce ta dame shi da kara, a nutse ya dauka yana dubawa Halisa ce,
kamar ya share ta,sai wata zuciyar tace”ka dauka kaji wane shirme zatai maka,
Cikin yanayin muryarshi yace”Assalamu alaikum”

Wata irin ajiyar zuciya Halisa tayi, cikin shagwaba tace”Habibi ka tashi lafiya”?

“Lafiya,kefa”?

” Nima lafiya lou, sai dai tunanin ka da ya uzzira min”
Halisa tafada tana mutso-mutso kan bed din ta, itafa ko muryar shi taji sai ta shiga wani hali, ballan tana ta kusance shi, ji take kamar ta rungume shi ta huta da abunda take ji a kansa

Muryar shi kasa-kasa yace”bacci zanyi yanzu in kina da abun fada ki fada ko na kashe waya ta”

Jin yanda yayi kasa da murya ya kara gigitata, makale wayar tayi a kunnen ta tace”cewa nayi fa gani ina kewar ka ina ma ina kusa da kai da nayi maka tausa”

Shiru yayi mata,kawai ranshi ya soma baci da shirmen da tafara yi masa, shiyasa suke fada kullum,sabuda shi ya tsani mace mara kamun kai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button