GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin daurewa Sadiya ta watsa maganin a baki ta had’a da ruwa ta shanya, yace “muje in raka ki ki kwanta, kar ki k’ara futowa sai da safe”
Tare suka futa hannusa rik’e da nata, Balaraba na tsaye a bakin k’ofa kamar ta d’ora hannu a ka, tana kamar an tashe ta ta farka daga nannauyan baccin da ya d’auketa,wanda kafin tayi shi sai da ta shafa, saboda tunanin da yayi mata yawa, kawai sai ta duba taga k’ofa a bud’e babu Sadiya, ta mik’e a zabure! ta sauka k’asa, duk girman farlon ta dudduba bata ganta ba, da sauri ta dawo sama ta tsaya bakin k’ofar tarasa abunda zatayi, hawaye kawai sai ya k’wace mata, zuba kawai suke zuciyar ta sai sak’e-sak’e take mata. kawai sai taga an bud’e k’ofa, suna had’a ido yayi saurin kau da nasa dan bazai iya kallonta a yanayin da take ciki ba, kai babu d’an kwali, ga kayan jikinta sun futo mata da k’irar ta, da sauri! tazo zata fuzge hannun Sadiya, tana kuka, gabanta sai fad’uwa yake tana addu’ar Allah yasa bai cutar mata da k’anwa ba, rik’e hannun yarinyar yayi tamau! yak’i saki yana son yaga iya gudun ruwan ta, hannuta tasa tana tureshi , kamar me ture dotse sam yak’i motsi cikin kuka tace”Allah ya isa tsakanina dakai, mugu azzalimi Allah sai ya saka mana, ka cuci marainiyar yarinya sai nayi shari’a da kai”
tana kuka tana dukan k’irjinsa take maganar.

Lokaci guda ya fahimci abunda take nufi, cikin tsantsar b’acin rai da damuwa ya fidda hannu ya tsinka mata mari, zuciyar shi tana tafasa yace”me kike nufi ne da wannan maganar taki”?

“Duk abunda kake nufi shi nake nufi” tafad’a cikin hayaniya, abunka da dare, gari yayi tsittt! shi tsoransa ma kar hadiman sa suji tunda wasu, suna kwana a k’asa, wa ni k’ebantaccan guri, wanda yake da k’ofa w ciki da waje, saboda haka sai ya sa k’irjinsa ya tura ta cikin d’akin ya shiga shima da Sadiya a hannusa yarinyar duk ta furgice! da sauri Balaraba ta mik’e tsaye, saboda fad’uwa tayi k’asa lokacin daya angiza ta, tayi kan Sadiya tana dukanta tana kuka, kamar wata mata hankali, tunkud’e ta yayi a karo na biyu ta kara fad’uwa k’asa yace”wallahi ki shiga hankalin ki, banza shashasha kawai kin saki baki kina bacci, saboda abunda kikazo yi kenan, kin bar yarinya ta futo da zazzab’i a jikinta, dube ki don Allah”
yafad’a yana mata banzan kallo, ya cigaba da cewa”duk abunda kike tunanin nayi da ita to nayi d’in ,kema bazan barki ba, zan biyo dare inyi dake, kuma tunda kika shigo gidana babu ke babu futa kin shigo kenan, zanga k’arshen rashin kunyar ki”
Yana gama maganar sa ya fuce daga d’akin kamar walkiya.

Sadiya ta jawo tana kuka tana duba mata jiki, ita har ga Allah ta tsorata dashi, sam bayanin da yayi mata bai gamshe ta ba,

Yana komawa d’akinsa ya zauna bakin gado ya dafe kansa cikin damuwa, wannan yarinyar ta b’ata masa rai, ko neman mata yakeyi me zai tsinta jikin yarinya k’arama irin wannan, mik’ewa yayi da sauri yaje ya kunna CCTV Camara, ya sai ta komai, idon ya zuba mata sosai yana kallon yadda bakinta yake motsi, sai masifa takewa yarinyar tanayi tana kuka,

Wani murmushi ne ya k’wace masa ya girgiza kai kawai, shi mamakin yarinyar ma yake, da gaske zargin sa take yayi wani abu da yarinyar.

Comment d’in da kuke min baya isa ta, in kun k’ara in k’ara yawan typing

Comment Vote and Share
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM

????61
Yana zaune yana kallonta cikin CCTV Camara ta zabga ta gumi dagani tana cikin damuwa, mik’ewa ya ga tayi tana gyarawa k’anan nata kwanciya, ta nufi toilet, da sauri ya d’auke kansa lokaci da ta juya baya tana tafiya, gabanshi ya dunga fad’uwa, idonsa k’urr! a k’ofar ban d’aki har ta futo da alamu alwala ta d’ora, yana kallo ta bud’e k’aramin a kwatunsu ta d’auko zanin atamfa da wani k’aton hijab tayi shirin yin sallah, can inda a ka tanadi daddumar sallah yaga ta nufa ta tada sallah, agogon bango ya kalla, hud’u shaura minti ashirin, mik’ewa yayi shima a nutse a shiga toilet ya had’a ruwa, yayi wanka, sannan ya d’auro alwala, niko nace, ko wankan me yayi oho,da asubar fari shi da ba mata gareshi ba.

Sabuwar jallabiya fara kar, ita ya sanya a jikinsa, yaje ya kashe CCTV Camara, ta idar da sallahr tana zaune tana kallon gabas hannunta duk biyun a sama da alama addu’a take, sai yaji yarinyar ta burge shi, da alamu me ibada ce, Sallahar raka’atanin fajri ya tayar, bayan ya idar ya zauna yana jan jarbi har lokacin da a kafara kiran sallahar asubahi, sannan ya mik’e a nutse ya sauka k’asa, suka had’u da d’an rakiyar shi yana zaune a farlo yana jiransa, yana ganin sakkowar sa ya mik’e tsaye yana kwasar gaisuwa suka gaisa, a mutum ce, Sarki! ne a gaba shi a baya har suka isa masjid.

Balaraba kuwa ta dad’e kan abun sallah bayan idar da sallah asubahi tana rok’on Allah ya futar da su daga damuwar da duke ciki da ita da “yan uwanta ba, bacci ne ya dunga fuzgarta dan haka nan kan abun sallahr ta b’ungire bacci ya kwashe ta.

To bayan an idar da sallah ne anyi gaishe-gaishe kowa yana so ya koma shashensa, Moddibo yake tambayar shi amanar da ya bashi, rasa abunda zai ce masa yayi kawai ya share shi, Moddibo yace” to tunda ka k’i fad’amin muje inga ya suka kwana”
A hasale Sarki! yace”ni wannan binbinin naka ne banaso wallahi, ni yanzu bacci nakeji jiya sam banyi baccin kirki ba kabi ka dameni da zan wata Balaraba, da ta hana mutane sakat!”

Cikin sanyi murya da sanyi jiki Moddibo yace”muje dai in ganta, wallahi jiya kwana nayi ina mafarkinsu ita da “yan uwanta, ina kaunarsu, a zuciyata kuma nakeji kamar bazan yi wani dogon zama dasu ba”

Cikin mamaki yake kallon Moddibo lallai yau ya gazgata da cewar Moddibo da gasken gaske! yake son Balaraba, bai tab’a jin tausayinsa ba irin na yau, tabbas ya yarda so bala’i ne.

Yace”kan wane dalili zaka dunga yadda zuciyar ka tana maka sak’e-sak’e na abu marasa kyau, na d’auka tuntuni ka daina irin wad’annan tunanin naka”

“Mubar maganar kawai Magajin Sarki ni kad’ai nasan abuda yake damun raina fa, jiya kwana nayi ina murk’ususu ciwon cikina ya tashi, kasan yadda yake min in ya motsa min”

Da sauri ya kalli fuskarsa yaga duk tayi zuru-zuru, tabbas da gaske yake, yace”kayiwa girman Allah ka rage k’ulafun yarinyar nan, kar kaje ka tayar mana da hankali, kafi kowa sanin in ciwon ka ya tashi, babu me zaman lafiya, da kwanciyar hankali, ba kai kad’ai ne kake shan wahala ba harda mu gaba daya “
Girgiza kai Moddibo yayi yace”sam ba soyyayar da nakewa Balaraba bace zata tayar min da ciwon na ba sai dai rashin fahimtar dake tsakaninku da ita, Balaraba ba ta da kowa,a yanxu sai Ina so ka tayani sonta da kula da ita”

“Shikkenan zanyi yadda kace, amma don Allah kar ka jawo mana tashin hankali, Indin saboda bana sakin jiki da Balaraba ne, yasa kake wannan tunanin na dai na daga yau insha Allah”

Farin ciki ne ya kama Moddibo fuskarshi a sake suka shiga shashen Sarki! d’in zama yayi cikin kujera shi kuma Moddibo ya hau sama,d’akinsu Balaraba, tana zaune ta zanga tagumi cikin damuwa Sadiya da Usuman na zaune gefe-da gefen ta, yayi sallama ya shiga, dak’in dago kanta tayi cikin nutsuwa ta sauke a kansa har ya k’araso kusa da ita ya zauna da murmushi a fuskarshi, yace”barka da asubah sarauniyar zuciyar Yusuf Moddibo, zuciyata tana azabtuwa da so da k’aunarki Ina fatan kin tashi lafiya”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button