GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

A sake tace”shikkenan sai ka dawo a gaishe min dasu”

“Zasuji insha Allahu”
Yafad’a yana k’okarin barin gurin.

Bayan futar Moddibo daga falo,sai yayi shiru saboda duk masu hidima a gurin sun gama sun futa,sai sautin AC ne kawai yake tashi, Usuman can gefe yake yana ta “yan wasaninsa, sai taji zaman gurin ya gundure ta, taja tsaki ya kai sau biyat r in ta d’aga kai ta hango Sadiya,na cin abunci ta sake sosai dashi tana masa hira har da dariya.

Sam! tak’i yarda su had’a ido dashi, a sace take k’are masa kallo yana cin abunci cikin nutsuwa, gashi fuskarsa a sake,yana sauraron hirar da Sadiya take masa,cikin zuciyar ta take ayyana irin dukan da zata yiwa Sadiya.

Taku! tafaraji k’was!k’was!k’was! irin na mace, takun takalmin ya d’auki hankalin ta har shi uban gayyar, da yake can inda yake zaune saitin k’ofar shigowa ne, shiyasa ya ga wacce ta shigo Gimbiya Halisa ce, Balaraba na zaune can wata kusuwar wa shiyasa bata ganta ba,

Halisa tana tare da wasu bayi guda biyu suna take mata baya, wanda suka tsaya bakin k’ofar shigowa, can inda ta hange shi zaune ta nufa fuskarta babu walwala,ganinshi zaune da wata,daga can nesa tana yiwa Sadiya kallon wata k’atuwar budurwa, shiyasa ta sha kunu,sosai tana tunanin me ya kawo mace har falonsa duk da tasan halinsa ba ya Neman mata.

Giftawar ta Balaraba ta hanga,ta bita da kallo daga sama har k’asa, tana ganin yanayin shigarta ta gane,” yar sarauta ce.
Sarki! kuwa d’auke kansa yayi daga kanta har ta k’araso gurin ta tsaya gami da d’ora hannuta kan kujerar da Sadiya take zaune tana mata wani kallo irin na raini tace”Habibi wannan yarinyar a ina ka samo ta,naga sam ba jinsin mu bace”

Banza yayi mata,kawai ya cigaba da cinsa abuncin sa a tsana ke,

K’ara maimata maganar tayi,ya d’ago kansa cikin jin haushin ta yace”ban sani ba, ki kauce daga kan mutane tunda ke baki da ladabi da sanin ya kamata”

Ganin ya hasala! yasa ta fara yak’e tace” tunda na shigo na ganka zaune da mace a guri guda naji hankalina ya tashi shiyasa na rasa nutsuwa ta, sai da na k’araso kuma naga ashe ma yarinya ce,amma dai duk da haka hankalina bai kwanta da ita ba,yarinya sai kace,me dubi yadda take k’walo ido kamar mayya”
Karaf! a kunnen Balaraba,dama taji abunda Halisa tace a farko Dan gane da Sadiya.

Ranta a b’ace ta futo daga inda take,ta tsaya a gurin tana kallon su, a cunkushe ta bud’e baki tayi magana, tace”ke! Sadiya baro gurin nan, kinji ko”
Duk hankalinsu ya koma kanta har shi,uban tafiyar, ganin fuskar yayar ta a murtuke ya fad’ar mata da gaba,sai ta fara yunk’urin mik’ewa tsaye domin ta cika umarnin ta, yayi saurin dafe hannun yarinyar ya hanata tafiya, ido ya zubawa Balarabar dake tsaye can gefe tana cika tana batsewa, ganin Sadiya tak’i tasowa yasa ta k’ara buga mata tsawa,a karo na biyu.
A nutse ya d’an daga muryarsa yace”tak’i zuwa d’in in kin isa kizo ki jata,da k’arfi mugani”

Comments Vote and Share
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM

????63

Cike da karsashi,da jarumta ta durfafi inda suke fuskarta a had’e tamkar wacce bata tab’a dariya ba, tana zuwa tafara yunk’urin fuzge hannun Sadiya daga cikin nasa, a nutse ya d’ago kanshi tare da zuba mata idanunsa,ya bud’e tar! Gabanta ya buga! sai kace mai lak’ani a idonsa, duk gwiwarta ta sage! kanta ta sunkuyar k’asa domin bazata iya jurar k’alon k’wayar idonsa ba, amma duk da haka bata fasa k’okarin fuzge hannun Sadiyar ba saboda k’arfin Hali, rik’e hannun yayi tsaf! da tazo zata k’wace sai su had’a hannu, sai ya had’a da hannun nata ya matse,ganin abun nasa harda iskanci, yasa ta fuzge hannunta tana zabga masa harara, batare da tabari ya gane gazawar ta ba,ta kalli Sadiya,cikin fad’a tace”zan kama ki,wallahi tunda kike barin maza suna rik’e miki hannu” barin gurin tayi a fusace,ta kama hannun Usuman suka haura sama.
Kallo ya bita dashi, fuskarsa d’auke da murmushi, girgiza kai yayi kawai yana mamakin k’uruciyar ta, yanzu ya gane itama yarinya ce, sakin hannun Sadiya yayi dake zaune tana mayar da k’walar da ta taro a idonta,saboda tasan halin masifar yayarta
Yace”kwantar da hankalin ki kinji ko Halimatu, duk abunda tayi miki in mun had’u zan rama miki, tashi kije” mik’ewa tayi jikinta a sanyaye, ta haura sama

Sai sannan ya mai da hankalinsa kan Halisa dake tsaye, tana cika tana batsewa duk wani abu da ya faru tsakanisa da Balaraba ta gani mussaman had’a hannu da suka yi”

B’ata fuska yayi kad’an yace” kin zama dogariya ne,wai duk gurin zaman nan bai miki ba sai dai ki tsaya a kai na”

Cikin fushi tace”ai banga fuska ba, tunda ka kawo wacce kakeso har gida,ita kuma wannan mai sifar karuwan fa”

Hararata yayi yace”ki iya bakin ki wallahi ranki zai mugun b’aci a kan wannan yarinyar matar Moddibo ce in sha,Allahu”

Wata dariya ta shek’e da ita,ta nemi guri ta zauna, cikin jin dad’i tace” gaskiya Ya Yusuf ya iya zab’e tsaf wannan zata yi masa wayo dubi idonta,don Allah,wai me ma ya kawota shashen ka ne, kuma meyasa har ka zauna da ita da k’anwarta guri guda”
ta k’arasa maganar da damuwa!

“Sai ki bari sai ya zo sai ki tambaye shi,amma yanzu ni bani da lokacin baki wannan amsosin naki”

Mik’ewa yayi daga gurin ya barta zaune,babu shiri ta mik’e tana bin bayansa har ya zauna kan wata kujera me cin mutum d’aya, ta zauna a wacce take fuskantar sa, wata k’aramar drowar ya jawo k’asan kujerar ya futo da wani k’aramin littafi irin na addini yafara dubawa, tunda taga yayi wannan zaman tasan ba zai saurareta ba, duk abunda zatayi kuwa,dole ta jira ya kammala tukkuna, mintuna goma ta gaji da zaman gurin sai ta mik’e ta fa kaici idonsa, ta hau sama tana laluben inda Balaraba take, cikin sa’a ta ga wani d’aki a cikin d’akunan dake barandar a bud’e,kai tsaye d’akin ta nufa cikin k’asaita ta tura k’ofar da k’afarta,ta shiga babu sallama, Balaraba na zaune gefan gado ta cire hijab d’in, tana sanye da doguwar riga,cotton mai taushi,tana da yankakken hannu, sai tayi amfani da k’ara min hijab me hula, irin na Larabawa, tayi mugun kyau,kamar wata balarabiyar k’asar Oman, Halisa sai da Gabanta ya ganin ciki da k’asaitar Balaraba,fata luwai sai kace me rayuwa a kasar waje,ko ita albarka,ita da take rayuwa a cikin jin d’adi.
Dukkaninsu k’ofa suka kalla jin a bugo da k’arfi an shigo, dogarewa tayi bakin k’ofa tana watsa musu kallo, ta kalli Balaraba a k’asan kan ce,tace”zo ki rufe min k’ofar nan,ke me kama da “yayan bayi”!!

D’as!d’as!d’as! K’irjin Balaraba ya fara buga jin furucin Halisa, cikin sigar izgili da nuna ke awa! kuma baki isa ba,tace” a matsayin ki na wa! da har xaki bada umarni abi,ki bari sai kin kai matsayin zama cikkakun mutane sai ki bada umarni,amma dai yanzu baki isa ba”

“Ke ni kike fad’awa magana,har kike k’okarin zagina,munafukar Allah, ta’alah macuciya, an ga gidan sarauta an lallab’o, to bari kiji,shi kanshi Moddibo baza ki same shi ba,balle kuma Sarki! Wannan nawa ne ni d’aya”
Halisa ta k’arashe maganar tana dungurewa Balaraba kai, abunda Halisa bata sani ba shine ba’a nuna Balaraba da d’an yatsa,komai girman ka kuwa sai ta nuna maka ruwa ba,sa’an kwando bane,
Wani ba hagon mari ta tsinkawa Halisa a fusace! Sam!ba tayi tunanin abunda zai je ya dawo ba.
Ihu Halisa ta kurma! tayi kan Balaraba da duka sai zaginta take,abinka da sabo da fad’a tuni Balaraba ta tare ta,su kafara kokawa abun mamaki, nan Balaraba ta yar,da Halisa a k’asa, saboda ita bata iya fad’a ba,ga jikin Hutu,babu k’wari, sosai Halisa taji ciwon fad’uwar ta k’asa, ko da mik’e bata daddara ba,ta k’ara yin kan Balaraba a karo na biyu, tayi nasarar fuzge mata hijab d’in wuyanta ta cire hular kan nata,ta tattaro gashin kan Balaraba ta rik’e sai ja take,tana gaya mata maganganu na b’atanci kuma sai ta d’aure ta,tunda ta sake tayi kokawa da ita, Balaraba kuwa k’okarin kwatar kanta takeyi hannuta ta kama ta murd’e! da k’arfi, Halisa ta saki ihu,babu shiri ta sakar mata, kai tana duba hannunta tana cije baki, ki take kamar wacce tayi targad’e, ganin sunk’i su dai na fad’an yasa,Sadiya sauka k’asa da gudu, domin taje ta fad’awa Magajin Sarki, yana zaune,a inda yake,kanshi k’asa yana duba littafin hannun sa, ya ga Sadiya gabansa tana zare ido,d’ago kai yayi yana rufe littafin hannusa, yace”dukan ki tayi kike haki! haka”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button