GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ni Yusuf Waziri Zayyanu na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki uku,saboda wani dalili,ina rokon Allah ya had’amu da ita a aljanar Firdausi

Innalilahi wa innailaihi raji’un
Kalmar da me Martaba yake ta maimai tawa kenan, kafin su ankara Moddibo ya zube a gurin yana wani irin murk’ususu, jini na fita ta baki ta hanci, ya rik’e cikinsa tamau! bakinsa na motsi,kalamar shahada kawai yake
Sarki! ne ya futo daga b’angaransa ya na d’aure da alwala,sai ya hango abunda yake faruwa saboda haka cikin sauri da sassarfa ya k’arasa gurin,lokaci mutane har sun taro, hankali a tashe ya tsuguna ya d’ora gwiwarsa a k’asa ya d’auki kan Moddibo ya d’ora a cinyarsa, cikin damuwa ya sanya gefen rigar shi yana goge masa jinin dake futa daga bakinsa, Moddibo ya rik’e hannunsa tamau!! wani hawaye yana zuba ta gefen fuskarsa, muryarsa bata futa sosai yace”Allah yayi bazan yi tsayin kwana ba, a duniya balle in rayu da yarinyar da zuciyata take mutukar so, d’an uwana ne kai ko na mutu kai na amunce da ka maye gurbi na gurin Balaraba, ka bata hakuri,ga tanan na bar maka amana son Balaraba wani b’angare ne na zuciyata na tabbata ko na rayu a duniyar nan to da soyayyarta zan mutu, Sarki! na baka amanar Balaraba”
Ya k’arashe maganar yana wata irin shak’uwa!
Cikin tashin hankali da damuwa me Martaba ya bada Umarni a dauko mota domin a tafi asibiti,Moddibo najin abunda ake sama-sama girgiza kai kawai yake domin shi yasan halin da yake ciki,,hannun me Martaba yake taso ya kama,ganin haka yasa Sarki!kamo hannun me Martaba ya had’a dana Moddibo, me Martaba ya rik’e hannun sosai yana kalmatussha hada, nan take Moddibo ya fara fad’a shima. “La’ilahaillallahu Muhammadur rasulullahi,sallalahu alaihi wassalam” Da wannan kalmar Moddibo ya cika, dai-dai lokacin da ake k’wala kiran sallahr magariba.
[07/08, 13:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????


We are here to educate,motivate and entertain aur readers


DIDEGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????69

Wata irin ajiyar zuciya Sarki! ya saki lokacin da ya ji jikin Moddibo ya shika a jikinsa, sai yayi zaman dirshan a gurin had’e da rungume gawar yana wani irin kukan zuci idanunsa sunyi jajawur!kalmar innalilahi wa’ina ilaihi raji’un kawai yake maimaita wa cikin zuciyarsa.

Kafin kace kwabo mutuwar Moddibo ta watsu a cikin gidan,mutane kowa na futowa daga b’angaran sa cikin tashin hankali, lokacin da labarin ya iski Waziri bai yadda ba,sai da ya tura Khalifa domin yaje ya gani gaske ne,aikuwa Khalifa ya dawo cikin tashin hankali,ya tabbatarwa da Mahaifin nasu hakane.

Waziri ya shiga cikin tsananin rud’u da tashin hankali,a gigice ya futo kafarsa babu takalmi ya nufi fada,zuciyarsa na yi masa sak’e-sak’en cewa Sarki Almustafah shine ya kashe masa d’ansa saboda wani dalili nasa.

Lokacin da ya isa,gurin ana ta k’okarin cire gawar Moddibo daga jikin Sarki! Abun ya gagara domin ya rik’e shi tam! wasu hawaye na zubo masa masu tsananin rad’ad’i, cikin zuciyarsa yake cewa shikkenan na rasa d’an kuwa nagari shikkenan narasa amini me share min waye, me yasa mutuwa zata d’auki Moddibo ta barshi,shi a duniya shima tabbas bashi da wani amfani a cikinta.

me Martaba ne yake ta rarrashin sa kan ya sake shi a d’auke shi daga gurin,gashi lokacin sallah yayi,amma tamkar da dutse yake magana,kwata-kwata Sarki! baya fahimtar abunda yake cewa.

Waziri ne ya k’araso gurin idanunsa a kan gawar Moddibo,kurrr!! Yake kallonsa kamar wani zautacce yace”K’arya ne, babu wani munafurci da ban sani ba,a gidan nan duk wani abu a dake shirya min ni da “yayana nasan shi, saboda haka, ni sai nabi kadin jinin d’ana Yusuf Moddibo”

Cikin mamaki jama’ar dake gurin suke kallon Waziri jin irin maganar da yake fad’a,maganar tasa tayi kama da ta masu tab’in hankali. Babu wanda ya saurare shi, a cikin su, suka cigaba da bin umarin me Martaba, da k’yar suka samu suka b’anb’are Moddibo daga jikin Sarki! suka nufi fada dashi, domin killace shi tunda dai dole yayi kwanan keso.
Waziri ne ya bi bayan su yana gyara alkyabar dake jikinsa, yace”Ban yadda a aje min gawar d’ana anan ba, domin inaso in kaishi kabarinsa da duk sassan jikinsa gaba d’aya, idan aka aje min gawar d’ana a wannan fada ban yafe ba,domin wannan fada bata alkairi bace,bata tattare da komai sai shirka,da tsafi gami da shanye jinin mutane”
Jin irin kalaman da Waziri yake fad’a ne yasa wad’anda suke d’auke da gawar Moddibo suka dakata, me Martaba kuwa cikin karfin hali yace”Kuje Ku cika umarnin da na Baku”
Aikuwa sai suka shige ciki sosai suka aje Moddibo gefe, suka futo gami da tsayawa bakin Kofa,suna jiran Umarni na gaba, me Martaba ya kallesu a nutse yace”Ku tsaya nan gurin ban yadda kowa ya shiga inda yake ba,yanzu zan futo zan shiga sallah”
Nan suka amsa suna godiya

Me Martaba ya wuce Waziri a gurin yana zare ido.

Waziri kuwa duk ya rasa abunda yake damunsa duk wannan maganganun da yayi, yayi ne kan ya b’ata wa me Martaba rai sai yaga ko a fuskarshi be nuna ba, ya fahimci yana cikin tashin hankali,kuma yasan bata komai bace face ta rasuwar gudan jininsa,.
Shi yanzu sam bai damu da rasuwar Moddibo ba,burinsa kawai yaga ya rusa sarautar Sarki Almustafah,ya kafa tasa
B’angaran sa ya koma fud’un-fud’un yana tafiya yana zancan zucci.

Bayan idar da sallar ne limami ya sanar da rasuwar Moddibo ta lasifi k’a inda jama’ar gari suka ji suka shiga cikin tsananin d’imuwa da jin mutuwar bawan Allah Moddibo, mutumin da bai dauki kansa a komai ba, yana rayuwa dai-dai da kowa Moddibo in ka ganshi baza ka taba cewa yana da alak’a da sarauta ba.

Hajiya Kattime tayi kuka tayi Ala wadai da turr! da halin mijinta,babu tamtama shine yasa zuciyar Moddibo ta buga ya mutu lokaci guda, duk da cewar ita musulmace muka ta yadda duk kanin me rai mamaci ne,mutuwar Moddibo tana alak’a da mahaifinsa Waziri,shine sila.

Humm Rayuwa kenan, me Martaba ne da Sarki! suka wanke Moddibo tsaf suka suturtashi, suka kuma kwana dashi, har garin Allah ya waye.

Mutane damk’am a harabar gidan sarautar suna jira a futo da gawar Moddibo domin su sallah ce shi, kowa da irin abunda alkairin da yake fada a kansa.

Har waye war gari Waziri bai futo ba, kuma duk irin karatun da ake cikin gidan yana ji, domin malamai ne suka taro suna ta sauke wa Moddibo al’ikur ani.

Me martaba ne ya bada Umarni a je a kira Waziri dole ya zo kan gawar danshi kafin a d’auke shi, sannan ya umarci Sarki! kan yaje ya futo da Balaraba, itama tazo kan gawar mijinta kafin a d’auke shi.

Gabansa ne ya fad’i domin kwata-kwata ya manta da Balaraba, nan take ya shiga wani yanayi da ya tuno da nauyin ta da Moddibo ya dora masa kafin rasuwar sa.

A nutse ya mike ya futa daga fadar, wani bawansa yana take masa baya, kai tsaye shashensa ya nufa.

Balaraba kuwa tun lokacin da Moddibo ya kaisu daki ya ajesu, ta shiga cikin wani yanayi me wahalar fad’a motsi kad’an tayi zataji gabanta na faduwa,lokacin da Moddibo ya zo futa kiran sa tayi ta sanya kuka, tace”Yusuf a rayuwata bani da babban masoyi sama dakai da me Martaba, tabbas yanzu na kara tabbatar da soyyayar da kake min ta gaskiya, Yusuf na baka amanar kaina, saboda kazama jigo na rayuwa ta, ina rokan Allah ya amintar da ruhimu tare”
Hawaye ya share mata,yana wani murmushi Wanda ya kara masa kyau,ya kama duk hannuwanta ya rik’e a nasa cikin taushin murya yace” Gimbiya baki da matsala dani insha Allahu karshen kukan ki ya k’are a duniya,fatana dake kawai ki rik’e amana ta,kuma ki tayani addu’a zanje in nemi yafiyar mahaifina, saboda na lura da halin da ya shiga lokacin daurin auran mu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button