GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin mamaki Maddibo yace”kana nufin kace min itace yarinyar da kake fada min dazu muna mota”

“Kwarai kuwa”
yafada idanunshi a lumshe, ya cigaba da cewa”tun ganina da ita na farko naji na tsaneta sabuda dabi’ointa na lura yarinyar tana da girman kai sosai, kai kanka kasan halina bana shiri mutum mai girman kai da nuna shi wani ne”

Girgiza kai Maddibo yayi yana cigaba da sauraronsa

Ya cigaba da cewa”babban abunda ya burgeni da ita shine, lokacin da aka kirata cikin jama’a a lokacin bukin saukar alkur’anin nasu, ta bude taro da addu’a, lokacin ta bani sha’awa sosai jin tana futar da kira’a sosai, hakan yasa, Maimartaba yayi mata kyauta nima nayi mata tawa”

Shiru yayi yana jan numfashi tsawon minti biyu baice komai ba, yana dan girgiza kansa, yaja tsaki kadan ya bude idonsa sosai wanda suke lumshe yace”inda na kara tabbar da cewar yarinyar nan bata da kirki,lokacin da zata karbi kyautar daga hannuna, in kaga irin kallon da tayi min irin na wulakanci sai ka rike baki,kwata-kwata kanta na wani gefe bataso ta kalli fuskata, ina nan da hotonan in kana bukata zan dauko maka kagani kai ma zakayi mamaki”

Shiru Maddibo yayi kawai yana sauraronsa

Shi kuma ya cigaba da cewa”a lokacin abun ya bani mamaki, ganin lokacin dana futo daga gida itace ta farko gurin mikewa domin ta ganni, kamar yadda jama’a suke yi amma yanzu gata a gabana tana dauke kai, kawai na shareta amma abunda tayi mun ya bani mamaki, sosai, naje na zauna, Shahid ya nuna min irin hotonan da yayi mana ni da ita, a lokacin na kara ganin, wukantacan kallon da ta din ga yi min,shi kuma Shahid cewa yake wai mun dace da ita sabuda yana ganin kamar “yar wani ce a garim nan kuma yarinyar tana da kyau sabuda haka kawai in shi ga,raina ya baci sosai da maganar da yayi min, wannan shine dalilin batawar mu dashi,domin da muka shiga gida, ya dame ni da zancan ta, fada mukayi dashi sosai, shine dalilin da yasa kaga baka ganshi ba kwana biyu, to wannan shine,abunda ya hadani da ita, sabuda haka,naji bana kaunarta kai kasan halina,in naki mutum to nakishi har abada wallahi”

A nutse Maddibo yace”ni dai yanzu hakuri nake baka, maganar nan ta wuce kai kayi laifi,itama tayi laifi, sabuda haka sai ayi hakuri a yafi juna,amma gaskiya banji dadin tofa mata miyau da kayi ba”

“Ok yanzu hakuri kakeso inje in bata kome”?

A’a ni bance ba,kawai ka kiyaye ko da nan gaba zaku hadu,tunda dai kasan babu abunda zai hanani auranta,sai dai idan mutuwa nayi”

“Wannan kuma abunda ya shafe ka ne, wannan yarinyar bana fata in sake ganinta,har abada kai ma ina me baka shawara ka janye maganar auranta,zai fi maka alkairi,kanemi yariyar arziki domin samawa ” yayan ka Uwa ta gari”

Cikin Sanyi murya Maddibo yace”Addu’a kawai zaka taya ni dashi a kanta, amma maganar gaskiya Allah ya jarrabe ni da kaunar ta, kuma kai ne kake mata kallon mara tarbiya Balaraba yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, abunda yasa ake mata kallon mara tarbiya dalilin sana’ar ta ne kawai”

“Ok me yasa baza ka hanata talla a cikin kasuwa, in dai da gaske kana sonta,sai ka hanata fita kawai ka killace ta guri guda,kai kanka kasan al’adar cikin gidan nan, abu mawuyaci ne su yarda ka aure ta”

“Ko kowa yaki yarda da al’amarin Maimar taba zai lamunce min,sabuda kasan halinshi da saukin kai, mutukar a kayi buncike a kanta, a gano babu wani aibu, a tattare da ita, ba zai hana kulluwar al’amarin ba”

“Ok Allah ya bada sa’a”
Abunda yace kenan, ya koma ya kwanta cikin kujera

Shiru falo yayi kowa yana sake-sake cikin zuciyarsa,daga bisani Maddibo ya mike ya nufi wani bedroom dake falon domin ya yi wanka yayi shirin bacci

Shi kuwa Sarki! da alama a falon zai kwana domin dai bashi da alamar tashi ya shiga bed din yana kwance yana dacin rai, tunani kawai yakeyi kan Balaraba, wane irin mataki zai dauka a kanta, domin duk abunda yayi mata bai wuce ba sai yaga karshen rashin kunyar ta, sai dai wannan ya zama dalilin batawarsu da Maddibo

Comment
Vote anda Share
[07/07, 22:32] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????

            _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDIGATED
TO
{ RAHAMA ALIYU}

????41

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Har karfe biyu na dare yana zaune a falo yana kallace-kallace,Maddibo ko tuntuni yayi bacci babu abunda ya dame shi, wani film yake kalla tashar Sky Moveis, sai da yaga karshen film din sannan ya mike a nutse ya kashe kayan kallon ya nufi bedroom din nasa, kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka gami da dauro al’wala, ya futo a nutse ya shirya, jikinshi, ya fesa turare sannan ya shimfida dadduma ya tada sallahr nafila kamar yadda ya saba,duk daran duniya, yana nan zaune kan abun sallah har aka fara kiran sallahr asubahi, ya mike tsaye hannushi rike da carbi ya sanya wani takalmi mai uban kyau,jikinshi duk wani gashi-gashi kana kallon takalmin kasan irin na masu mulki ne, futa yayi daga dakin nasa ya nufi kofa, har yq bude zai futa,sai ya tuna da Maddibo ya koma da baya, ya bude bedroom din da yaga ya shiga jiya, Maddibo na kwance bacci yake sosai,
Kiran sunanshi yayi”Maddibo”
Bude ido yayi dake bashi da nauyin bacci

“Ka tashi kayi sallah ni na tafi massalaci, sai kafito”

Bai tsaya ya saurari abunda Maddibo zai ce ba kawai ya fuce daga dakin

Yana futa suka ci karo da Maimarta ba ya futo tare suka jera har zuwa massalacin,

Bayan an idar da sallah suka gaisa, jama’a kowa yana so su gaisa da Maimarta ba, da yake in an idar da Sallah ya kan zauna a massalanci su gaisa da Jama’a ko kuma in da akwai daurin aure ko radin suna duk nan za’a gabatar kafin ya koma gida ya futo fada

Sarki ya na zaune kusa dashi Waziri yazo suka gaisa da dan uwanshi, da alama akwai maganar da yake so yayi, ganin haka yasa mutane suka fara futa da dai-dai da dai-dai, gurin ya rage daga Maimarta ba,sai Waziri da Sarki! Sai Maddibo dake gefe guda yana lazimi

Kanshi a kasa yace”Allah shi taimake, dama akwai maganar da nake so muyi da kai, tuntuni wallahi sai yau, nace,ko zamuyi maganar kawai a huta Allah shi taimake ka”

Maimarta ba,yana zaune hannushi rike da wani carbi mai kyau sai kalli yake,lazimi yake, kallon kanin nasa yake, yana nazarinsa sabuda yafi kowa sanin waye Waziri, duk da girmansa sam bai san abunda ya dace ba gashi bai iya yanke hukunci ba,shiyasa ko wani abu a kakawo gaban fada,ba ya wakiltashi a kai, gwara ya wakilta Sarki!sabuda yana yin abu cikin hikima da adalci,

Gyaran murya yayi yana nuna masa carbi,alamar ya daka ta tukkuna, ya cika carbin

Tsit!gurin yayi har sai da ya kammala, sannan ya dago kanshi cikin nutsuwa yace”Wace irin magana ce, wannan wacce ka boye ta ka kasa fada gashi kullum muna zama a fada, da tuni an warware ta”

“Allah shi gafarta maka, ai wannan maganar bata shafi fada, ba ta shafi cikin gida ne,”

Girgiza kai Maimarta ba yayi tsawon minti biyu bece komai ba,daga bisani ya kalli Waziri yace”ka sameni a shashen Fulani sai mu tattauna maganar, Allaj ya warware mana”

“To” To Masha Allah, Allah ya kara nisan kwana ai magana ce ta alkairi nasan kuma kai ma zakaji dadin ta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button