GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin kallo tayi masa mai kama da harara wanda hakan ya zame mata jiki shiyasa mutane suke mata kallon mace mai girman kai gami da izza da takama,

“Ban ga dalilin da zaisa in gayyace ka gidanmu ba,babu wata kyakykyawar magana a tsakanina da kai,kabari tukkuna sai an kwana biyu”

Girgiza kai yayi kawai ya mike tsaye yana kallon agogon hannushi yace”duk abinda kikace haka za’ayi Gimbiyata ina jiran kiran wayarki”

“Ok a sauka lafiya”
Tafada gami da latsa wayar hannuta,

Har ya wuce ya dawo fuskarsa a sake yace”yau baki da sako gurin Mama kilishi”?

Murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,tun sanda ta ga hotan matar a wayarshi taji tana mutukar kaunarta,sosai shiyasa duk lokacin ya zo cin abinci take hada mashi waina(masa) sabida ya fada Mama tanason wainar shinkafa, shiyasa kullum take hada masa da yawa ya kai mata,Mama kilishi har tasan da zaman Gimbiya Balaraba,
[18/06/2019 3:02 PM] Binta Umar Abbale: Mikewa tayi a nutse ya bita da wani mayataccan kallo,duk tana kallonshi, kawai sai taja ta tsaya gami da cewa”kayi gaba ganinan zan kawo maka sakon har gurin da ka aje motarka”

“Menene hujjarki ta fadar haka,? Kina nufin in wuce gaba ke kya biyo ni daga baya, ban yadda ba”?
Yafada gami da bin ta da wank kallo mai dauke da so da kauna

Gaba tayi kawai bata saurare shi ba sabida ta riga ta San mugun nacin sa

Bayanta ya bi yana kare mata kallo ji yakeyi in bai auri yarinyar rayuwarshi zata shiga garari,

Hauwa tasa ta hada mata komai cikin wani take away na mussaman an nan nadeshi da wata Leda mai kyalli a sanya leda mai zurfi, ta fito rike da ledar a hannunta,ta mika masa, “gashi a kai mata ace ina gaidata da kyau”

Cikin murumushi ya karbi ledar har yana kokarin hadawa da hannuta tayi saurin zare hannunta ledar ta kusa faduwa kasa, sai harararshi take

Basarwa yayi yace”zataji insha’Allahu, kizo ki rakani gurin motana”

Share shi tayi ta kawai ta koma gurin zamanta, ta zauna gami da dora kafa daya kan daya, babu abinda ya dameta.

Girgiza kai kawai yayi ya wuce,ya na mamakin izza da mulki na yarinyar ya lura abin a jikinta yake,ko shi da yake dan saurata ba ya yin irin abinda take,asalima sam bayaso a san cewa yana da alaqa da masarautar garin, sai dai dayawa daga cikin abokanshi in sun ganshi cikin kasuwar sai su riqa mamakin mai yakawoshi har dai suka fahimci gurin Balaraba yake zuwa, to babu irin maganar da ba’a fada masa ba a kan Balarabar amma yayi kunnan uwar shegu da jama’a sabida shiyasan wacece Balaraba a cikin zuciyarsa.

????YANZU MUKA FARA
[20/06, 05:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

[6/19, 12:18] Binta Umar Abbale: [????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????????????????????????????

             *NA*

®BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYA
Nana Khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani writes
Association????????

BISIMILLAHIR
RAHAMANIR RAHIM

????28

_ Biyar saura Ashiru mai Napep ya zo daukarta dama lokacin suke tashi sai da tabbatar su Hauwa sun tsaftace mata gurin komai an wanke an ajeshi in da ya dace sannan ta bawa ko wacce hakkinta sukayi sallama cikin mutumci, Ashiru ya dauketa suka bar kasuwa mutane sai zindanta sukeyi mussaman wadanda suka kawo mata maganar banza a kasuwar ta ci musu mutumci,shiyasa sam basa iyayin munafurce-munafurcensu a gaban idanta sai sun ga bata guri
[6/19, 20:48] Binta Umar Abbale: Abin mamaki suna zuwa dai-dai danja kamar dazu suka tadda uban gosolow gashi yamma tayi duk “yan kasuwa kowa yana kokarin komawa gida, amma an dakatar da jama’a , cikin mamaki Balaraba tace ” wai me yake faruwa ne?

kallonta yayi ta cikin mudubin Napep din yana shakkar abinda zai fada mata,yace “ai Sarki Almansor ne ya dawo, ashe sun je daurin aure can gwarzo, maimarta bai samu damar halarta ba sai ya wakiltashi dashi da mai girma waziri Rayyanu”

Tsaki taja tace”Allah ya kyauta, gaskiya an shiga hakkin jama’a dayawa wallahi, daga zai wuce sai a dakatar da jama’a sabida takama da sarauta,sam wannan bazai iya mulkin garin nan ba”
ta karashe maganar tana tabe baki

“yar dariya Ashiru yayi yana satar kallonta gefe guda kuma yana jin tsoran maganar da zai fada mata, amma sai ya dake yace” nura Gimbiya sam Sarki Almansor baya burgeki,kuma baki fahimce shi bane mutum ne shi mai sauqin kai gami da iya mu amula da jama’a yana da tausayin nakasa dashi sosai, matsalarshi kawai muskilanci shiyasa mutane suke masa kallon mutum mai girman kai da izza”

shiru tayi masa batace komai ba, sabida ta lura da Ashiru yayi nisa da kaunar Sarki!

wayarta tafito da ita tana dubawa ranta a bace, ta najin yadda motoci suke gudu kan titi dago kanta tayi tana ya muste fuska, cikin rashin dace idanunsu suka hadu dana juna, cikin sakon daya ya gane ko wacece,sai yayi saurin kauda kanshi gami da gyara kwanciya cikin motar

tabe baki tayi ta kauda kanta,ko daga bacci ta tashi zata iya ganeshi sabida ranar saukarsu ta kare masa kallo, shiyasa in taga ana rububin ganinshi sai tai ta jin haushi sabida ita sam bata ganin kyawunshi da mutane suke zuzutawa

bayan motarshi ta wuce sauran motocin suka dinga wucewa a jere har suka kare,sai sannan a kabawa jama’a damar wucewa,

Agogon dake daure a hannunta ta kalla biyar da rabi sun samu kosan rabin awa a tsaye a titi, giriza kai kawai tayi a zuciyarta tace idan tasan wannan bacin ran zata samu da babu abinda zai kaita fitowa wallahi

Sabida haka ana tsaka da kiran sallahr magariba ta karaso gida, tun daga nesa ta hango Shamsiyya na suyar doya da kwai matasan unguwar duk sun kewayeta

tana karasowa gurin warin taba ya sata saurin toshe hanci tana kauda kai, da kyar ta samu ta ratsa ta tsakiyarsu tana kokarin shiga gida,

Iro ne ya tare mata hanya yana wani washe baki yace”Kanwata kin dawo kenan?

Sama-sama ta kalleshi tana kokarin wucewa tace”e wallahi”

ganin tana kokarin wucewa tabarsha a gurin yasa ya kira sunanta,

tsayawa tayi tana kallonshi yace”tuntuni nake so muyi wata mahimiyar magana dake dama”

sabida sanin da tayiwa Iro da kafirin nacin tsiya yasa tace masa”yanzu dai lokacin sallah ne kaga isha’i ta kusa yi gashi banyi magariba ba kabari sai anjima sai muyi maganar ko”?

Washe baki yayi wasu jajayen hakora suka bayyana Balaraba tayi saurin dauke kanta zuciyarta ta wani mugun tashi,lallai Iro ya bata rayuwarsa

yace”babu damuwa ai zamu hadu anjima,yau bazan fiya yawon dare ba, watakila ma a gida zan kwana”

ko saurarsa batayi ba tayi saurin shigewa cikin gidan sabida yadda taji zuciyarta tana tashi warin tabar wiwi da ganye duk sun cika soran gidan.

Muje zuwa
[21/06, 18:40] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

®BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????29

__ “Salamu alaikum”
Balaraba tayi sallama cikin gidan nasu, babu wanda ya amsa mata,duk da cewa dukkaninsu suna zaune a tsakar gidan, har Lantana ma domin ita ma bata dade da dawo wa daga yawon tallata ba, tana zaune ta mike kafa kan tabarma tana lissafa kudin cinikinta, ita kuma Uwa na gaban murhu tana soya a wara dake bayan tayi ta safe wacce Mabaruka take dauka to da yamma ma sai ta kara dora kasko, bata tashi sai wajan karfe goma na dare, ita kuma Shamsiyya a waje take soya doya da kwai,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button