GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fuskarshi a sake yace”muje can gurin maganar sirri ce”

Jiki a sanyaye Salihu ya mik’e ya bi bayan Sarki! sauran abokanshi suka bisu da kallo cikin mamaki,

Kai! wannan guy, d’in me ya kawoshi gurin Salihu, Allah yasa dai ba wani abun ya jawowa kansa ba”
Maganar daya daga cikin matasan dake gurin kenan, “To wa yasa ni mudai babu ruwan mu”
na kusa dashi yafad’a ya cigaba da shan raken sa.

Can wani gefe suka tsaya,wanda yake da k’arancin haske, A nutse Sarki! ya kalli Salihu yace”Abokina kasan wata yarinya Balaraba a nan unguwar”?

Shiru yayi na tsawan minti biyu yana tunani can yace”Eh na san wata a can lungun take” yafad’a yana nuna lungun gidansu Balaraba, ya cigaba da cewa, “amma gaskiya ba a fiye kiran ta da sunan ba sai a gidan su mu dai matasa muna kiranta da Gimbiya sabuda girman kanta, gashi ita ba ” yar kowan kowa ba, a na tunanin ma Uwar da ta haifi baban ta Mayya ce”

Shiru Sarki! yayi yana nazarin maganar yaron, daga bisani yace” kasan gidan nasu ne,inaso ka rakani gurin baban ta”

“Nasan gidan mana”
Salihu yafad’a ya cigaba da cewa”k’anin ta Walidi abokina ne, Allah yasa kai ma ba wani abun tayi maka ba, dan jiya ma wanta Iro ta cirewa d’an yatsa guda, yanzu haka yana can kwance yana jinya”

Cikin mamaki Sarki! yace” garin yaya mace kamar wannan zata cirewa saurayi kamar ka d’an yatsa guda, dame ta cire masa”?

“Humm Wannan yarinyar ai inda kasan ” yar daba haka take, da wuk’a take yawo, mu dai inda mukaji wai tana so shi yayan nata yayi lalata da ita dama kuma shine zai aure ta, shine da yak’i amuncewa ta futo da wuk’a ta yanke shi, muje in raka ka kaji a bakin mutan gidan nasu”

Cikin mamaki Sarki! yake bin bayan Sallau, yana al’ajibin abunda Salihu ya fad’a masa yanzu al’amarin yarinyar har ya kai haka

Yayi mamaki sosai da inda yaga yarinyar take rayuwa a rin wannan lugun mai tattare da k’azanta da bola amma take wa mutane kallon banza,

Shamsiyya na zaune a kujera “yar tsuguno tana lissafa cinikin a wara, ta bisu da kallo, da Sauri Sarki! ya dauke kanshi zuciyar shi na wani irin tashi, sabuda kauri gami da zarnin futsari da warin bola da ya cika masa hanci, hankici ya futo da shi yana d’an goge fuskarsa cikin basarwa, Salihu ya k’arasa kusa da ita yace” Shamsiyya babanku yana nan”?

“Bayanan menene”?
tafad’a kai tsaye

“Dama wannan guy din ne yake neman shi”

Da sauri ta mik’e ta karasa kusa da Sarki! cikin kwarkwasa tace”sannu ina wuni”?

Dauke kai yayi da sauri, sabuda wani irin k’auri da yaji tana yi yace”lafiya lou alhamdulilahi”

“Salihu yace ” wai kana neman babanmu”

“Eh hakane”?
yafad’a ba tare da ya kalleta ba.

” Bayanan amma bari in sanya yaro ya kira maka shi yanzu”
tafad’a tana kokarin tafiya, sai wani murgud’a mazaunai take,wai dole sai ta burgeshi,
Tare suka jera da Salihu domin futa bakin lungu ko zata ga Walidi ta tura shi ya kira baban nasu domin tana ganin wannan bak’on nasa na alkairi ne.

Kanshi a kasa yayin da ya zuba hannuwansa duk biyun cikin aljihun jins d’in dake jikinshi,yana jimanta labarin da Salihu ya bashi a kan Balaraba, lallai in ko hakane yarinyar ba matar aure bace.
kanshi a kasa ya fara jiyo wani mugun k’amshin turare mai dad’in gaske, d’ago kansa yayi, karaf! suka had’a ido ta cikin gilashin dake idonshi yake kare mata kallo, a kwai hasken fitala tunda da wuta lokacin, d’auke kanta tayi cikin izza! da tak’ama take tafiya, tana sanye da wasu riga da wando pakistan ta masu kalar blue da pink da adon wasu manya-manyan stons masu shek’i ta yane kanta da wani mayafi wanda ya sakko kad’an ya rufe mata k’irjin ta amma duk da haka ana ganin tudunsu, wandon ma duk da burgujeje ne,amma bai hana bayyanuwar sharp dinta ba, masu gigita lafiyayyan namiji kai har wanda ma bai cika lafiya ba, in ya kalli duri da k’irar Balaraba sai yayi sha’awa, shima da sauri ya kauda kai, ya d’an sosa kansa kamar yadda ya saba, yace”Jimana “yan mata”

Tsayawa tayi tana shan k’amshi, gefe guda kuma tana tunanin a ina tasan wannan muryar.

Cikin Yanayin tafiyar shi ya karasa inda take tsaye tana masa wani kallo sama sa k’asa,tana tab’e baki, har ya k’araso ya tsaya dab da ita, tayi saurin matsawa baya, tace”Lafiya Malama”?

Gyara murya yayi ya k’ara yin k’asa da ita yace”amm” ina neman maigidan nan ne wanda kika futo daga ciki”

D’auke kai tayi ta d’an turo baki gaba, tace”bayanan” tana fad’a tayi gaba,tana d’aga kai sama, as,usul

“Ok yanzu a ina zan same shi a kwai abunda ya kawo ni, gurin shi”
yafad’a yana d’an daga muryar shi sabuda tayi masa nisa kad’an.

Tsayawa tayi tace”in zaka iya tsayuwa nan ka tsaya ka jira shi,yanzu zai dawo tunda tara tayi”ta k’arasa maganar tana k’okarin tafiya a karo na biyu, da sauri yace”d’an tsaya mana, “yan mata ai ban gama tambayar ba”
Wani irin kallo ta watsa masa,wanda yasa shi saurin dauke kai, “wai me zan maka ne, uhum? ka tambaye ni na baka amsa,sai me kaga ina da uziri ni,yi sauri kafad’i abunda zaka fad’a in wuce abuna”
Ranshi ne ya b’aci sosai! jin yadda take masa tsawa sai kace wani sa’an ta, lallai yarinyar nan baza ta canza ba, kanshi ya sosa kad’an yace”naji kince tara na dare tayi, ke ina zaki a matsayinki na “ya mace me kamun kai, babban abun mamaki ma kin ci uwar kwaliyya gami da turare mai dad’i me zai hana ki tsaya ki tayani hira kafin Baban yazo”

Wanini irin kallo take masa,wanda kana kallonsa kasan ta shirya wulak’anci, a ya tsine tace”baka da hurumi a kan abunda kake tambaya ta,haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya tayi zak’i, aikin banza kawai ni natsani munafurci wallahi, ka tambaya an baka amsa ka tsaya neman magana”
Wani irin d’aci-d’aci ya fara ji a bakinshi,tsigar jikinshi ta fara tashi, tunda yake a rayuwar shi babu “ya macan da ta tab’a ci masa mutumci irin wannan sai wannan yarinyar,
Daure zuciyar sa yayi kawai yana bin ta da kallo, tabbas ya gazgata abunda Salihu ya fad’a masa yanzu a kanta

Tun daga Nesa Shamsiyya ta hango Balaraba da Sarki! a tsaye, tamkar zata tashi sama haka ta k’araso gurin zuciyat ta tana tafarfasa, tace” ke dabbar Araf! mayyar maza, wato ke duk inda ki kaga namiji sai kin nuna masa ke karuwa ce ko, to bari kiji wannan da kike gani yafi k’arfin wallahi sai dai ki gani ki kyale, domin shi dai ba d’an iska bane irin ki”
Shamsiyya ta karashe maganar tamkat zata tsone mata ido

Abun mamaki sai yaga kawai Balaraba ta girgiza kai zata wuce ba tare da tacewa Shamsiyya komai ba, a zuciyarsa yace”wato wannan yarinyar rashin kunyar ta da rashin mutuncin ta akan mu yake” kallasa Shamsiyya tayi tana wani fari da ido ta jawo mayafin da Balaraba ta nannad’e kanta dashi Balaraba tayi saurin dafewa sanadin haka har sai da wayarta ta fad’i k’asa had’e da pose d’ita sabuda in ta cika, Shamsiyya zata iya cirr mata kuma babu hula zai ga gashin ta, Shamsiyya tace”kaga wannan wallahi kar ka yadda da ita,sai ta lalata ka, dan muguwar makira ce ta iya kissa da kisisina duk da haka takewa maza irin ku masu kud’i”

A dake! yace”to ke wanene yace miki ni mai k’udi ne, sakar mata mayafi ta tafi”
yafad’a a cunkushe, dan yaji haushin abunda tayi Balaraba ko meye dalili oho

Sakar mata mayafin tayi tace”gayyar tsiya gayyar datti da najasa sai an dawo”

Wuce Balaraba tayi bata kallon gabanta, sabuda tsanani b’acin rai, karo sukaci da Sallau ya shigo lungun yana baza babbar riga sai kace wani limami ya kalleta, a banza ce yace”wallahi in baki dawo da wuri ba zaki zo ki tadda mun kulle k’ofarmu domin baza mu tsaya jiran ki ba”
yana gama maganar sho ya shige bagaz-bagan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button