GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL


Hajiya Kattime ce zaune a falo tana jiran futowar mijinta, sai gashi ya futo cikin shirin zaman fada, tace.”Allah ya taimake ka ina da magana da kai.” A k’asaince yace.” Ina sauraron ki,zan shiga fada ne.” Zama ta gyara tana fuskantar sa sosai tace.” Dama tambaya nake so in maka.” Yace.” Ina sauraron ki.” “Me yasa da yaran ka suka a mutu baka nuna damuwar ka ba? Kuma me yasa baka so a shiga wancan dakin na kulle.”? A hasale! Yace.” Ke saurara min da maganar banza haka.” Shiru Kattime tayi ya cigaba da cewa.” Idan mala’ikan d’aukar rai yazo kan ‘yayana sai in hanashi kan wane dalili zan tashi hankalina zaki mutu zan mutu zamuje inda sukaje,saboda haka babu dalili da zai sa in tada hankalina, bayan wannan kuma kina maganar wancan dakin dake kulle dakin sirri na ne,ko da wasa kar ki kuskura ki kai kanki gurin zan iya sakin ki a kan hakan.” Kattime ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki.
Futa yayi ya bar ta da tunani.


Mabaruka ne da saurin ta cikin mota zasu dawo gida, duk suna cikin maye, Alhaji Ashiru sai fafara gudu yake, ba tare da bin ka’idar tuki ba, wata k’atuwar mota ta buge su,suka gangara cikin daji,ihu!! Mabaruka take kurmawa tana k’okarin futowa ta fado kasa motar ta bi ta kan kafafunta, ta cillata can gefe, motar ta cigaba da katantanwa a gurin, tayi raga-raga Alhaji Saminu kansa ya fashe take ya amsa kiran ubangiji ita kuma Mabaruka ta suma.


Hajiya Kattime na zaune a inda take tun bayan futar mijin nata take tunani kan yadda zata yaudare shi har ta samu nasarar shiga dakin sirrin shi, murmushi tayi lokacin da ta tuno abunda zatayi masa, gyad’a kai tayi a fili tace.” Insha Allah sai asirin ka ya tuno mutukar ba abun kirki kake shukawa ba.”

‘Yan a gaji ne suka kawo dauki gurin, ba tare da b’ata lokaci ba,a ka dauki Mabaruka a kaita asibiti ,shi kuma Alhaji Saminu cikin motar suka duba suka ga katin sa da shaidar garin da yake, nan suka saka gawar sa a mota domin su kaishi dangin sa.


Ranar Sarki! Da Balaraba sun sha soyayya sosai ji suke tamkar su kadai suke rayuwa a duniyar Balaraba har fargaba take su koma gida, in ta tuno da masifaffan kishiyoyinta wanda ko anan ma sun dunga damunsa da kiran waya babu dare babu rana.

Sai k’arfe shida shu Shahid suka shigo gidan,dama me girma governor ya koma lokacin da yayi kwana uku, nan sukayi sallahr magariba, suka zauna suna cin abunci suna hira, Shatima ya futo da magunguna ya mik’a masa, b’ata fuska yayi yak’i karb’a.Balaraba na kallonsa, ta kalli Shatima a hankali tace.” Ka bari zan bashi in anjima har na shafarwar ma.” Shahid yace.” Hakan yayi ke in kika bashi sai yafi karb’a mu kam kullum sai ya bamu wahala.” Murmushi tayi kawai. Gyaran murya yayi yace. ” Na fa gaji da zaman gidan nan, Dole gobe nima na futa in kusanta kaina ga Allah don haka sai Ku shirya futa dani.” Shahid yace.” Allah ya kaimu goben muna fatan a sanya mu cikin addu’a.” Yace.” Jikina na bani insha Allahu da k’afafu na zan koma gida.” Shatima yace.” Idan Allah ya yarda kuwa haka muke so.” Nan suka cigaba da hira suna kallo, sai k’arfe goma da rabi sannan sukayi sallama kowa ya shige makwancin sa. Balaraba ce ta tura shi bedrom ta d’auko masa kayan bacci, ta taimaka masa ya sa, ta sanya nata sukayi kwanciyar su, cikin so da kaunar junan su.
????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA

ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.

DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????114

To bayan likitoci sun gama binkicen su a kan Mabaruka nan suka yanke shawarar yanke mata k’afafu domin babu wani sauran dubara da ta rage k’afafun Mabaruka duk sun karye karaya mafi muni! Wanda ko dori akayi baza su k’ara amfani ba, Mabaruka tana ji tana gani aka yanke mata k’afafu, ta futa daga cikin hayyacin ta saboda azaba fatan mutuwar ta kawai take.


Ranar Juma’a da misalin k’arfe d’aya shaura na rana, Waziri ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya bude dakin sirrin shi ya shiga tare da kullewa, Hajiya Kattime na zaune a falo tana kallonsa, ya shiga ya fi minti goma a ciki sai gashi ya futo da sauri, yaja kofar tare da murza mata mukulli ya cire ya futa ba tare da ya kalli inda take ba. Kamar wacce aka bawa umarni ta mike Zumbur! Kofar dakin taje tana murza wa, abun mamaki kofar ta bude, bata tsaya tunanin komai ba ta afka cikin dakin, abunda ta gani yayi mutukar gigita mata tunani,nan take sai kanta ya fara juyawa ta zube a gurin a sume.!


Tsaf! Ta shirya shi cikin wani parkinstan irin na maza sunyi masa kyau sosai kanshi sanye da hula irin ta Larabawa tsaf idan ya shiga cikinsu zai saje, turare ta d’auko tana fesa masa, ya rike hannunta yana murzawa, murmushi tayi tace.” Ka bari in fesa maka fa kar Ku makara gasu Shatima na jiran ka.”

A kasalance yace.” Kece duk kin gajiyar dani jikina duk ciwo yake.” Hararsa tayi kad’an tace.” Kana da Neman magana ko.” Murmushi yayi tare da lakuce mata hanci yace.” Gaskiya ne ai.” While chair d’in ta kama tana k’okarin tura shi domin ta futa dashi farlo, yace.” Bari ki gani da izinin Allah yanzu zan taka k’afafuna.” Balaraba ta matsa gefe tana kallon ikon Allah, ya yunkura bakinsa d’auke da Addu’a sai gashi tsaye da kafafunsa, cikin mutukar farin ciki ta furta “Alhamdullahi ala kullu halin.” Shima cikin farin ciki yace.” Allah ne abun godiya.” K’okarin futa take yi ya rike hannunta da sauri yana fad’in ” INA zakije kece ‘yar jagora ta fa.” Cike da farin ciki tace.” Wallahi duk na rasa ya zanyi saboda farin ciki,hak’ika ubangiji naji rokan bawansa ne.” Yace.” Hakane mutukar bawa zai mik’a lamarin shi ga ubangijinsa to babu shakka dukanin Matsalar sa ta kare.” Rungume shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya, cire ta yayi daga jikinsa yana Dan murmushi yace.” In kika karya min alwala fa , zamuje massalaci yanzu in mun dawo kiyi min tanadi me kyau.” Ta sinne kanta kafadar shi suka futa a haka

Su Shahid na zaune suna jiran futowar sa,kawai suka ganshi ya futo da k’afafun sa,tare suka mike tsaye cikin mamaki ! Shatima yace.” Alhmdullahi Alhmdullahi ala kulli halin, yaushe ka mike ka fara tafiya.” Suka fada a tare. Balaraba tace.” Yanzu ne kamar da wasa wallahi ya mike.” Shahid ya zube gurin yana sujjadar godiya ga Allah,shiko Shatima waya ya futo da ita zai kira mutan gida, Yace.” Ka bari tukkuna muje mu dawo ko meye sai ya biyo baya in ka kira mutane yanzu zasu hana mu ibada.” Shahid yace.” Hakane bari muje mu dawo kawai, tare suka futa har da Balaraba tana sanye da dogun hijabinta fari tass dashi mijinta ya rike mata hannu suka fara tayi,dake gidan da suke bashi da nisa da harami da kafa suka tafi,
Bayan an idar da sallahr jama’a suka zauna massalaci suna add’a tare da karatun alkur’ani me girma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button