GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Uwa! Ta fashe da kuka ta zube gaban Mama tana k’okarin rik’e mata kafafu Mama ta janye k’afar ta cikin tsoro tace”Baiwar Allah me ya kawo ki nan”

Cikin kuka Uwa! Tace”Ki gafarce ni Uwar dakina ban so na shigo nan da wannan sigar ba, raina ne a bace” ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa”Ni dai sunansa Uwa! Matar Sallau a da kenan Wanda yake a matsayin uban Balaraba, wannan kuma” tafad’a tana nuna Lantana da tayi tsilli-tsilli a tsaye har yanzu hannuta na dafe da kuncin ta, ta cigaba da cewa” Wannan ita ce Lantana Kenan Uwar mijina Sallau ta kasance muguwa CE azzalima me son kanta duk wata masifa Dana ke ciki dani da “yayana itace sila, hakanan duk wani bala’i da Balaraba ta shiga itace Sila, itace tayi sanadiyar kashe kishiyar ta Suwaiba mahaifiyar uban Balaraba Ayuba kenan, bayan haka kuma itace tayi sanadiyar kashe iyayen Balaraba, itace tayi sanadiyar da ” yayana suka zama karuwai itace ta nuna min hanyar bin gidajan malamai da bokaye gami da “yan bori,, tun lokaci da mukaji labarin auran Balaraba da Sarki! Muka bazama gurin malama domin mu rusa abun Allah bai yi ba, sai da mukayi nasara karbo asiri gurin malamin mu Wanda aka je aka debo kasar kabari aka had’a dashi domin a zubawa balaraba. Kan hanyar ta ta wucewa idan ta tsallaka ta hau kace,sai Shamsiyya ta maye gurbin ta”

Mama ta rafka Salati da sallami tace”Da kanku kuka aikata wannan aiki”?

Uwa! Ta daga Kai tana share hawaye, ta cigaba da cewa”Duk nau’in kayan asirin yana gurin ta wannan zaman da kuke tare da ita bashi da amfani ne tazo ne domin ta aiwatar da kudirin ta,, Yau a kanta Sallau ya sake ni saki uku duk ya manta hallacin da nayi masa na ciyar dashi na shayar dashi duk ya manta shiyasa kawai naga gwara inzo in tona mata asiri”

Lantana ta dunga rantse-rantse cewar k’arya take mata duk sharri NE ta nayiwa Balaraba bakin ciki NE ganin ta a gidan sarauta, Balaraba kuwa in banda kukan bakin ciki babu abunda take,, lokacin su Sadiya da Usuman suna makaranta,, wani irin tausayin ta ne ya dura a zuciyar Madabo mahaifiyar Halisa kenan Lallai yarinyar tana ganin rayuwa.

Mama tace”Duk Ku rufe min bakin ku anan, sukayi shiru,, suna zare ido kallon Lantana cikin bada Umarni tace”Je ki d’auko min kayan asirin”

Lantana babu musu ta mike simi-simi ta shiga dakin da take, shiru falon yayi kowa na sake -sake, Lantana ta dawo hannuta rike da bak’ar Leda ta aje gaban Mama,, Cikin kunya da tsarguwa.

Mama tace”Bud’e muga abunda yake ciki”

Hannu na rawa Lantana ta fara bude ledar,, Sosai Mama take mamakin ganin kayan asiri Wanda duk tarin kasa ne da wasu saiwowi tace”Wannan itace k’asar kabari”?

Daga kai Lantana tayi cike da kunya

“Wannan fa”?
Tafad’a tana nuna d’aya ledar.

Baki na rawa tace” Wannan yace”A sama ta a abunci sunan shi shashatau zata mance kowa bayan ta hauka CE”

Mama tayi murmushi me ciwo tace”Kin ce da k’arya ake miki”

Lantana ta hau inda inda

Daga mata hannu Mama tayi tace”Ya Isa”

Shiru tayi gami da sunkuyar da kanta kasa

Mama tace”Ina son duk Ku biyun kuji tsoran Allah Ku tuna yana ji yana kallon Ku da dukkanin abunda kuka aikata, Hak’ika shi ubangiji na kowa da kowa ne kuma mai amsa bukatun bayin sa, hakanan me yafiya ga Wanda ya sab’a masa,, Hak’ika kun aikata babban kuskure na had’a Allah da waninsa,, babu me yi sai Allah shine ya hallice mu ya hallice duk wani Abu me rai da Mara rai tsirai zafi sanyi ruwa wuta da sauransu shi ya halli rai da mutuwa,,, ina rokan Ku Ku tuba tun kafin lokacin mutuwar Ku yayi domin babu Wanda zai dawwama duniya, ga Balaraba nan a zaune a gaban Ku ku nemi gafara ta zata yafe muku abunda kukai mata kunga bata da hakki a kanku gashi da kanku kunzo kun tonawa kanku asiri,,, bayan kun nemi gafarar ta kuje kuyi ta istigafari domin Neman yardar Allah”

Uwa! Tana kuka wurjajan ta matsa kusa da Balaraba tace”Ki yafe min abunda nai miki Wanda na sani da Wanda ban sani ba,, nasan na cutar da rayuwar ki nayi miki sharri da kazafi gashi duk abunda nake jifan ki dashi bai same ki ba sai alkairi abun sai ya koma kan “yayana nasan hakkin kine wallahi”

Share hawaye tayi tace”Uwa! Ki daina kuka kinji ko har yanzu kinanan a matsayin uwata kuma na yafe miki duk abunda kikayi min Allah ya yafe mana baki d’aya”

“Nagode-nagode nagode sosai Balaraba Allah ya baki zaman Lafiya da mujin ki”

Mama tace”Amin haka ake son mumunin ya zama me ya fiya”

Lantana ma ta matsa kusa da ita tana kuka sosai Sam ta kasa magana.

Balaraba ta rike hannunta tana fad’in nasan abunda kike so kice”Na ya fe miki, dama tun tuni na ya fe miki kuma har yanzu kinanan a matsayin kakata naji mutukar dad’i da kuka gane gaskiya.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????104

Mama ta kalli Shafa’atu tace”Ki d’auki wannan kayan tsubbu kije ki k’ona su can bayan gida, ubangiji Allah ka rabamu da sharrin zuciya”

Jakadiya tayi bisimillah ta d’auki ledar dake aje gaban Mama ta futa daga d’akin domin taje ta aiwatar da aikin da aka sata.

Madabo tayi musu wani kallon banza tace”Ya kamata Ku zo a mai daku gida domin zama daku annoba ne,wallahi Fulani ki barni da halina kawai amma na tsani mutum me asiri wallahi”

Murmushi Fulani tayi tace”Na san halin ki ciki da bai don me yasa bakya shiri da Kulu ai saboda halin ta ne”

Madobo tace”Wallahi kuwa ai Kulu tayi nisa sai addu’a”

Mama tace”Ita kad’ai ce magani”

Shiru falon yayi, kunyar duniya ta ishi su Lantana sun kasa d’ago kai su kalli mutane,,Balaraba ma kanta na k’asa tana sak’e-sak’e, k’amshin turaran sa ne ya gauraye falon,, da sallama ya shigo cikin yanayin tafiyar sa ya zauna kusa da mamansa.

Kwarjinsa da haibar sa ya cika falon, Lantana duk dadewar ta a gidan bata tab’a ganin shi ba sai yanzu, bakinta na rawa tace”Ranka ya Dade ya barka da yamma”

A nutse ya galli gefan da take ya amsa Cikin yanayin muryar shi.

Mama tace”Kakar Balaraba ce nasan baka gane ko wacece ba”

Mai da ganinsa yayi kan Lantana wacce tayi muzu-muzu a zaune tana tsoran kar Mama ta fada masa halin da ake ciki,, minti biyu yana kallonta yaji sam matar bata kwanta masa,, a hankali ya Dora idonsa kan Uwa! Ta zaune sai gumi take cikin zuciyarta take cewa dama wannan ne Sarki! Almansur din? Lallai Allah yayi hallita a gurin,, ina Shamsiyya ina shi,, a ya zama dole ta sanar da Shamsiyya cewar ta daina wahalar da kanta ko mutuwa zatayi ta san Sarki ya fi k’arfin ta,, Ya mutse fuska yayi ganin wata koriyar kwanta a idon Uwa! Abun k’yamk’yami yace”Ita kuma wannan fa”?

A hankali Mama tace”Matar Kawun ta ce, sunanta Uwa!” Tunda yaji haka ya d’auke kansa zuciyarsa tana tashi tunda ya kalli fuskar Uwa! Babu kyawun gani,, gai sawa sukayi da Madabo cikin mutum ci da girmama juna,, ya gaida mahaifiyar shi a mutumce, falon yayi shiru kowa da abunda yake sak’awa a zuciyarsa

Tunda ya zauna a gurin yake so su had’a ido da ita,, Allah bai bashi iko ba, itama gane hakan ne yasa taki d’ago kanta sai kara sunkuyar da kanta take.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button