GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

A nutse ta futo daga d’aki nta ta jawo k’ofar gami da sanya mata kwad’o, Lantana na tsaye bakin k’ofar futa hannunta rik’e da wani k’aramin buhu da alama kasuwa zata shiga, wani kallon banza ta watsawa Balaraba, ta ci gaba da magana da Uwa! dake zaune a kujera “yar tsugono tana faman soyawa a wara, gaishe su tayi, suka k’i amsa wa, tace” Matar Kawu Ina antashi lafiya”?
Sadiya dake sunkuye tana wanki bakin rijiya tace”lafiya lou Balaraba,kin futo”?
“Eh matar Kawu”
Balaraba tafad’a tana k’okarin barin gurin.

“Allah ya bada sa’a”
Matar Kawu tafad’a ta cigaba da wankin ta.

“Ameen” Balaraba tafad’a ta nufi kofar d’akin Iya.

Iya jiki yayi sauk’i suka gaisa a gurguje, ta aje mata kular abuncin su Sadiya tayi mata sallama ta futa.

Ashiru yana cikin Napep yana jiran futowar ta, dan haka tana shiga suka gaisa, cikin mutumci yaja Napep din suka bar Unguwar.

Daf da zasu shiga kasuwar wayar ta tayi kara, tana dubawa taga Modibbo ne, d’aga wa tayi tace” Ina titin jark’asa yanzu, zan tsaya dai-dai masu sai da lemo da a yaba sai kasame ni a nan”

“Ok gani nan zuwa”
Moddibo ya fad’a gami da kashe wayar.

Futa tayi daga Napep d’in ta sallami Ashiru,

Nik’ab d’inta ta futo dashi ta sakaye fuskar ta,sabuda zurga-zurgar jama’a duk da safiya ce, ko minti goma batayi ba, taga wata mota mai kyau tayi parking a gabanta, d’auke kai tayi domin tasan ba motar Moddibo bace, futowa yayi yana murmushi, yace”Gimbiya wannan shan k’amshin naki yana burge ni, gaskiya dole maza su dunga jin shakkar ki”
jin muryarsa yasa ta waigo da murmushi a fuskarta tace”barka da zuwa”
“Barka kadai Gimbiya,shigo mota mana” yafad’a yana bud’e mata k’ofar motar, tunda take bata tab’a shiga motarsa ba sai yau, sabuda haka a nutse ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe, ya zagaya ya bud’e ya shiga shima,

“Maddibo ya kalleta a nutse yace” wannan nik’ab d’in yayi miki kyau Gimbiyata”

K’okarin cirewa take, tace”kaga ni ko ala dole nake sashi sabuda kallon da ake damuna dashi”

“Nima kinyi min gata”
yafad’a da murmushi a fuskarsa,ya cigaba da cewa”da zaki dinga sawa daga nan har lokacin auran mu”

Kallonsa take cikin nutsuwa tace”Yusuf da gaske kana sona”?

“Kwarai kuwa”
yafad’a cikin shauk’i yau gashi ga ita

Idanun ta ne ya fara tara ruwa tace”zaka iya aure na dani da k’anne na biyu wato Usuman da Sadiya”?

Cikin tausayi yace”kwarai kuwa, duk abunda kike so ina so balle Usuman da Sadiya Gimbiya ki kwantar da hankali, in sha Allahu zan rik’e ko da amana”

Hawaye ne ya fara zuba a fuskarta, taso ta danne kukan amma yak’i dannuwa, tace”Nagode sosai, inaji a rayuwata bani da mai k’aunata kamar ka, na auna ka sosai na lura tsakani da Allah kakeso na, ba wani abu nawa ne yake burgeka ba,shiyasa na yanke shawarar tsayar dakai a matsayin mijina kuma Uban “yayana, sabuda haka in ka shirya kawai ka futo muyi aure in huta da bala’in da nake ciki”

Shima kamar zai yi kukan yake rarrashin Gimbyar tasa duk hankalinsa ya tashi, yace”kinyi magana a kan gab’a Gimibiya, dama ke kad’ai nake jira ki amunce min naj dad’i insha Allahu zaki futq daga halin da kike ciki zan aure ki domin kyawun halinki,ba dan kyau da wani abu naki ba, ni ina sonki tsakani da Allah” ya karasa maganar jikinsa na kyarma, ji yake kamar ya yaye mata damuwar dake damunta.

Rarrashin ta yake har sai da ya ga damuwar da take ciki ta ragu, domin har dariya tai masa,sai suka cigaba da hirarsu cikin so da k’auna, yace”yau baza ki shiga kasuwa bane”? girgiza kao tayi tace”yau bazan shigaba,zan koma gida ne, domin a kwai sauran aiki da nabari, zan tare a sabon gidan da nakama haya” gabanshi ne ya fad’i yace”kamar yaya kin kama haya? haya wace iri”?

Sunkuyar da kai tayi tace”har gida mana”

Cikin mamaki yace” Gimbaya kin kama hayar gida, kikace min maganar babu dad’in ji, ke baki san yanzu sai ki zama abin kwantacce ba, ne, kamar ki budurwa kina zaman kanki,gaskiya ban amunce ba”
ya k’arashe maganar da b’acin rai a fuskarsa.

” Yanzu ya kakeso ayi ne”
tafad’a da damuwa a ranta, domin bata son tona asirin gidansu”

Sassauta murya yayi yace”ki bar maganar kama hayar gida kiyi hakuri ki koma gidanku ki cigaba da zama kamar yau ne komai zai huce”

“Shikkenan, zan bi maganar ka”
tafad’a cikin tausayawa kanta”

” Yawwa nagode Gimbiyata, yafad’a fuskarsa d’auke da murmushi najin dad’i

Wayarsa ce tayi k’ara yana dubawa yaga Sarki! ne, Balaraba ya kalla fuskarsa d’auke da murmushi yace”ga mutumin ki fa”

“Wanene”?
tafad’a cikin rashin sani

” Sarki ne”!

Shan kunu! tayi ta d’auke kanta, murmushi yayi kawai ya girgiza kai tana ji yana masa magana yana amsawa sama-sama, da alama wani abun yake tambayarsa, yana gama wayar ya kalleta yace” muje in kanki gida, yana can yana jirana yanzu”

” A ya mutse tace”gashi ni kuma bangaji da ganin ka ba, sai yaya kenan”?

Agogon hannunsa ya kalla da murmushi a fuskarsa yace”Kiyi hakuri in kin bani dama zan shigo da daddare mu k’ara gaisawa, yanzu muhimin abu ne yasa ya kirani”

Tab’e baki tayi tace” wannam d’an rainin hankalin wallahi na tsane shi”

Cikin mamaki yake kallon ta fuskarsa ta janza da yanayin damuwa yace”har kike rantsewa Gimbiya yanzu d’an uwan nawa kika tsana”?

Tab’e baki tayi tace”ranin wayo ne dashi,wai shi d’an Sarki, nifa gaskiya ko aure mukai da kai bana buk’atarsa a gidanmu”

Shiru Moddibo yayi yana jimanta al’amarin yace”ya kamata ki rage wannan tsanar da kike yi masa domin wata rana zata iya zama so, kamar yadda Annabi Muhammadu (Slw) yafad’a

Comeent Vote and Share
[22/07, 02:06] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????

Bisimillahir-rahamanir-rashim

????56

Shiru tayi masa kawai, yace”muje in kai ki gida ki huta don Allah kar ki sake futowa waje,domin bana son rana tana dokar miki fuskarki mai kyau da kwarjini”
murmushi tayi kawai, yana “yar dariya ya kunna motar suka bar gurin, kafin suka k’arasa gidansu Balaraba kira ya shigo wayarsa, yana dubawa yaga mutuminsa ne, a fili yace” aiki ya had’ani da wanda baya son jira,Gimbiya d’auki wayar nan”yafad’a cike da bada umarni,aiko batare data duba wanene yake kira ba, kawai ta d’aga wayar gami da kara ta a kunne, tayi sallama cikin siririyar muryarta mai dad’in saurare, gabanshi ne ya fad’i jin muryarta, sai yayi d’iff, sallama ta k’ara yi tana duba fuskar wayar a karo na farko domin taga wanene, Magajin Sarki! sunan da tagani kenan, tasan ko waye, tsaki taja ta zata kashe wayar, yace”ke ina me wayar yake,ne ke dashi duk kun zama shashashai, dallah bashi wayar zamuyi magana, kuma ki kuka da kanki gurin yi min tsaki, kinyi min sau biyu kar ki kar ki sake kiyi na uku, wani tsakin ta k’ara ja a karo na biyu, ta mik’awa Moddibo wayar batare da tace komai ba, k’arba yayi da hannu d’aya, d’ayan kuma yana tuk’i dashi ya kara a kunnensa gami da fad’in ” ya a kayi ne, ganinan fa a kan hanya”
“Kar Allah yasa kazo d’in”
Sarki! ya fad’a da rai a b’ace! ya cigaba da cewa “an d’ora min nauyi duk a kanka, tun safe na kiran wayarka dan wulak’anci,kana min hanya-hanya sabuda kana tare da wannan mara kunyar yarinyar da in kayi wasa sai ta lalata ka, kaja mata kunne da kyau duk ranar da ta kuskura ta kuma yimin tsaki, sai nasa an d’aure ta a na tsawon kwana uku, ba budurwar ka ba,ko mecece d’inka bai dame ni ba sai ta d’auki hukunci,tunda kai so ya rufe maka ido kana gani tana abu na rashin kamun kai ka kasa tsawatar mata”
yana gama fad’in haka ya kashe wayar yana wani irin huci! ji yake kamar yaje ya samu yarinyar ya koya mata hankali, ranar da suka fara zuwa gidansu shida Moddibo tayi masa tsaki, jiya tayi masa yau ma tayi masa uku kenan, mutukar ta kara wani to sai ta fuskanci hukunci,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button