GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ta kalle shi tana fad’in “Dama yanzu nake cewa a kira min kai zamu zauna da kai da iyalin ka”

Shiru yayi yana d’an Sosa kai as’usuel.

Gimbiya Halisa ta futo daga wani daki dake cikin falon tw cire alkyabar jikinta yanzu tana cikin wata muguwar shadda wacce akai mata mugun aiki mai bala’in kyau (sirfani) abunka da siririya sai dinki yak’i zama a jikinta sosai, duk cikin kayan lefansu take Balaraba na da irinta Azima ma haka.

Mama ta kalli su Lantana da suka muzanta tace”Yanzu sai Ku shirya a mai daku gida ko”

Lantana kamar ta kurma ihu shikkenan, taga samu taga dashi,inama ace Balaraba ta ce ta zauna mata

Jakadiya Shafa’atu CE ta dawo ta zauna Cikin nutsuwa,, Mama tace”Jakadiya kar ki gaji a had’a musu tsaraba zasu wuce gida”

Jakadiya ta mike tana fadin”An gama Uwar dakina”

Balaraba ta mike a nutse ta nufi dakin da take, duk wani Abu da tasan nata ne naci da na sawa ta had’a su guri guda ta futi dasu da k’yar,, zama tayi kujerar da ta tashi tace”Gashinan Ku raba Wannan nawa ne babu yawa,, Ku gaishe min da Iya matar Kawu”

Lantana godiya kawai take yau ta k’ara tabbatar da cewa Ubangiji mak’agin baiwa ne me yin yadda yake so da kowa wai tana raye a duniya Balaraba tayi aure kuma ta dauri Sarki! Lallai idan kace tukunyar wani baza ta tafasa ba to taka ma ko dumi baza tayi ba, tabbas taga ishara ta gane duniya ba komai bace, yanzu dole ta kwantar da kai suci su sha ta dalilin Balaraba..




Shamsiyya tsugene a bakin kofar zauren Arrama ta buga-buga an ki budewa, wata zuciyar tace watak’ila yana ciki yana aiki shine ta tsuguna tana jiran ya gama,, wasa take da wani kara a hannunta taji zuciyarta tana wani irin tashi, da sauri ta mike taje bakin kwata ta dunga yunk’urin amai,, aikuwa kafin kice me sai ga wani amai Kore fatau tana kyalashi,, mutane suka fara taruwa a kanta suna tausayin ta,,wata mata tazo ta kamata ta mikar da ita suka samu dakali suka zauna, da k’yar ta dawo hayyacin ta sai haki take, matar tace”Yarinya daga ina kike haka ai gwara ki koma gida ki je ki huta”

Shamsiyya ta ya mutse fuskarta har yanzu tana jin tashin zuciya tace”Nazo gurin Arrama ne, tun d’azu nake bugu bai bude ba nace ko aiki yake ne”

Matar ta girgiza kai cikin takaici wato ire-ire “yan Matan da suke zuwa gurin Arrama ne, wannan wai duniya INA zaki damu bin malamai babu yara babu manya babu zawawara babu Matan aure da ” yan mata, tace”Ai sai da kiyi hakuri jiya-jiyanan aka kama shi yanzu yana hannun hukuma saboda jiya wata buduwar yarinya tazo Ita da uwarta gurin nan cika yayi da d’an Adam tazo tana kuka yayi mata ciki wata uku shine sukaje suka d’auko “yan sanda a ka kamashi, to d’azu da safe labari ya same mu cewar ya kufce daga hannun ” yan sandar ya gudu”

Shamsiyya ta d’ora hannu aka tana fad’in”Na shiga uku na lalace, Arrama me yasa zakayi min haka,, kace Saura kad’an aikina ya kammala shine zaka gudu baka k’arasa mun ba”
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????105

Yara suka fara taruwa a kanta sai kurma ihu! Take, da sauri wannan matar ta d’ora ta a hanyar gida tana tafe tana kuka kamar shashasha sai surutai take.


Mota a ka kawo su har k’ofar gida cike da kayan arziki, yaran unguwa suka yi dafifi suna shafa motar suna tsalle har yanzu sun kasa sabawa.

Yara matasa suka kwashe kayan da suka zo dashi suna shiga gadan dasu,, suka bi bayan su duk jikinsu a sanyaye,, Buba direba yaja motar sa ya tafiyar sa,, suna k’okarin shiga gidan ana k’okarin futo da Sallau a rirrike jikinsa yayi tsanani, Lantana ta rafka salati gami da fashewa da kuka tana fad’in “Ina zaku kai shi”?

Walidi Yace” Asibiti za a kaishi domin jikinsa yayi tsanani, nan ta bisu a baya tana kuka, Uwa! Kuwa gida ta shige tana matsar hawaye, Sadiya da Iya na tsaye tsakar gida cike da tausayin Sallau Uwa ta shigo gidan, kallo suka bita dashi ganin tana matsar hawaye domin sun d’auka ko ganin jikin Sallau ya rikice yasa ta kuka, zauna tayi a tsakar gidan tana kukan nadama.

Ko minti goma ba’ayi ba sai ga Shamsiyya ta shigo gidan tana kurma ihu, ta zube gaban mahaifiyar ta tana fad’in”Shikkenan Uwa! Aiki ya lalace “yan sanda sun kama Arrama jiya da yamma”

“Don Allah ni yi min shiru da zancan wani Arrama in zaki hak’ura ki hak’ura ki zauna inda Allah ya aje ki, ni kam. na dawo daga rakiyar wannan duniyar me cike da rud’u”
Uwa! Ta fada tana sharb’e hawaye

Shamsiyya ta d’ago kai tana kallonta cikin mamaki tace”Ban gane abunda kike nifi ba kina nufin in rabu da maganar aure na da Sarki! Ko me”?

“E abunda nake nufi kenan, Domin babu yadda za’ayi ya aure ki yana da Balaraba”

Shamsiyya ta fashe da kuka tana fad’in “Uwa kar muyi haka dake kinji, kece fa kika yi mana alk’wari cewa ko da zakiyi yawo tsirara sai in da k’arfin ki ya k’are zaki tsaya min gurin ganin buk’ata ta ta biya”

“Ke ni ki k’yaleni don Allah inji da masifar da nake ciki, ubanki ya sake ni saki uku, ga masifar Ku ta same ni, Nazo a banza zan koma a wofi ni yanzu waye zai aure ni” ta k’arashe maganar tana rusa ihu!

Shamsiyya ta dafa kirji tana fad’in “Baban bamu ne ya sake ni yau she haka ta faru”?

Nan Uwa ta kwashe duk abunda ya faru ta fada mata har da zuwan su gidan Sarki! Shamsiyya ta kwanta tana rusa ihu! Babu kamar wacce uwarta ta mutu


Suna zaune gaban Mama Fulani duk su ukun sai shi da ya zama cikon na hud’un,, yana hakimce kan kujera.
Mama tace “Salati goma da Annabi” Duk suka amsa da “Sallalahu alaihi wasalam”Minti goma tsakani tayi addu’a ta shafa suka shafa suma,, ta kalli Sarki a nutse tace” Babban abunda yasa na tara ku anan shine, in ja muku kunne gami da nasiha, mussaman kai” tafad’a tana nuna shi da hannu, kansa ya sunkuyar kasa, ta cigaba da cewa”Allah ya d’ora maka wani babban nauyi a kanka na mataye har uku, dukaninsu suna da hakki a kanka babu wacce tafi kowa a gurin ka sai wacce tafi kyautata maka a cikinsu, don haka ina mai gargadin ka da ka rike amanar su ka bawa ko wacce hakkin su,da ya rataya a kan ka”
Yace”Insha Allah Mamana kar ki damu”

“Ku kuma na dawo kanku”
Tafad’a tana kallonsu duk su ukun, ta cigaba da cewa”Ku yi kokari Ku kula da mijin Ku Ku fahimci me yake so da Wanda ba ya so, yi nayi bari na bari Ku yi k’okarin zama lafiya da juna domin Ku kwantar masa da hankali gurin ganin ya rik’e amanar Ku, da jagorancin mutanan gari da ya hau kansa, ni Wannan kawai zakuyi min Ku faranta min, insha Allahu , kuma idan wani sab’ani ya shiga tsakanin ku dashi, ba fata nake ba,, zama ya gaji haka zo mu zauna zo mu sab’a haka duniyar take, to sai Ku same ni Ku sanar dani insha Allahu komai zai zo da sauk’i”

“Mama Insha Allahu zaki same mu masu zaman lafiya da juna” Balaraba tafad’a kanta a kasa,, Azima da Halisa ma Abunda suka ce kenan, Mama tace”Masha Allahu Allah yayi muku albarka” Ameen suka ce gaba d’ayan su.


K’arfe shida na yamma, gurin Walima ya d’auki harami ya tsaru ya k’yayatu sosai Shahid da Shatima ne suke ta kai kawo a gurin suna saukar abokan su, da suka fara zuwa.
Suna sanye da wata arniyar gezna wacce ta amsa sunanta anyi musu dinki iri daya hula da takalmi duk kalar shaddar ne,, ruwan toka kenan sai shek’i take aikin ya. zauna a jikinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button