GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daga wannan pege din sai na k’arshe Ku zauna cikin shiri❤❤❤❤
????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA

ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.

DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????????????????????????????????

????115

Da k’yar ya samu ya kufce daga hannun Halisa ya gudu part d’insa inda su Shahid suke zaman jiransa,nan kama kafin ya tafi sai ya gargade su kar wacce ta bishi, saboda hutawa zaiyi Balaraba cikin zuciyarta tace.” Dama ni ko ka neme ni ba zuwa zanyi ba, zama zanyi inyi jinyar zuciyata da zatayi kwana hudu ba tare da Kai ba.

Nan gurin Mama suka zauna dukaninsu, kallon Balaraba sukeyi a fakaice ganin yanda tayi Wani mugun kyau, tayar ta kamar ka tab’a jini ya futo ta kara cika da kwarjini, wani kyashi da bakin ciki ya damu zuciyarsu babu abunda ya kara daga musu hankali sai yanda Mama take kula da ita, tana kaf-kaf da ita da tayi motsi zatace “Ya akayi in dai akwai abunda kike sha’awar ci kiyi magana akawo miki.” Girgikai kai kurum take cike da kunyar Maman, Halisa ta kalli Mama da jiki a sanyaye tace.” Bata da lafiya ne.”? Murmushi tayi tace.” Cutar ta arziki ce ai insha Allahu kun kusa samun baby.” Ita da Azima ban San wanda yafi wani shiga rud’u da tashin hankali ba, neman miyau tayi ta rasa abakin ta, idonta ya ciko da ruwan hawaye, Balaraba na da ciki,cikin kuma na masoyinta Wanda taci burin ita zata fara Haifa masa ‘yaya, to wai abun tambaya anan, shine mutumin da ya tafi Neman lafiya ta yaya har ya iya kwanciyar aure babban abun tambaya yaya akai shi da bashi da kafa ya sarrafa kansa.

Dariya nayi nace lallai Halisa kin cika hamaguwa????

To tunani da take shi Azima take duk sun shiga tashin hankali Lallai BALARABA tayi musu fintinkau tayi musu zarra,yanzu meye abunyi? Halisa take tambayar zuciyar ta, wani b’angare na zuciyar tata Yace mata,kawai yau kema ki matsa masa yayi miki ciki ki haihu, aikuwa ta yarda da wannan shawarar ta zuciyar tata.


Walidi ne ya siyowa Shamsiyya atamfa guda biyu dinkakkau ya siyo rago ranar suna yaro yaci sunan mahaifin su,wato Sallau, Salihu kenan, a ranar ne kuma labarin Mabaruka ya same su, ta hanyar k’afafun yada labarai, an nuno ta kwance gadon asibiti babu k’afafu, ana cigiyar danginta harda Lamar waya aka kawo wa Walidi aikuwa atake ya kira wayar yayi musu kwantan inda suke, ba tare da bata lokaci ba aka sako Mabaruka a mota tare da keken guragunta tana kuka tana da tasani abunda tayi, Ranar kwana sukai kuka Iya da Sadiya matar Maman suna ta tausar zuciyar su.


Ana kiran idar da sallahr Isha’i Halisa ta dura a part din Sarki! Cikin shirin ko ta kwana, tayi kwalliya iya kwalliya, sama ta hau domin baya farlo,shima tunda su Shahid suka tafi ya hau sama domin ya huta, bude kofar tayi ta shiga bakinta d’auke da sallama ya amsa babu yabo babu fallasa, zama tayi kusa dashi, tana sak’e-sak’en maganar da zata yi masa, yace.” Halisa mun same Ku lafiya ko.”? Cikin dauriya tace.” Lafiya lau Yallab’ai.” Shiru yana sauraron ta yasan da akwai magana a bakinta, yace.” Wane tanadi kikayi min.”? Yake tayi kawai tace.” Ni wane tanadi zanyi maka,nice ma Nazo kayi min tanada kamar yanda kayiwa Balaraba.” Bai gane hausarta ba yace.” Wane tanadi nayi Mata.” Inda-inda ta fara yace.” Ke nake saurare.” Tace.’Nima ciki nake so kamun.’ Cikin mamaki yake kallonta. Yace.” Ciki Allah ne ke ba dashi ba mutum ba, sai kice ni in zama silar shi.” Kuka ya fara yi sosai harda sharb’ar majina.” Yace.” Meye abun kuka, kuma.” Tace.” Ina jin takaicin yadda wata zata fara haihuwa dakai bani ba.” Tsaki yaja yana girgiza kai yace.” Matsalata dake rashin wayo da dubara ni dake da balaraba babu Wanda ya Isa ya hana Allah ikonsa akanmu Balaraba zata fara haihuwa dani haka Allah ya tsara.” Kuka sosai takeyi takasa cewa komai ta kwanta kan bed din tana Jan ajiyar zuciya, tausayinta ne ya kamashi,ya kashe futal dakin tare da aje k’aramin littafin hannunsa ya rungume ta yana fada mata daddadan kalamai, nan labari ya sha BABBAN, na futo na barsu ina fatan samun nasara da ‘yaya masu albarka.

To sarki! Ya biya Halisa domin dai jiya ya kashe ta da soyayyar sa mai wahalar mantawa lokaci kad’an ta manta da damuwar ta,ta cigaba da kyautatata masa.


Tsito ne ya dura a gidan kamar tsohon mahaukaci ya nufi b’angaran Hajiya Kulu me dakin kudu, yazo domin ya karb’i sauran kud’in aikin sa. Nan ya samu babu. Kowa a shashen nata sai hadiman ta, suka ce masa satin ta biyu bata gida,hakanan yaranta suma ba kullum suke kwana a gida ba, haka ya futo yana tunanin ina zashi,domin yanzu duk aljanun da suke kanshi sun dare sun gudu baya iya yin aikin komai watarana ma da yunwa yake kwana, ya tabbatar da cewa abunda suka aikata da Waziri ne ta shafe shi, zuciyarsa ta bashi shawarar kawai yaje ya nemi afuwar iyalin Waziri ko Allah zai sa ya gama da duniya lafiya, sannan suyi masa iso gurin Sarki! Almansur domin ya nemi gafarar sa Halin da yaga Waziri a ciki ya bashi tsoro bakinsa ya dinga rawa ya rasa abun cewa,Hajiya Kattime tace.” Bawan Allah daga ina haka domin banga ne ka ba.”?

Tsito ya fashe da kuka yana fad’in.” Yanzu haka Waziri ya koma oo ni Tsito.” Kattime tace.” Kayi min bayani mana, yace.” Nine Tsito wanda nayi ma mijin ki aiki duk Dan yayi mulki nan ya warware mata duk abunda ya faru, yaran ta suka taso domin suyi masa duka ta hanasu, tace.” Ku kyale shi shima zai ga karshen sa, nan Tsito yayi dasu su masa iso gurin me Martaba Kattime ta hana, haka suka tarkatashi suka futa dashi fadawa suka tasa keyarsa har waje, yana futa ya kasa gane hanya kawai sai ya dauki wata haya ta daban yana tafiya yana tsayawa bola-bola yana tsince-tsince duk ledar da ya gani sai ya d’auka ya sa a bakinsa yana taunawa.

Ubangiji Allah kasa muyi kyakyawan k’arshe


Kwana biyu da Halisa tayi ta samu kulawa sosai a gurinsa ganin yanda ta kwantar masa da kai tana kula dashi komai sai tace idan BALARABA ta haihu za’ayi kaza da kaza, hakan ne yasa ya Sakar mata jiki suka sha soyayya.

Azima ya ta karb’i girki sai girin gidishi take tasha magunguna mata kamar banza mararta sai kullewa take jira kawai take dare yayi ta shiga part din Yallab’ai a kashe boss.


Hajiya Kattime ce tayi sallama ta shiga a nutsue Mama ta amsa Jakadiya ta gyara mata gurin zama,sannan ta futa ta basu guri, Kattime ta gyara zama tana fadin .” Fulani magana nake tafe da ita.” Mama tace.” Ai tunda naga fuskar ki nasan akwai magana.”

Kattime tace.” Wallahi kuwa, jiya na samu wani labari da bakin da ya fada min bazai k’arya kai asalima shine ya asassa al’amarin.” Mama ta zuba mata ido, Kattime ta cigaba da cewa.” Kin san Azima da ita aka had’a baki gurin cutar da Almansur.” Mama ta mike zaune sosai tana kallon ta cikin mamaki! Kattime ta cigaba da cewa.’ Jiya Tsito mashirikin da yayi aikin yazo ya warware min komai, saboda haka Nazo na fada miki auran Azima da Almansur dama da wata manufa aka had’a shi don haka ki umarce shi da ya rabu da ita tun wuri.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button