GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

To Masha yanzu zamu saurari jawabin sarki mai Adalchi kafin jawabin Manyan baki da malamai da iyayen yara”

Cikin kamala da dattako mai martaba ya mike tsaye ,wani bafade ya karoso gurin hannunshi riqe da wata zungureriyar lasika ya sai ta ta daidai bakin sa ,

Sarki ya bude taro da Addu’a cikin Lafazin sa mai kyau da lumana yayiwa dalibai nasiha da iyayen su sabida jajircewarsu gurin ganin “yayansu sun samu ilimi in gan tacce.

Kana ya kuma ya zauna ,gurin zamanshi cikin nutsuwa da qasaita irin ta sarautar da ta Amsa sunanta,

Da dai dai da dai dai malamai da masu jawabi gami da iyayen yara kowa yayi nasa jawabin sannan mai gabatarwa yayi gyaran Murya yace “yanzu zamu kira daya daga cikin dalibanmu masu hazaqa zata yi mana karatu kafin mai martaba ya mikewa ko wanne Allonshi muna wa kowa fatan Alkairi gami da ko mawa gida lafiya”

Muna bukatar
BALARABA AYUBA TANKO
Tafito nan ,mai gabatarwa yafada cikin lasifiqar,

Hankalin kowa ya koma kan taron Matan dake zaune can cikin wata katuwar Runfa a ke 6ance a gurin,

Shiru Balaraba tayi gabanta yana faduwa domin Sam bata taba tsammanin ita ce zatayi karatu ba,

Gaskiya duk rashin kunyarta tana jin nauyin ratsa dubban mazan dake zaune a gurin ,gani take ma baza ta iya karatun ba domin ita kam ta tsani kallo wallahi,

Bushira ce take zungurinta ,tana jinta tayi mata banza,

Mai gabatarwa yakara maimaita Balaraba Ayuba tanko ta fito ,mana”

Shiru taqi fitowa,

Dago kansa yayi cikin ginshira yana bin ilahirin jama’ar dake gurin da kallo cikin izza ,ya dinga karade tarin “yan matan da Kallo so yake yaga ta inda wannan yarinyar zata fito ,wacce tun dazu a ke shalar tafito tayi kunnen Uwar shegu da jama’a,

Wai ina BALARABA AYUBA TANKO TAKE NE?

mai gabatarwa yaqara mai maitawa A Dan Fusace,

Ko gama rufe bakin sa bai yi ba ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din ta sosai ,kana ta gyara zaman glass din dake fuskarta ,tafara ratsa Jama’a domin zuwa gurin da ‘a tanadar domin ita din

Tun da tafito cikin jama’a sosai hankalin mutane ya koma kanta, banda Almansor ,domin kallo da yayi mata ya kauda kai yana Jan tsaki,

Taje ta tsaya gami da gyara lasifiqar sosai ,tayi gyaran murya cikin Nutsuwa ,tafara kwararo karatun Al’kurani mai girma tamkar wata balarabiyar kasar Saudiya yadda take fitar da harafi dallah dallah take bawa kowa nashi hakkin ga wata murya mai dadin sauraro gami da kashe jiki

BINTA UMAR ABBALE????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA

YARO DA KUDI

GIMBIYA BALARABA

????????????????

✍????,,,,,,,,
[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYABALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????WRITTEN BY
Binta Umar
~MAMAN ABDUL WAHABU~

~MRS AHAMAD GWADABE~????

WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR
08089965176

????3

Shiru gurin ya dauka jikin duk Wanda yake gurin ya Mace sakamakon karatun Al’kur’ani mai girma da yake ratsa gurin.

Sai da ta karanta Ayoyi goma na farkon Suratul bakara ,kana tarufe da Addua’a cikin Nutsuwa a je lasifiqar Hannuta ,a ma’ajiyarta tafara kokarin barin gurin

Ida nun mutane sukai caaaa! A kanta Sai tafiyarta tafara hardewa tamkar zata fadi.

Cikin isa Ya dago kanshi dalilin Da yasa Abokinshi Shahid ya takura masa da Magana kasa kasa wai lallai sai ya kalli ita wannan mai karatun

Yana ya mutse Fuska gami da Limshe ido yabi bayanta da kallo domin baiyi nasarar ganin Fuskarta ba ,Wata irin ingarmar Mace ya hango game tsawo ga qiba dai dai Misali ga wani Uban Sharp Wanda sai da yafito ta cikin hijab din a nagani ,Sakamakon yadda Allah ya wadata ta dasu ,kafarta ya kalla cikin bakin takalmi Fara Tass tass da’ita ,Da’a lama jikin ma haka take

Ajiyar zuciya ya sauke yayi saurin dauke idonsa daga kanta,jin zuciyarsa tana darsa masa wani Abu,A rayuwarshi yana son farar Mace kasan cewarshi Mai dun fata .Sai tarin kyau Wanda Allah yayi masa

Shiyasa yake son Farar Mace inji hausawa Alkyabbar Mata,

Shahid ya zungure shi kadan yace”yaya ka ganta Yarinyar tayi fa wallahi irin kallar ka gata zata dace da Sarauta dubi zubin tsarin jikinta dagani A kwai qasaita”

Gyaran Murya yayi kadan “yace “yar wane sarki ce ? Waye Babanta a garin nan ? Da kake hada ni da’ita haka kawai daganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaqi!
Yafada Cikin izgili gami da qasaita Wanda hakan yazame masa jiki,

Shiru Shahid yayi sabida yasan halin Abokinshi Dan daukar zafi ne yace”yanzu dai mubar maganar sai muntashi daga nan”

Ta6e baki Sarki! Yayi dake haka yanwancin suke kiransa dashi Sabida isa da takamar da yake da’ita wacce shi kanshi sarki Almustapa baya yi a Matsayinshi na sarkin ,shi da kanshi yake kiran Almansor din da Sarki zamu’iya cewa shine ma yasa masa sunan Sabida yadda yakeyi din tun yana yaro. To shine fa Abokanshi suke kiranshi da sunanan ,cikin gida kuwa da yarima suke kiranshi.

Mai gabatarwa yakara fitowa a karo na biyu ,bayan Maryam taje ta zauna Cikin nutsuwa yace’Alhmdullhi mun saurari karatu daga bakin Dalibar mu Maryam Ayuba tanko dalibar datayi fice tayi zarra cikin Makaranta sabida hazaqarta da tsaftarta biyyarta Nutsuwarta Tabbas Muna Alfahari da ita Kuma munai mata fatan Alkairi gami da samun miji nagari.

Yanzu batare da bata Lokaci ba Mai martaba sarki Mai adalci Uban talakawa Mai tausayin Al’umma ,zai fito ya rarrabawa ko wanne Alonshi gami da sauran kyautittikan da muka tanada ga dalibanmu da Suka Sauke Al’kurani mai girma kimanin Mutum Dari Uku da sha bakwai Muna fatan wata shekarar dalibai na kasa zasu bada himma da jajijrcewa Musamu ninkin waddanda muka yaye Allah yakarawa Mai Martaba Lafiya da Imani,yafada gami da aje lasifiqar ya bar gurin a nutse .

Gurin yayi tsitt! Mai Martaba yayi gyaran Murya Cikin Abin Maganar ,Wanda yana zaune gurin zamanshi wani bafade yake riqe dashi,

Ya dauki Allon Farko

Sunan BALARABA AYUBA TANKO yagani jiki yace’Alhmdullhi.

Balaraba Ayuba tanko

Wannan karon ba tayi nawar fitowa ba ta mike tafara ratsa jama’a a karo na biyu Cikin qasaitarta da yanayin tafiyarta ta durfafin inda Mai martaba yake zaune

Idon Mutane yayi caaaa! A kanta kamar dazu ,tsaki taja a ranta tace wallahi na tsani kallo ko kadan”

Ta kasan idonshi yake kare mata kallo har tazo ta durqusa kusa da Mai martaba gami da gaidashi Cikin Nutsuwa,

Yayi saurin dauke idonshi daga kanta ganin ta dago kai ba yaso taga yana kallonta duk da cewar ta kasan idonshi ne idan ba mai kurrala ba ma babu Wanda zai fahimci ita yake kallo ciki ko harda ita balaraba n.

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????
✍????,,,,,,,,,
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????Writting by
~Binta Umar~

~MAMAN ABDUL WAHABU~

~MRS AHAMAD GWADABE~

WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR
08089965176

????4

Mai martaba ya Maka mata Alo gami da kyautitikan ta na musamman ,Masu photo da video sai aikinsu suke a gurin.

Sannan ta mike hannuta riqe da Allon Fuskarta cike da Walwala,Mai martaba ya kara lasifiqa a bakinshi yace” Ma haifin wannan Yarinya mai Albarka yafito a kwai kyauta ta musamman da na tanadar domin ku iyayen yara”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button