GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lantana na hango Balaraba ta mike da sauri zaninta ya fad’i ta d’auka da sauri ta d’aura taje ta rungume Balaraba ta fashe da kuka tana fad’in “Ashe kina nan Balaraba, munyi neman duniya bamu ganki ba,Shima Sallau da k’yar ya koma gida ranar ashe alkairi ne a tartare dake Balaraba”
Wasu irin sambatu Lanatana ta dunga yi Mamaki ya kama Balaraba sai ta rik’e ta ta zaunar da ita tana fad’in ki zauna mana, don Allah ki nutsu sosai sai muyi maganar.

Ita dai Mama tana kallonsu cike da mamaki

Jiki narawa ta zauna tana hawo hannun Usuman yana fuzgewa yana komawa bayan Balaraba,

Tace”Zo nan Sadiya mu gaisa” k’in zuwa tayi yarinyar.

Fashewa da kuka Lantana tayi cike da munafurci da kitifi tace”kinga abunda nake fad’a miki ko Balaraba, dubi wai jina ne yake guduna duniya kenan”

Balaraba na jinta tasan dai makircin Lantana,, tace”Ki nutsu nu gaisa mana”

Jikinta na rawa ta hau gaida Balaraba, amsawa tayi kawai tana kunshe dariyarta ita Abunda Lantana take ya soma bata mamaki wallahi.

Mama kanta ta fuskanci rashin gaskiya gurin Lantana.

Da k”yar ta hillace ta suka nufi gurin cin abunci Lantana taka tunga ta tsayawa wai baza ta hau kan daining ba, haka ta had’a mata ta kai ta aje mata can wani k’ebabtaccan gurin Cin abunci take kamar wata jaka babu kamun Kai babu komai, Mama Fulani na daga gurin zaman ta tana kallon ikon Allah, Balaraba kuwa wata irin kunya ce ta kamata, a hankali tace “Lantana kici a nutse mana”

Ko saurarenta batayi ba,sai da ts cika Uwar hanjinta da kyau sannan ta tsame hannuta tana goge bakinta,,, Mik’ewa tayi ta koma falo kusa da Mama Fulani,,Tsaki Balaraba taja tana d’auke kanta,tanajin Lantana tana cewa Mama wai tana so ko bayan biki ta zata zauna anan”

Mama Fulani tace”Ai babu komai sai ta zauna d’in.

Mama Fulani dai shiru tayi musu ita da Jakadiya suke hira itama da tagaji sai tao shiru ta k’yaleta,, sai banbadanci takewa Fulani.

Mintu ashiri Mama ta kara a gurin ta mike tsaye tana musu sallama domin zataje ta kwanta, nan sukai mata sai da safe, ta shige d’akinta, Jakadiya ma sallama tayiwa Lantana ta mike ta nufi dakin kwananta.

Balaraba ta kalli Lantana da rai a b’ace tace” Ai sai ki tashi haka muje ki kwanta, wai don Allah meyasa kike haka ne”?

Lantana ta hau yak’e tana fad’in “Me na aikata ” yar nan, baki San su irin wannan mutane dole sai kana musu banbad’anci ba”

Tsaki taja tana fad’in “To banda wannan masarautar ta masu hankali ce,don Allah ki dunga nutsuwa kar ki bani kunya gurin abokan zamana da mutanan gida”

Lantana tace”To naji zan kiyaye ai kina da damar da zaki fad’a min duk irin maganar da kike so, saboda Kinga zaki auri Sarki!

“Shiru kawai tayi mata tana surutai a cikin zuciyarta take fad’in ko wannan auren ya dama,ni a gurina sunan shi auran biyayya.




Komai yayi farko yana da k’arshe

Cikin shiri sosai suka futo daga shashinsa gida ya cika ya tumbatsa baka jin komai sai busa da sarewa irin ta gidan sarauta, marok’a da magogo sai aikinsu suke, k’amshi suke ko ta ina Sarki yana cikin wata d’anyar Shadda gezner me mugun tsada anyi masa wani irin dinki babbar Riga da ” yar ciki ita kanta hular dake kansa da da yankin shaddar aka had’a ta kafarshi sanye da wani takalmi rufaffe mai mugun kyau kalar kayan jikinsa sky blue yayi masifar kyau fysakarsa sai futar da annuri take, sajensa ya kwanta lif-lif a fuskarsa hannusa wani irin agogo ne, na zallahr azurfa, kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki da annushuwa, sai gaisawa yake da manyan mutane gwamnoni da “yan majslisa sanatoci da sauransu, ” yan abokan arziki duk murna sukeyi da farin ciki.

Wata kujera ya nufa wacce a ka k’wata ta da shimfud’u na alfarma yana tafe su Shatima na take masa baya, zama yayi cike da k’asaita, wasu nayi dake tsaye suna jiran zuwansa suka hau yimasa firfita, Shahid da Shatima suka zauna gefe da gefan sa.

K’irari kawai kakeji da busa marok’a sun rud’e kowa da irin nashi rok’on kowa naso ace nashi yafi na d’an uwanshi.

“Masha Sarki! Ya futo fasa taro Jimana na gaban Giwa, baka iya ba Allah ne zai yi maka, yaro me Halin dattako! Fari mai farar anya! Hak’ika matayen ka sun dace da samun nagartaccan miji jarumin jarumai,, Duk zaka iya dasu har da k’warl’wara ma, Sarki! Almasur kujerar mulki takace Allah ya yataka ruk’o jamuje Gami sha sassaka duk wani mak’iyinka sai da ya mutu!!!!!!

faaaa!! Gurin d’aurin aure ya kai ya kawo jama’a d’aurin auran mataye uku ba wasa ba ne, Waziri Zayyanu na gefe guda shi da tawagar shi duk ransa a b’ace yake shi ba abun ya koma gida, wata zuciyar tana ce masa ya zauna kawai a k’arasa dashi, dole shine Waliyyin Ango kuma yayi rantsuwar bazai masa waliyi ba, Yana kallon Shige da fucen da Galadima yake shida Wambai, sam sunk’i su zauna kusa dashi,sun karkata gurin Sarki,yasan duk kalar munafurci ne, kujerar mulki sukewa yaga kuma yadda za’ayi a karb’eta a hannusa.
Gaisawa kawai yake da jama’a ba dan ransa ya so ba, mutane sai zind’ansa suke suna nuna shi a matsayinsa na Sarki me rik’on k’warya.

Sai da aka fara d’aura auranshi da Halisa kan sadaki dubu d’ari sannan aka d’aura da Azima itama sadaki dubu d’ari, sai Balaraba itama haka, Liman ne ya karb’i wakilcin Balaraba,saboda babu wakili Sallau ne kuma bai zo ba saboda tsabar bak’in ciki,shi kuma Maman baya gari yana can tafiya tafiyensa dake babbar motar d’aukar kaya yake ja,,, Kowa ce aka damk’awa Wakilinta sadakin ta, Liman ya rik’e na Balaraba a hannusa yace shi zai bata da hannusa.

Bayan d’aurin. Aure guri ya hargitse da ciye-ciye na abunci nau’i nau’i ana futo dashi daga gida,, Masha Allah kowa yaci kuma yayi guziri guri bai watse ba sai dab da sallahr azahur sannan kowa ya nufi gida domin yin sallah.

Mahaifin Azima ne suke keb’e da Waziri suna maganganu k’asa-k’asa karku manta da cewar dama tuntuni abokai ne

Tun daga nesa Sarki! Ya Fahimci akwai maganganu da suke tattaunawa. Kuma da alama basu da gaskiya, suna ganin sun k’araso gurin Mahaifin Azima ya saki fuskarsa sosai yana fad’in “Dama ina cewa azo a nemo min kai muyi sallama yau zamu koma ni da tawaga ta, inai maka fatan alkairi da d’or ewar zaman lafiya kai da iyalinka, ga Azima nan nabaka amana,yanzu ma abunda nake kara jaddadawa abokina kenan gashi nan a tsaye”

Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya mik’a masa hannu yana fad’in “Insha Allah karkadamu mungode sosai A sauka lafiya”

Cire hannusa yayi ya mik’awa Waziri Zayyanu, kauda kai yayi ba tare da ya bashi hannusa ba, yace”Ka rik’e gaisuwarka ni bana buk’atarta, na fad’a maka tun wuri tsalle d’aya mutum yake ya fad’a rijiya, amma sai yayi dubu bai futo ba”

Yana gama maganarsa ya wuce ya barsu tsaye a gurin,

Sarki!
Shahid
Shatima

Duk suka bishi da kallon mamaki.
????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????94

Sanin Hali yafi sanin kama,Sarki fuska yayi kawai ya wuce ba tare da ya tsaya ya k’ara sauraron wata magana daga bakin Mahaifin Azima ba wato me Martaba sarkin Yalwa, ganin ya wuce ne yasa su Shahid suma suka rufa masa baya suna cike da mamakin abunda Waziri Zayyanu ya aikata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button