GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lantana ta rage Karfin Redion ta ,tana mata wani kallo gami da ya mutse fuska

“Lantana kiji tsoran Allah kiji tsoran ranar kumawarki ga Allah ,Lantana meye duniya,kishiyarki Na naquda kika bari har ta gala baita batare da kin je kin sanar ba duk Wanda yayi nagari kanshi”

Lantana ta harziqa!! Tace”kinga shattu banason kinibibi kunsan Yarinyar baza ta iya haihuwa da kanta ba kuka kulla mata Aure duk domin ku bata min rai!, to Ta Allah ba taku ba,Sai kije ki nemi Wanda yayi mata cikin yazo ya karbi haihuwar Amman ni karki kuma saka ni a lamarin Ehee!!!!

Sallau dake gefe yana cin wake da shinkafa cikin Langa,ya fashe da dariya,jin Abinda Uwartasa tace wai aje a nemi Wanda yayi mata cikin yace “in banda Abin baba Mu kadai mun isheshi “yayan Asali ba sai yaje ya hada jininshi da bara gurbi ba”

Lantana tace”ai Abinda Akeso ya gane kenan yaqi yagane sabida muna fukai sun zigashi”

Sallamar Atika ce ta sa Gwaggo shattu bata tanka musu ba sai tasaki labulen dakin da sauri ta karbi rubutun hannun Atika,suna rige-rigen shiga dakin Suwaiba

Abin Mamaki jinjiri ne kwance cikin jini yana motsi Igiyar cibiya ta sarqe masa wuya,ga shi mahaifar bata fado ba

Da sauri Shattu taje ta dauke shi gami da since masa zaran cibiyar ta sanya reza ta yanke gami da daurewa,tana tai wai Allah tasbihi,ta mika wa Atika yaron ,taje tadago Suwaiba tana kokarin bata rubutun domin asamu mabiya ta fado sai taga Suwaibah ta koma Sharaf! Ta kwanta ,Rai yayi Halinshi!!

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????
08089965176
[04/05, 03:13] +234 808 996 5176: ????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????Writting by
Binta Umar
Maman Abdul Wahabu

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????

????17

Bissimillahi

inalillahi Wa inna ilaiyi rajiun!

Shine Abinda Gwaggo Shatu take Fada, Jikin sai rawa yake yi ta kalli ,Atika dake tsaye a gurin gabanta yana Faduwa! Tace “Suwaibah ta rigamu gidan gaskiy…
Kafin ta karasa Malam Tanko ya daga Labulen Dakin cikin tashin hankali,
Ya ga Suwaiba Kwance a kasa lullube da Zani ,da Sauri ya dauke Zani yana kiran Sunanta,Gwaggo Shatu ta fashe da Kuka! Tace”Malam Suwaiba Babu Allah ya raba ganawa”

Innalillahi Wa’ina ilaihi rajiun

Malam Tanko ya fada Bakinshi sai rawa yake yi Da Sauri ya Fita daga dakin ya tsaya kofar Dakin Lantana,Daga Waje yace”Lantana ki fito ,Suwaibah Allah ya karbi Abinshi, Burinki ya cika”
Yana gama Maganar Yayi waje Cikin Zafin Nama,Bakinshi dauke da Addu’oi Ga Suwaiba Matar Arziqi

Da Sauri Lantana ta bankada Labule,ta fito kamar gaske ta tsaya tsakar gidan Tafashe da ihu! “Wayyo Mun shiga Uku! Ihu! Take Sosai Sai kace Mahaukaciya ,Cikin Ziciyarta Sai murna take

Nan Makota suka dinga Shigowa Cikin tashin Hankali ,Masu kuka nayi masu salati nayi ,kar dai Lantana taji Labari

Malam Suka shi go dashi da Liman da Sauran dattawan Unguwa,

A ka sutturce Suwaiba a ka kai ta gidanta Na gaskiya, Sosai mutuwar ta ta ba zuqatan Mutane banda Lantana da yaran ta

Bakin ciki Kamar yakashe Lantana Lokacin da ta Fahimci Da Namiji Suwaibah ta haifa,suka riqa tsara yadda zasu kashe jinjirin ita dasu Sallau,Fahimtar Hakan yasa Malam Tanko ,daukar jinjirin Bayan kwana ba kwai ya Miqashi ga Gwaggo Shattu ,yace ya bata Amana

Gwaggo tace ta karba Allah ya tayata riqo ,A lokanci A kwai qan warta da take Shayarwa sai ta bata,Jaririn Wanda yaci Sunan Ayuba,da zumar in ta yayashi Sai ya dawo Hannuta,

Lantana taji ciwon Abinda Malam Tanko yayi ,nan ta Sanyashi a gaba ta rika cin mutumcinsa bai ce Mata komai ba

To A taikaice dai rikon Ayuba ya dawo Hannu Gwaggo Shatu yana da Shekara Uku ,Sharasa Bakwai a duniya Allah ya dauki Ran Malam Tanko Sakamakon Rashin Lafiya tafarar daya,

Ayuba ya shaqu da Mahaifinshi Sosai Shiyasa Yaji Dacin Mutuwarsa,inda Kiyyaya da tsana gami da tsangwama,ce Tsakaninsa da “Yan Uwansa don ko da a kazo rabon Gado Sallau da Lantana ,Cewa Sukayi Ayuba Bashi da gadon Ubansu Domin Ba Dan Halak! Bane ,Sai da Malam Liman ya tsaya tsayin Daka A kan Lamarin Sannan A ka fitarwa da Ayuba gadonsa a gidan Ubansa.
Duk Rayuwarshi gidan Liman yake yin ta ,inda ya kasance Yaro mai zafin Nema,a wancan lokacin duk Abinda ya ta6a sai ya zama kudi.

Sallau ya sakoshi a gaba Da bakin ciki da hassada ,duk inda yasan yana zuwa Nemansa sai ya je ya batashi.
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

✍????Writting by
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????

????18

Bissimillahi

A lokacin Sallau yayi Aure inda ya Auri “Yar yayar Lantana Mai Suna Fatsima suna kiranta da (Uwa!) Yarinya ce Mara kunya inda bata ganin girman kowa ,babba da Yaro ,Har Mahaifiyarta fito Na fito take da ita,Bata da Aiki sai yawon tallace Tallace to har a kayi Auran Uwa Na fita kofar gida ta dasa kasko Na suyar Awara gefe ga gyada nan cikin Faratin A quq-qulle a leda marau da tubes! Haka take Tara matasa ai ta shirme ,idan har kan dillanci tazo nan ma tana tabawa
A takaice ita ce take ciyar da Sallau domin shi ya zauna zuciyarsa A mace yaqi ya fita ya nema ,Gwara Maman shi ya kan fita yayi buge bugensa ya samu Na kashewa,ita ko Lantana Kasuwanni take bi tana tallan zogale da kuli ,Da wannan suke Samun Abinda zasu kai bakinsu.

To shiyasa daga Lantana Har Sallau! Suka taso Ayuba a gaba da kyashi gami da hassada,Wanda hausawa sukance (Hassada ga mai rabo taki ce)

Ayuba ya shaku da “Yar Uwarshi Atika ,domin duk wani Sirrin shi tasani ita da Gwaggo Shatu marikiyar shi ,

Haka ya cigaba da Rayuwa ,tare da Kiyyaya da tsangwama gurin “Yan Uwanshi,Amma duk da Haka shi bai fasa Zumunci da su ba,

Hafsatu ita ce Ayuba ya Amince da tazama Uwar “Yayanshi, Domin ya yaba da tarbiyar ta gami da nutsuwa da kamun kai,”Yar Makotan Su Atika ce Yayarshi Ita ma haifinta ya rasu,to haka dai Malam Liman ya tsaya Masa tsayin daka ganin Tabbatuwar Auran

Nan ta tare gidansu ,Bangaran shi Na gado,Uwa da Lantana suka ce dawa Allah ya hadasu,suka sanya ta a gaba Babu irin Muguntar da basai Mata,yarinyar duk ta kwar zane,kullum cikin Aikin Awarar Uwa take tamkar ita take Auranta,inda Allah ya tai maketa ma ,Lantana,bata yini a gida Sai Yamma take dawowa daga zarar ta dawo ,zatai ta kwala Mata kira tana zagi! Tai ta sanya ta Aikin Wahala ,ko da ta Samu ciki basu bar ta ta huta ba, Kullum idan Ayuba ya shi go gidan yaga irin wahalar da take sha,sai bakin ciki ya kamashi gashi bashi da Bakin Magana,Lantana ta tsigale shi, Kullum in sun shiga daki yai ta Rarrashin ta yace”tayi hakuri Shima ba yason Wannan Wahalar da take sha Da yana da Hali da sai ya kama mata Haya ko daki guda ne,to Babu Hali domin duk wasu hanyoyin Samunsa Sallau ya shiga ya fita ,ya rabashi dasu da Asiri da kuma Ziga ga Mutane ,cewar kar Wanda ta hada hurda dashi domin ko ba Dan gari ba ne,Zai cuce su ya gudu

To Lokacin A kwai qarancin Ilimi gami da Wayewa Sai Jama’a suka dinga gudun Ayuba,
Tunda ga Lokacin ya dai na sana’a sai dai ya fita tayi buge bugensa ya dawo gida

A lokacin Uwa! Tana da Yara Biyu Namiji da Mace’Iro da Shamsiyya, To iro tun yana shekara Uku ya iya yawon Talla kusfa kusfa,haka zata kasa masa a faran ti tun Safe ,ba bu Maganar zuwa makaranta
Haka ake Zaman doya da Manja a gidan Domin Maman ma ya yi Aure shima Matarshi Na gidan , Mai suna Halima inda ta kasance mace mai sauqi hali gami da Hankali ,kwata kwata bata kaunar Abinda Su Lantana sukewa Hafsatu Matar Ayuba ,sai ta riqa Jan ta a jiki tana tausar ta,nan ko Uwa!! Tace dawa Allah ya hada su ,shiga fita Dari sai ta Zubda musu Ha baici ta dauki gaba da Halima ,duk dai a kan tana kula Hafsatu,ita ko Lantana dama Macace mai mugun kwadayi kasan cewar Maman duk ya fisu Samu yasa bata son Laifin sa ko Na Matarshi shiyasa ta kyale ta take Kula Hafsatun Dan kar ta dai Na bata Abinci da kayan dadi in Maman ya siyo Domin ,shi kwata kwata ya Manta da wata Lantana ta Matarshi yake,in Anyi Magana yace ai tana fita Nema taci da Kan ta,shima yanzu Nauyi yayi masa yawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button