GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin mamaki Ashiru mai Napep yaja Napep din yana satar kallonta ta cikin mirrow din din Napep din nashi, mamakin karfin halinta yakeyi da yadda take magana cikin gadara gami da takama ita ba “yar kowan kowa ba sai mugun bacin rai,a zuciyarsa yace” wallahi kika sake kika fadi wata magana akan masaurar garin nan sai kin kare rayuwarki a kurku ko kuma mutan gari suyi kuli kulin kubara dake in basu kashe ki ba ma, yana so ya fada mata haka a fili amma sabida yadda take masa mugun kwarjini yasa ya yi gum da bakinshi sai satar kallonta yakeyi
Ganin yadda tayi wani kicin-kicin da fuska.

Binta Umar Abbale
08089965176
[17/06, 02:59] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

[16/06/2019 9:50 PM] Binta Umar Abbale: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

           *NA*

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA YARO DA KUDI ````GIMBIYA BALARABA
08089965176

“`BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

????26

_ Sha daya saura minti biyar Balaraba ta shiga kasuwar lokacin costomas dinta sun cika gurin, da ka dubesu zaka san sun ci sun ta da kai, sabida kudi, Balaraba ta shiga gurin cikin tafiyarta da qasaita kamar wata basarakiya, fuskarta babu walwala ta din ga bin gurin da kalo sabida kwata-kwata bata san kazanta ko kadan, wasu “yan mata ne guda uku suna kai wa da kawowa kokarinsu su sallami duk Wanda yake gurin cikin nutsuwa suke komai.
[16/06/2019 10:25 PM] Binta Umar Abbale: Ta nemi wata kujera ta zauna tana duba wayarta, bata so ta shiga inda mutanan suke sabida ta lura da motar Alhji Yusuf a gurin mutumin ya takura mata, babu irin korar karan da batayi mishi ba a gurin amma sabuda tsabar bakin naci yaki hakura da dai na zuwa cin abinci

Tana zaune tana kallon mutane na kaiwa da kawowa cikin kasuwar kowa yafito nema,a fili tace”Allah ka bamu sa’a

Wani al’amajiri ta hango kusa da wata me kosai sai ta kirashi da hannunta,

Da sauri yaron ya taso har yana hadawa da gudu,

Gudar dari biyar ta ciro cikin pose din ta ta mika masa, gami da cewa”je ka bawa mai kosai kace ta yi muku sadaka in jini”

Hannunshi yana karkarwa ya karba, yana godiya sosai, ya wuce da Sauri

Iyani, mai kosai soya kosai kawai takeyi tana addu’ar Allah yasa kar tayi mata bandaro gashi sha daya na safe har ta wuce ji take tamkar ta dora hannu a ka taita kurma ihu sanin da tayi in kosai nan yayi kwantai bata da yadda zatayi a gida sabida tabar marayun”yayanta,

Almajirin yace”Iyani gashi in Gimbiya wai ki mana sadaka da kosan ki”

Da sauri Iyani ta dago kanta tana kallon Yaron jin ya abanci Gimbiya tasan babu mai wannan sunan sai mutuniyarta Balaraba

Gudar dari biyar ta gani hannun Yaron sabuwa dal

Tayi saurin kallon rumfar Balaraba,aiko suka hada ido Balaraba ta dago mata hannu fuskarta a sake

Iyani ta washe baki tace”Uwar dakina ashe kinzo tun dazu nake tambayar Hauwa’u tace baki karaso ba, kila kina kan hanya, yau kin makara gaskiya”

Fuska a sake tace”wallahi kuwa kinga mun hadu da gosolow a hanya,wai Yaron sarki zai wuce shine fa a ka kashe hanya”

“A’a lallai ai a kashe hanya,cewa zakiyi masu garin ne za su wuce”
Iyani tafada tana tsamo kosai cikin matsami

Tsaki Balaraba ta ja bata kara cewa komai ba ta bar Iyani tana 6a6atun surutunta.

Nan almajirai sukayi dan dazo suna karbar sadaka,ganin haka yasa Balaraba ta kira daya daga cikinsu tace ya shiga kasuwa gurin Delu mai kunu ya karbo na dari biyar shima irin Wanda take daurawa a Leda

Da gudu Yaron ya ruga ya shiga cikin kasuwa sai murna yakeyi

Girgiza kai tayi kawai a fili tace”lallai ko wane Yaro da irin tarbiyarshi, Allah ka shirya mana zuri’armu

Alhaji Yusif ne ya fito yana ta raba ido so yake ya ga inda mutuniyar tashi take sabuda yanzu ya tambayi daya daga cikin yaran ta tace masa sai yanzu ta karaso

Yana sanye da wata muguwar shadda wa gambari mai uban tsada taji sitati sai motsi take yi kanshi da hula zanna bukar kana ganinshi kasan dan birni ne kuma akwai daloli yana da kyau dai-dai misali irin mutanan ne masu qiba amma ba sosai ba

Tana kallonshi yana dube dube tai masa banza,sai ta fito da wayarta ma tana dubawa,

Kamar ance ya kalli gefan damanshi sai ya ganta zaune cikin kujera

Ya kasa boye farin cikinsa sai ya saki dariya,har sai da hakoranshi tas daya yana sanye da hakorin magana, kana ganinshi kasan Alhajin Allah ne.

????YANZU MUKA FARA
[18/06, 22:42] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

[18/06/2019 3:01 PM] Binta Umar Abbale: [18/06/2019 2:08 PM] Binta Umar Abbale: ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

          _*NA*_

®BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
08089965176

???? Zamani writes Association????????

Al hayyu Al kayyumu ya Allah

????27

_________Kicin-kicin da fuska tayi gami da dauke kanta ta cigaba da danna wayarta tamkar bata san da wata hallita ba a tsaye a kanta.

Gyaran murya yayi fuskarsa dauke da murmushi mai kayatarwa yace”ranki shidade Gimbiyata gaisuwa daban take sarauniyar zuciyar Yusif zuciya takice na baki ki yadda kikeso da ita”

Kanta a kasa tana danna waya har ila yau takasa dago kai ta kalleshi ballantana tabashi gurin zama

Murmushi yayi yace”ko zan iya zama, tun dazu nake nan gurin ina sauraron zuwanki naji shiru, sai yanzu Hauwa’u ta ce dani kinzo”

Dago kanta tayi ta zuba masa idanunta masu rikita masa lissafi, tace”ajiya kabani da zakazo kana nema da sanyin safiyar Allah”

Dariya ya saki mai tattare da shauqi gami da so da kauna sam bai ji haushin kalaman ta ba.

Ya zauna kujerar da take fuskantar ta yace”e mana baki san na baki amanar zuciyata ba”

Mtssss taja kawai ta maida hankalinta kan wayarta gami da duddubawa,ta bawa banza ajiyar Yusuf.

Murmushi ne,kwance a kayatacciyar fuskarsa kwata-kwata yarinyar bata bashi haushi asali ma, wani sabon so da kaunarta ne ya mamaye zuciyarsa

Kawai ya zuba mata ido kawai bai ce mata komai ba

Harara ta ban ka masa gami da cewa”bai yuwa kazo ka tasani a gaba kana kallo tamkar Wanda ya samu madubi, ni kam bana son kallo wallahi”

Har yanzu da murmushi a fuskarsa yace” ke kin fi madubi a gurina tunda kullum dake nake kwana nake tashi a zuciyata,Gimbiya kinki ki amince dani, Why”
Yafada muryarshi na karkarwa

A nutse tace”wace irin amince zan yi maka ne? bayan kasan kai kafi qarfina, ko ni sam bana sha’awar auran namiji mai dukiya ko mulki,talaka zan aura dai-dai dani,nafada maka tuntuni”

“Wai me yasa kike magana irin na jahilai ne,Gimbiya, kituna (Annabi Muhammad Slw) ya auri mace mai tsananin dukiya kuma bazawara, kinga kenan babu laifi cikin abin,namiji ya auri mace mai dukiya,ko mace ta auri namiji mai kudi ko mulki,wannan maganar taki bata da tushe ballantana makama”

Shiru tayi sabida bata da abin cewa

Yace”kinyi min shiru Gimbiya”

Wayar ta kashe ta kalleshi fuskarta babu yabo babu fallasa tace”shikkenan kaje kawai zamuyi maganar ko a waya ne,kaga nan cikin kasuwa ne bana son kallon da mutane ke mana”

“Ok baki dauki maganar da muhimanci ba shiyasa kikace zamuyi a waya wannan ba dai-dai ba ne, me makon kice min inzo gida in sameki, zai fi ai”
Ya karashe maganar yana karyar da wuya,cikin nashi salon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button