GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fuskarahi a sake yace”godiya nake Gimbiya ta gidan Maddibo”
Murmushi tayi tana wani fari da ido,suka jera a tare suna hira cikin fahintar juna, “yan yaran da Balaraba take rabawa naira biyar-biyar kullum in za tafita, suna zaune bakin hanya suna ta wasa, duk da dare ne kuma babu wadataccan haske,amma sai sa suka gane ta, nan suka rude,” laaaaa Aunty Balarabamu, a dawo lafiya”
“Allah yasa”
Balaraba tabisu tana amsa wa babu kyara ballantana hantara!

Wata katuwar Mota taga sun nufa, ga wanu mutum tsaye jikinta,jikinsa sanye da wasu jajayen kaya, irin na gidan Sarauta, cikin mamaki ta dinga bin Maddibo a nutse sam babu wata fargaba a tare da ita,

Sarki! Yana zaune cikin mota yana danne-danne cikin waya ranshi yayi mugun baci! ganin yadda Maddibo ya bawa banza ajiyarshi yana can yana zance da budurwarsa ya manta tare suke,wato da ma dan ya wulakanta shi ne yasa yazo ya takurashi dole sai yayi masa rakiya,dole ya nuna masa bacin ransa,dan bazai yi zaman banza, cikin mota, sai kace mara abin yi”
Kokarin bude motar yaji a nayi, sai ya gyara zama a nutse ya sanya hannushi ya bude motar ta ciki sabuda ya sanya mata sucurity dole sai shine zai bude,
Shan kunu! yayi domin yasan Maddibo ne, ya bude motar kawai ya dauke kansa, ya mayar da hankalinshi kan wayar dake hannusa

Balaraba na tsaye a bayan Maddibo duk taga abunda yayi, so take ta kalli fuskarsa, sosai babu haske sai hasken wayar hannunshi,

Cikin Dariya Maddibo yace”Mutumina kaji ni shiru ko, kasan halin Gimbiya tawa sai a hankali”

A fusace! Sarki! ya dago kanshi ya watsa masa wani kallo,kana yace”kaga Malam abunda ya dame ka ne wannan, dan tsabar rashin mutunci ka tafi kabar mutane zaune a cikin mota kamar wasu marasa abunyi, dubi time fa”
Yafada yana kallon haddadan agogon dake daure a hannushi, ya cigaba da cewa”tun misalin takwas da kwata duba fa sai yanzu ka dawo tara da minti ashirin da biyar, duk irin zancan da zakuyi da kai da “yar towo-towon naka ai yaci a ce ka tuna dani,tunda dai ni ba banza bane da zaka shanya ni kamar wani shashasha”
Ya karashe maganar cikin masiba!

Tunda Ya fara magana gabanta ya dinga faduwa! ko cikin mafarki taji wannan muryar baza ta taba mance da me ita ba, Sarki! ne Yariman Sarki Almustapah Maimarta ba sarkin garin nasu mai adalci,
gabanta ya cigaba da dukan uku-uku jin sunan da yake kiranta dashi, wai “yar towo-towo.

Muje zuwa

Comment
Vote and Share
[05/07, 12:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

   ∆∆∆∆∆∆   
    _*GIMBIYA BALARABA*_
    ∆∆∆∆∆∆
             ????????????????????????????????



         _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir-rahamanir-rahim

????38

              *Real Bintu Batula*????

Rai a bace Maddibo yake kallonsa, jikinsa duk yayi sanyi jin irin bak’aken maganganun da Sarki! yake ya wa Balaraba, kwata-kwata ya rasa me zai ce masa, kallon Balaraba yayi jiki a sanyaye ya bude baki zai yi magana, tayi saurin tararsa,fuskarta babu yabo babu fallasa ta kalleshi a nutse tace”Kar ka bata ranka a kan abunda abokin ka ya fada a kaina, tabbas kamar yadda ya fada cewa ni “yar bakin kasuwa ce,haka abun yake, duk da nake ” yar towo-towo ban taba nema a gurin uban kowa sabuda haka babu wani mahalukin mutum da ya isa yazo har kofar gidanmu yace zai ci mun mutumchi in kyaleshi komai kudinshi da mulkinshi wallahi”

A nutse ta kalli Sarki! dake zaune cikin mota yana jin duk abunda take cewa kwata-kwata bai yi mamakin jin abunda tace, Sabuda tun da tafara magana ya gane ko wacece, tabbas muryarta baza ta taba bace masa ba.
Wayarshi ya ke dubawa amma hankalinshi na kanta, duk da cewa a kwai duhu a gurin hakan bai hanashi kare mata kallo ba, ta kasan idonshi.

Cikin isa da gadara Balaraba ta kalleshi shekeke! tace”Idan ka isa kai wani ne ka aje wayar muyi magana da kai, bari kaji wani abu, ni Sunana Balaraba Ayuba Tanko kamar yadda kasani, kana ji na ko”? tafada tana hura hanci, kana ta cigaba da cewa, “kai kuma in har ban mance ba Kai ne Almansor Sarki! dan Sarkin Almustapah, hakane ko ba haka ba”?
tafada cikin sigar tambaya gashi ta tsare shi da ido, tana tsaye babu fargabar komai a tattare da ita, Cikin jarumta tacigaba da cewa” Wallahi baka isa kazo har kofar gidanmu ka ci mun mutumci ba, domin ni bani na kira ka ba”

Tsit!!!! gurin yayi Maddibo yana mamakin jarumta irin ta Balaraba,ko shi da yake Namiji bazai iya tsayawa gaban Almansor har ya gaya masa magana irin wannan ba, sabuda kwarjinin da Allah yayi masa.

A tsanake ya dago kanshi fuskarshi a murtuke, ko da wasa bai kalli inda take tsaye ba, murya a cunkushe yace”in kagama abunda kake kashigo mutafi,in kuma baka gama ba zan wuce kawai, sai katawo” “Wai me yake Faruwa ne,? tsakaninku naga kamar a kwai abunda kuke boya min, gaskiya banji dadin irin yadda kuka gaisa da junanku ba, abun bai min dadi ba”
Maddibo ya fada yana kallon Balaraba,

Murmushi tayi mai cike da takaici tace”Yusuf abokinka dan rainin hankali ne, wallahi ni kuma kasan bana daukar raini, ni “yar talaka ce, amma ban nema gurin wani ba sabuda haka babu mutumin da ya isa ya zage ni ban rama ba”

A fusace!Sarki ya bude murfin motar Balaraba na tsaye jiki tayi taga-taga kamar zata fadi,cikin tsoro ta matsa gefe,gabanta yana dukan uku-uku, duk da cewar babu wadataccan haske a gurin sai hasken farin wata, hakan bai hanata hango tsantsan bacin rai a fuskarsa ba,
ganin fitowarsa yasa Buba Direba dake can gefe a tsaya yayi saurin karaso gurin yana baza babbar riga, ya na zuwa ya zube a gurin gami da dunkule hannunsa alamun jin jina, yace”ranka shi dade, a kwai abunda za’ai maka ne”

Cikin wani irin murya yace”Babu abunda za’ayi Buba koma inda kake”

Buba ya mike da sauri, kanshi a kasa yace”Allah shi taimaki Yarima Sarki Allah ya ja Zamanin ka”

Da Sauri Balaraba ta dauke kanta, ganin ya maido da hankalinshi kanta, ya zuba mata ido, kawai yana kallo, Lokaci guda ta nemi nutsuwar ta tarasa jikinta yayi mugun sanyi, ganin shi tayi yana matsowa kusa da ita a hankali, fuskarshi a murtuke! jinsa daf da ita yasa ta jingina da jikin motar a karo na biyu, kamshin turaransa duk yq cika mata hanci, sai sa ya tsaya daf da ita sosai har numfashinsu yana haduwa, sannan ya kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi,da kassara jikin duk wata “ya mace me ji da kanta

A nutse a bude bakinsa yace” Duk abunda kikayi a yanzu, bazan yi mamaki ba sabuda nasan zakiyi abunda yafi haka” Wani irin kamshi taji yana futa daga bakinshi, lokacin da yake mata magana, kanta ta sunkuyar kasa kagabanta na lugede tunda take, babu wani da Namiji da ya taba kusantar ta kamar haka, kokari kawai take ta kwaci kanta, amma babu hali,sabuda yadda ya yi bake-bake a gurin,duk tsahonta ya rufe ta.

Yayi tsawan Minti biyu kafin ya kara cewa komai kana ya cigaba da cewa” Babu mamaki duba da yanayin unguwar da kika taso a ciki, babu abunda yake damunki sai tsan-tsan jahilci, da gidadan ci , da Zama cikin maza, a cikin kasuwa, shashashar yarinya kawai, zan koya miki hankali, zaki nuna min da me kike gadara, da kikewa kanki kallon ke wata aba ce”
Yana gama fadin wannan maganar ya tattaro miyau, a bakinshi ya dai-dai ci fuskarta ya tofa mata, ya dora mata da wani banzan kallo yace”ina sauraron ki da duk hukuncin da zaki dauka a kaina”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button