GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna zaune a falonsa ko wacce kujerar ta daban da “yar uwarta babu wacce tayiwa ” yar uwarta magana, suna sanye da kaya iri d’aya Shadda ce, sky blue anyi musu d’in ki Aliya taji sirfani duk gaban rigar ko wacce ta d’ora d’auri dai-dai da kwalliyar ta, gwal kuwa kamar yayi magana hannayen su da wuyan su, takalman su iri daya ne, Azima da Halisa sun sha kwaliyyar fuska, babu Mayafi a jikinsu, Balaraba kuwa babu laifi fuskarta babu komai sai farar hoda da kwalli da ta zizara a idonta, bayan haka ko man leb’e bata sa, amma haka bai hana bayyanuwar kyanta ba, ta yafa k’aramin mayafi Wanda ya sauko ya rufe mata k’irji.

A hankali yake sakko wa yayin da k’amshin tura ransa ya cika gurin , dukanin su suka mai da su kansa,,

Kallo guda tayi masa ta d’auke kanta gabanta na fad’uwa. Yana sanye da shadda irin jikin su Sak,, anyi masa dinki irin na zamani,, me falmaran wacce yaji sirfani me tambarin sarautar su,gaba da baya hular shi ma da yanki shaddar aka had’a ta,, kafar shi sanye da wani ruffan takalmi mai gashi-gashi sky blue hannunsa daure da agogo na zallahar azurfa, ya tsunsa ma zobuna ne manya-manya masu d’auke da tambarin sarautar su.
Cikin nutsuwa ya k’araso gurin su,, Fuska babu yabo babu fallasa yace”Ku tashi muje” a nutse ta mike jin abunda yace, gaba yayi suna bin shi a baya,, sai ga Shahid da sauri ya tare shi tare da wasu fadawa su uku suna take masa baya, Shatima yace”Kuyi tafiyar ku kawai,, suka ce “An gama ranka ya Dade, magana yake masa k’asa-k’asa, tsayawa yayi yana d’an hararsa, shi kuma ya sa dariya, yace” Hakane mana sai kayi gaba ka bar amaran naka a baya kai fa d’an gata ne” banza tayi masa yana d’auke kai da alama yau “yan muskilancin nasa na kusa,, Shatima ya k’araso tare da su Balaraba dole suka tilas tashi ya shiga tsakiyar su,, suna tafiya su uma suna take musu baya.

Tunda futowar su har zaman su a masu hotona da vidio suke aikin su, marok’a duk sun cika gurin da roko, sosai gurin ya cika ya tumbatsa da mutane kowa sai farin ciki yake, ciki kuwa babu ” yayan Waziri Zayyanu ko guda. D’aya suna can bakin ciki kamar ya kashe su, jin cewar har governor sai da ya hallarci gurin.

Walima tayi kyau sosai an raba kaya naci Dana sawa jakkunkuna atamfofi masu d’auke da hotanshi da amaran sa , duk Wanda yazo gurin ya samu kuma yayi guziri. Bakwai shaura aka tashi saboda lokacin sallahr magariba ne. Kuma bayan sallah Isha’i Mama tace Ko wacce za’a kaita dakin ta.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????106

Hannuwan ta ya zubawa ido kurr!! Sun sha uban Jan lalle wanda yayi jajazur har ya fara yin b’aki, sosai abun ya burge shi kuma ya bashi sha’awa,, nata duk ya fi tafiya da imaninsa, nasu Halisa bak’i ne, irin wanda ake zanawa shima yayi kyau babu laifi, kowa da kalar nashi,Cikin nutsuwa ta had’a plate uku kowa da nashi,, ta mik’a masa nashi tana fad’in “Bisimillah” Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido yace”Ke ina naki plate d’in, kin had’awa kowa nashi” babu yabo babu fallasa tace”Na ci abunci kafin na futo,, kai tsaye yace”Ko kinci dole kici na nan, ka’ida tace, wannan” Cikin mamaki ta kalle shi, ganin yanda ya b’ata fuska yasa ta fara zuba abuncin domin bata son ayi ta Jan magana,,Shiru gurin yayi, sai motsin cokola, satar kallonsa take yanda yake cin abunci kamar baya so,, ita kanta taunar sa ma abun kallo ne, Halisa kanta ya k’ara girma ganin yanda yake kula da ita domin shine ma ya tsiyaya mata ruwa,, ya mik’a mata lokacin da ta k’ware ganin, yana sanya Balaraba aiki yasa suka kara mike kafa suna ganin sun fita daraja a gurin shi kuma yasan su dama basu saba da aikin wahala ba,, shine ya fara mik’ewa daga gurin,, ganin ya tashi yasa ta mike da sauri ta gudu part d’inta… To Azima ma da ta kammala mik’ewa tayi ta wuce part din ta, aka bar Halisa tunda itace take da miji a hannu jiya da yau.



Tsito da Waziri ne zaune cikin duhu,, Aljani Mak’asudu ya hauro kan Tsito nan suka fara magana da Waziri,, yana fad’a masa buk’atun sa, Mak’asudu yace”Akwai alkwarina a kanka na k’afa biyu kar kace na manta da wannan alk’awarin ina sane dashi, kuma sai na bi jinina,, wannan buk’ata kuma da kawo mana, zata biya amma da sharad’i idan ka kuskura ka kauce sharad’in da muka gindaya maka to sharrin zai koma kanka kaji!!!!!!! Ko”!!!!!!!? Waziri yace”Arne ya dafa maka ai duk sharad’in da kuka gindaya min ina me tabbatar maka da cewar zan bishi bazan kauce ba” Mak’asudu yasa dariya yana fad’in”Shikkenan ni zan jirge!! Yanzu amma zan Sanar da Tsito duk sharad’inmu sai ya fad’a maka” Waziri yace”A sauka lafiya Mak’asudu me mukulin mulki mak’asudu d’an gidan K’azaza gaba salamun baya salamun Ubana”” Tsito ya dunga wata irin katantanwa a tsakiyar d’akin yana wani irin ihu!!!!!! D’if dakin yayi shiru kamar anyi ruwa an d’auke.

Wajan minti goma Tsito ya dawo dai-dai cikin duhu ya kalli Waziri yace”Da alama d’azu muna magana da kai Mak’asudu ya hauro ko”?
Waziri ya gyad’a kai yace”Akwai sak’on da yace zai fada maka ka fada min” Shiru Tsito yayi yana sauraron Mak’usudu sai gyad’a kai yake alamun yana sauroro,, bayan ya gama sauraron Mak’asud’u ya kalli Waziri yana fad’in”Yace”Mu nemo bak’ar kulb’a da bak’ar kunama sai bak’in b’era dunka sai tsohon kadan gare Wanda ya soma sab’a saboda tsufa, duk a yanka su a cire musu fatar jikinsu,, a shanya ta bushe, sai ka kafa kusa a d’akin ka, duk ka kafe fatocin bango d’aya ka samu Jan yanki kasa a tsakiya, bayan nan kuma hanjin su,, a had’a shi guri guda a sanya su su bushe a dake lukwi sai a zuba masa a abunci, da iziinsa sai ya mutu idan bai mutu ba to zai rasa wani b’angare na jikinsa, sannan in ka kuskura mutum ko guda ne, ya shiga dakin Da ka kafe fatocin nan to abun zai dawo kanka,,sai magana ta k’arshe yace”Ka tafi bakin kogi da k’aton rago me tozali ka yanka masa zai shanye jinin” Waziri yace”Duk za’ayi da izininsa mutukar bukatar zata biya, yanzu yanda za’ayi na samu wad’annan dabbobin shine abun dubawa” Tsito yace”Wannan babu matsala gobe sai ka futa dani a mota ni zan samo maka,, sai dai ka ware min lada na” Waziri yace”Duk kar ka damu zan maka kyauta ta ban mamaki in zaka tafi” Nan sukayi sallama Waziri ya futa yana godiya ga Mak’asudu.



Kwanan Sallau Uku a asibiti yace ga garin ku nan, Lantana ta dunga kuka kamar ranta zai futa,, Uwa! Ma duk da ya sake ta ta koko da mutuwar Sallau,, Shamsiyya kuwa tun sanda ta dawo daga gidan Arrama ta kwanta ciwo kariris,, Amai da zazzab’i duk ta rame ta jeme sai uban zubar da miyau da takeyi,, jama’a ‘yan zaman makoki dayawa duk San fahimci ciki ne da ita Uwa! Ta gane da sauran mutan gidan rudanin mutuwa ya hanasu nuna b’acin ransu domin hausawa nacewa wani tashin hankalin yafi wani,,, Lokacin da Balaraba taji mutuwar Sallau kuka ta dungayi sosai, Mama tai ta rarrashin ta, tare suka tafi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button