GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Har ta nufi k’ofa sai ta dakata ta juyo tana kallon Balaraba tace “Ki kula da Almustafa,in ya tashi daga baccin ki bashi abunci, na lura kwana biyu yana wasa da cikinsa,duk ya rame”

Balaraba tace”Insha Allahu Zanyi Mama,Agaida Hajiya.

“Zataji insha Allahu”
Mama tafad’a lokacin da take k’okarin futa.

Shiru yayi duk yana jin zantukan da sukeyi,har yanzu idonsa a lumshe yake yana kallonta duk abunda take, cin abinci take a nutse har ta kammala,ta goge bakinta, shiru tayi tana tunanin ta yaya za’ayi ta tasheshi daga bacci har ta bashi abunci, dole ne ta cika umarnin da aka bata.

Mik’ewa tayi ta nufi inda yake, ganin ta nufo gurinsa yasa ya rufe idon gaba d’aya ta k’araso tayi tsaye kansa tana kallon fuskarsa, tsigar jikinta taji tana tashi ganin wani zallah kyau da annuri da yake futa a fuskarsa, mai d’auke da zara-zaran gashin idon had’e da sanjensa Wanda ya kewaye d’an mitsitsin bakinsa, tsabar hutu da jin dad’i yasa tafarshi tayi wata irin kala, ita ba fara ba ita ba b’aka, hakika Allah yayi hallita a gurin, ko da take farar mace, tayi shawa’ar fatarshi ji take ina ma itace take da Irin fatar.
Hannusa ta kalla mai d’auke da zararan zaran yatsu ya d’ora kan cikinsa, tayi saurin kauda kanta tana tunanin ya zatayi ta tashe shi, cikin sa’a d’aya daga cikin wayoyinsa tafara k’ara, yanaji yayi shiru, kallon fuskar wayar tayi, Matata,sunan da tagani yana yawo kan screen ni d’in, katsewa tayi wani kiran ya k’ara shigowa wata zuciyar tace d’auki kiyi magana, kiji wacece,tunda dai ita iya saninta dashi tasan bashi da wata mata, sun kuya tayi zata d’auki wayar yayi saurin dafe wayar da hannusa, hannuwansu suka had’u guri guda. Yarrrrr!! Ya ji a jikinsa sai ya d’amke wayar a hannusa tare da hannuta,ya bud’e idonsa tarr! A kanta sukayi ido hud’u
Abunda yasa ya hanata d’aukar wayar shine gudun rigimar Halisa yasan itace saboda ringing din da yasa mata daban ne, yasan taji muryar mace, tashin hankali zasuyi
Zare hannuta take k’okarin yi ya rik’e ya had’a da nashi da wayar ya kara a kunne, cikin wani kasalalliyar murya yayi sallama.
Tana jiyo muryar Halisa tana fad’in Habibi ganinan shigowa Shashen Mama yanzu na futo shashanka Buba yace baka shigo ba tun da safe, da ka futa”

Kamar baya so yace “Sai kin shigo “
Kashe wayar yayi yana me kallon hannun Balaraba dake had’e da nashi, babu zato taji yace mene kika tsaya min aka, tun d’azu”

TSANTSAR BUTULCI

              *_NA_*

BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

Littifi mai dauke da darusa gami da cin amana da iri-iri, kar ku bari a Baku labari
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????


We are here to educate,motivate and entertain aur readers


DIDEGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM

????77

Daburcewa tayi, tana k’okarin cire hannuta daga nasa, tace”Mama ce tace ka tashi kaci abunci yanzu”

Kallonta yake cikin nutsuwa yace”Mama batace ki tashe ni daga bacci ba, cewa tayi in dan na tashi ki bani,ai duk inajin abunda kuke fad’a”

Shiru tayi na minti biyu tace”Hakane, ko da yake dama hakkin ciyar da kai abunci ba akaina yake ba, ga matarka nan sai ta baka”
Tana gama fad’ar maganar takama hanya zata wuce,ya rik’e hannuta, yace”Ba ita aka umarta da ta bani abunci ba,ke a ka umarta da ki bani saboda haka,sai ki tsaya ki bani”

Cikin sanyi jiki tace”Wai me yasa kake son rik’e min hannu ne, nifa ba muharramar ka bace,abunda kake babu kyau,nasan ka sani kuma kana takewa”
Cikin d’an b’acin rai tayi masa maganar.

Hannunta ya saki,yana d’an sosa kansa irin na sabo, shi bada wata manufa yake tab’a jikinta,illa kawai irin sabon da Halisa tayi masa,n yawan kusantarsa,duk da yake itama baya wani zak’ewa iya kacinsa da ita ya rik’e mata hannu, ko kuma in zai mata magana ya d’an zungureta daga haka baya k’arawa,itace me zak’ewa da yawa yana tsawatar mata.

Ganin ya sakar mata hannu yasa ta wuce can inda kayan abuncin suke ta fara had’a masa lafiyayyan towon shinkafa miyar taushe me d’auke da wadattacen nama,da man shanu, cikin wani had’addan plate ta had’a ta rufe da irinsa ta nufu in da yake zaune.

K’asa ya sauko ya jingina jikinsa jikin kujera, tazo ta aje masa ta koma ta d’auko lemo jus ta da ruwan roba nan ta aje kusa dashi, ta mik’e zata bar gurin,gyaran murya yayi a tsanake yace”Dawo ki zauna ki bani kamar yadda aka umarce ki”

Cikin Mamaki Balaraba ta juyo tana kallonsa, a dake tace”Ban gane abunda kake nufi ba”?

“Ai baki gama aikin ki ba, yafad’a yana kallon k’ofa jin kamar za’a shigo,kafin tayi wani tunani Halisa ta shigo da siririyar sallama taci uwar kwalliya tamkar wata sarauniya, turusss!! Tayi ganin Balaraba kan Habibinta, shi kuma yana kallonta, k’okarin dane abunda taji a zuciyarta tayi ta k’arasa kuda dashi, cikin wata irin tafiyar k’asaita

Balaraba kuwa saurin kauda kanta tayi, cikin zuciyarta tana wani irin jin haushin Halisa haka kawai.

Ta k’araso ta zauna kusa dashi har kafad’arsu tana gugar juna,cikin tsabar kwarkwasa ta gaishe ya amsa babu yabo babu fallasa, yace” Wannan kwaliyyar da kikayi ni kika yiwa ko kuwa”

Cikin jin dad’in yaba kwaliyyarta da yayi tace” Kai nayiwa gwarzon zuciyata me mulkin zuciyata”

Wani k’asaitaccan murmushi yayi yana kashe mata ido yace
“Nawa ne kud’inta in siya”

Fari da ido Halisa tayi tace” Bana buk’atar komai sai so da k’aunarka”

Ganin yanda suke hira ta soyyaya sun shareta yasa Balaraba barin gurin da rai a b’ace!

Kallo ya bita dashi har ta shige d’akin da take.

Ita kuwa Halisa bud’e a abunci tayi ta fara bashi abaki sunayi suna hirar soyyaya ko da wasa bata yi masa zancan Balaraba ba saboda in gargad’in da yayi mata, kwanaki,a zuciyarta tace,kowa tasa ta fisheshi,ita k’okarinta taga ta mallake zuciyarsa ita kad’ai,don haka sai ta k’ara zage damtse tana ta shirya masa hira masu dad’i, sosai ya saki cikinsa yaci abuncin saboda dama neman me d’ebe masa kewa yake,bai samu ba.


To Sallau dai da k’yar ya koma gida tare da taimakon Mai gari da d’anshi Walidi,saboda tun a hanya ya jigata sai haki!yake tun lokacin da me Martaba ya fad’a masa cewar Balaraba zatayi aure a gidan shikkenan yaji zuciyarsa kamar ta dena aiki,sai haki!tsabar d’imuwa da tashin hankali sunyi masa katutu a k’ahon zuciya.

Duk suna zazzaune a tsakar gida suna jiran shigowar Sallau hankalinsu duk a tashe, kowa da abunda yake fad’a, akan Balaraba wai ita ta kai kararsa gurin Sarki!

A rirrik’e a ka shigo dashi Lantana ta tashi tana sallalami gami da salati dad’i take shikkenan,wannan “ya tasa anyi masa wannan bulala ta gidan sarki!Allah ya tsine miki Balaraba”

Ihu!Su Shamsiyya suke sukayi kan ubansu suka kakkamashi suka shiga d’aki dashi suna duba jikinsa sukaga babu wani k’warzane ko d’aya babu alamun duka a jikinsa.

Uwa!tace”Wai meye kake haka sai kace Wanda zai tada aljanu,tun safe munanan muna fargaba,gaka ka dawo kuma me makon kayi mana bayani kuma kazo kana wani nishi!sai kace kuturo”

Lantana tace”Ke rufe min baki shashasha kawai,bakya ganin halin da yake ciki,Allah yasa dai ba guba suka bashi yasha ko ya Ciba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button