GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ameen gimbiya ta”
yafad’a yana kallon Usuman dake kwance kan cinyarta yace”yayi bacci kenan”

“Baccin dai yake so yayi” tafad’a tana shafa kansa

Girgiza kai yayi yace”yaran suna bani tausayi sosai, in sha Allahu maraicinku ya k’are”

Wasu hawaye masu zafi ta d’auke tace”godiya a gareka gwarzo na zuciya ta,a yanzu banda kowa banda komai sai kai, nice kai, kai ne ni”

Sosai Moddibo yaji dad’in wannan kalamin nata, wani irin nishad’i yake ji a zuciyarsa

Hanyar gidan Sarki yaga ya nufa, bata kawo komai a ranta ba, sai da ta gansu dai-dai kofar shiga cikin gidan sarautar yana kokarin shiga da Motar tace” me za muyi a nan”?

Fuska sake yace”bana ce miki k’ebantaccan guri zan kawo ki ba,kinga nan gidan babu wanda zai san kina ciki,

Shiru tayi kawai gabanta yana wata irin fad’uwa, wata doguwar kwalta dake shimfud’e a cikin gidan suke bi, a hankali yake jan motar har suka iso shashen Sarki! me gadin gurin ya bude masa get ya shiga da Motar, gabanta ya dina fad’uwa wanda bata san dalili ba, duk inda ta kalla a gidan wasu irin tambari ne da zane-zane irin na sarauta anyi musu ado da wani abu mai kyalli,kasancewar a kwai haske tarwai a gurin, yasa taga hadiman dake kaiwa suna kawowa a gurin kowa da aikinshi, gurin aje mota suka nufa, tana ciki motar ta zama “yar k’auye ganin wasu shirga-shirgan mota masu kyau irin na masu a mulki,a fake a gurin, shima gurin k’ayata shi da wata rumfa, mai mai d’auke da ado mai tsari, parking d’in motar yayi, da sauri wani fade ya bude masa ya futo ya tsaya ya jingina jikin motar, ya futo da waya,yana k’okarin kiran Sarki!

Muje zuwa

Comment Vote and Share
[24/07, 16:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????

Bisimillahir-rahamanir-rashim

????59

Ya zaune a farlo cikin kujerar shi ta hutawa, wani k’aramin littafi ne a hannunshi irin na addini yana dubawa, idanunshi sanye da farin tabarau na k’ara k’arfin gani, yana cikin wasu kaya na shan iska, cikin nutsuwa yake duba littafin,sai yaji wayarshi dake can kan kujera tana k’ara, alamun an kirashi, mik’ewa yayi a nutse ya k’arasa inda wayar take yana dubawa Moddibo ne, a nutse ya daga, gami da yin sallama,
Moddibo yace” gani nan zan shigo da ita”

“Wacece” yafad’a cikin sigar tambaya.

Cikin mamaki Moddibo yace”har ka manta da maganar mu ta d’azu kenan”?

Shi sam! ya manta da sunyi wata magana dashi,sai yanzu tsaki ya d’anja k’asa-k’asa yace”naman ta ni, ina fatan kaja mata kunne dai”

“Baka da matsala da ita insha Allah”

Kashe wayar yayi,ya ajeta kusa dashi ya cigaba da duba littafin dake hannunsa.

A nutse Moddibo ya kalli Balaraba dake tsaye duk jikinta yayi sanyi, cikin zuciyarta take cewa anya batayi ganganci ba kuwa, ta guda daga gidansu,tabi wani namiji uwa duniya,duk tsiyar naka,shine naka amma tayi amanna da Moddibo ba zai cuceta ba.

Hannun Usuman ya kama, suka fara tafiya, cikin nutsuwa yake k’ara kwantar mata da hankali, ganin da yayi jikinta yayi sanyi k’alau.

Wata k’atuwar k’ofa me murfi biyu taga sun nufa, suna isa bakin k’ofar wasu bayi ne tsaye d’aya a gefe d’aya a gefe hannusu rik’e da wata sharb’ebiyar bulala, suna ganin Moddibo ne sai d’aya yayi saurin bud’e masa suka zub’e suna kwasar gaisuwa, a nutse ya amsa musu, suka gaida Balaraba, ta amsa a dake! sannan suka shiga ciki,

Ji tayi k’afarta ta nutse a cikin wani abu mai taushin gaske, da sauri ta kalli k’asa inda taga wani kwantaccan kafet ya mik’e samb’al har inda Sarki! yake zaune, wani mugun k’amshi ne ya ziyarci hancin ta, lumshe ido tayi cikin jin d’adin k’amshin ta bud’e ido tana rarrabashi cikin katafaran farlon mai d’auke da set d’in kujeru uku, ko wanne da sentar teble d’inshi a tsakiya, a tishawa su Sadiya da Usuman suka fara, saboda sanyin air condition d’in dake farlo, wannan atishawar da yaran sukayi itace tasa ya d’ago kanshi cikin isa yana kallonsu daga can bakin k’ofa, shi kuma Moddibo dama ya gano shi a can in da yake hutawa, a nutse yake tafiya domin zuwa gurin, Balaraba kuwa sam bata lura da mutum a gurin ba da suka shigo, shiyasa da taga Moddibo yayi wani gurin sai ta zage,jiki tana ta kalle-kallenta na k’auyanci.

Usuman ne ya rik’e mata hannu, yace”Yayarmu sanyi nake ji”
jikinsa sai b’ari yake, kallonsa tayi,taga da gaske sanyin yake ji, ta kalli Sadiya taga itama ta takure cikin hijabi,sai mutsu-mutsu take, rarraba ido take a farlon tana so taga inda Moddibo yake, yazo ya kashe musu wannan abun mesa sanyi, bata ganshi, ba dalili yana isa gurin Sarki! ya saki wani labule me igiyoyi masu kyalli yana gudun kar yayi masa halin nasa har Balaraba ta gani shiyasa ya saki labulen, duk iya laluben ta ba taga Moddibo ba, ga Usuman bayan atishawar da yakeyi har da tari sai k’warewa yake, sam! ta tsani matsalar “yan uwanta, kalle-kalle take a farlo ko zataga inda ake rage k’arfin fankar a cewar ta can ta hango wasu abubuwa a manne jikin bango, kai tsaye can ta nufa, batare da b’ata lokaci ba ta sanya hannunta ta murd’a da k’afi! aikuww farlo ya d’ume da wani sauti!! dimmmmmmm! da gudu! ta matsa daga gurin tana zare ido,wanda yayi dai-dai da futowar su Moddibo da sauri ya k’araso inda suke, yayi saurin yaje ya saisaita komai, shi kuma Sarki! tun kafin ya k’araso gurin yake zabga mata harara, yana k’araso gurin yayi mata wani banzan kallo cikin wani irin murya yace” ke bagidajiyar ina ne,uhumm! kawai zakiyi tad’aga mana hankali baki iya abuba kice zakiyi, ni wallahi bana son hauka”
yafad’a yana me zama cikin kujera tare da hard’r kafa d’aya kan d’aya

Sai da ta kusan suma,lokacin da taji muryar sa, hankalin ta ya tashi, sai ta nemi miyau ko d’aya ta rasa a bakinta, sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya, tana tunanin abunda yasa Moddibo ya kawo ta gurin mutumin da baya k’aunar ta, wata zuciyar tace”k’ila had’a baki sukayi dashi,domin ya wulak’an taki,dama namiji ba d’an goyo bane.

Shiru farlo yayi Modibbo ya rasa dame zai fara, Hannun Usuman ya rik’e da hannu d’aya, d’ayan hannun kuma ya rik’e Sadiya dashi ya kalli Balaraba yace”zo muje kinji Gimbiya”

D’ago kai tayi tana kallonsa fuskarta a murtuke tace”ina zamuje, Yusuf dama ka d’auko mu ne domin a tozartamu, ni banga gurin zama ba anan”
ta k’arasa maganar ta tana kokarin kama hannun Usuman dake cikin hannunsa,

Tayi-tayi ta k’wace hannun daga cikin nasa ta kasa, rarrashin ta yake kan tazo ya nuna mata d’aki a saman bene,amma fafur tak’i ita k’okarinta ya bar ta ta futa da “yan uwanta domin sai yanzu ta fahimci abunda yake nufi ya kawota gurinshi, domin yayi mata cin mutumci sam baza ta iya zama inuwa d’aya dashi ba.

Cikin k’asaita ya d’ago kansa yana kallon tababar da sukeyi, tsakaninsu ya kalli Moddibo yace” Meya sa kafin ka kawota nan baka fad’ama ta ba,? nifa wannan hayaniyar da kuke ta ishe ni, babu dole in zata zauna ta zauna, kai da zaka taimake ta kaine kake wani rarrashin ta, in bata zauna wa ka kyaleta kawai malam taje duk inda zata je, dama ta saba”

Moddibo ya d’an harare shi,bai ce masa komai ba ya mayar da hankalinshi kanta yana rarrashi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button