GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Walidi dake tsaye bakin k’ofa yasa dariya yana nuna Lantana da hannu yace”Babu wata guba da yaci,guba d’aya itace bak’ar zuciyarsa ya kusa had’iyewa saboda tsabar bakin ciki, Hahahahahaha”
Walidi ya shek’e da dariya babu abunda ya dame shi.

TSANTSAR BUTULCI

              *_NA_*

BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

littafin me cike da sark’akiya gami da cin amana, kar Ku bari a baku labarin
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
。。。。。。。。。。。。。。。
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA

Zamani writers Association


We are her to educate motivate and entertain aur Reades


DIDEGATED
to
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

????78

Wata k’atuwar harara Lantana ta makawa Walidi bakinta na kumfa tace” Walidi kayi asara wallahi ban san inda kaje ka samo wannan b’akar zuciyar taka ba, yanzu ubanka na halin rai da rayuwa shine kake masa dariya”
ta karashe maganar tata tana rik’e hab’a cikin mamaki!

Wata mahaukaciyar dariyar Walidi ya kara saki yace” Kaji Lantana da wani magana kuma, hahahahaha, ai bak’ar zuciyarki na gado, amma naji kina zancan ina na gado bakar zuciya, to ai kece kika gada mana ita, hahaha”

Ya k’arashe maganar da mahauaciyar dariyarsa, barin gurin yayi yana fad’in ni kam nayi nawa guri domin yau ina cikin farin ciki da annushwa sanadin Balaraba yau na “yantu na zama cikkaken mutum ehe duk d’an bak’in ciki sai dai ya mutu!
fucewarsa yayi ya barsu da baki a sake

Sallau kuwa tuni ya sharb’e a gurin bakinsa ya karkace miyau na dulala, da kyar ya d’aga hannusa guda yana kiran Lantana ta matsa kusa dashi tana salati, baki a mugud’e yace” Lantana muna cikin wani yanayi wannan yarinya da mukai wa rikon sakainar kashi, Allah ya rufa mata asiri tana gidan sarki za’a d’aura mata aure da d’an wazirin gar….. kafin y k’arasa maganarsa Lantana ta fahimci abunda yake nufi, wani uban ashar! ta kurma tamkar ba tsohuwa ba fad’i take, “Me nake shirin ji ni Lantana, Balaraba d’iyar Tanko itace zatayi aure gidan sarauta ni nawa jikokin na nan a zaune lallai da sake! tafad’a wata irin kumfa na futa daga bakinta tsabar tashin hankalin da take ciki sam yanzu rashin lafiyar Sallau din bata gabanba, tunanin ta ya koma gurin ganin yaya zatayi ta futo da Balaraba daga wannan gida ko ta halin k’aka ne.

Shamsiyya ce ta futo daga uwar dakinsu daga ita sai daurin kirji nonuwanta sun cika sun tun batsa sai kace wata matar gida goshinta sai kyalli yake. Lantana ta dube ta sama da kasa tace”Dube ki cikkakiyar mace wacce ta amsa sunanta na mace kina zaune a gida kina tsotsor tsamiyya waccan mutsiyciyar yarinyar ta shallake ki, ai ko ta halin k’aka sai kin zauna gidan sarauta kema”
Lantana ta karashe maganar kmar zautacciya

Shamsiyya tace”Wai hayaniyar me nake ji ne tun dazu ina bacci”

Nan Lantana ta kwashe duk abunda yake faruwa ta fada mata”

Wani irin k’yashi da bakin ciki da hassada ne suka dura a zuciyar Shamsiyya ,rashin abunyi ne yasa ta fashewa da kuka wurjanjan! ta kalli inda mahaifiyarta take zaune kamar mutum mutumi,sai kace wata gunki tace”Uwa! kina raye a duniya haka tafaru damu k’askantacciya ta fimu komai kullum.kina cewa zaki sabautata mata rayuwa, gashinan kina zaune taje ta auri dan gidan sarauta mu muna zaune”
“Wayyo na shiga uku na lalace”!

Sosai Shamsiyya take kurma ihi!

Wata wawar ajiyar zuciya Uwa! ta sauke zuciyarta cike da bakin ciki gami da hassada, a halin da ake ciki yanzu batasan yadda zata fara ba,amma ya zama dole ta bazama k’auyuka gurin malamai da bokaye, domin samawa kanta mafuta lallai maganar hauwa ta tabbata inda suke cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka ido, a halin yanzu duk hankalin ya karkarta gurin ganin yaya za’ayi su sabauta Bawa Balaraba rayuwa ko ta mutu ko tai rai ko ta haukace cikin uku za ayi daya
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
。。。。。。。。。。。。。。。
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA

Zamani writers Association


We are her to educate motivate and entertain aur Reades


DIDEGATED
to
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

Tunanin ka kamanin ka d'an uwa ka tsare kanka, Allah yai maka albarka, sai ka gyara makomar ka

Wannan magana taka haka take fasihin mawak’i Musbahu m Ahamad

Allah kasa mu dace

????79

Da sauri Uwa!ta mik’e har zanin dake d’aure a jikinta yana k’okarin fad’uwa k’asa, tayi saurin rikeshi ta tsallake Sallau da kwance magashiyan a dandaryar k’asa,sai nishi yake,d’akinta ta afka kamar mahaukaciya,taje ta zura rigarta ta yafo mayafi ta futo, tana kallon Shamsiyya tace”Maza jeki sako riga mu baza ma,domin zama bai gan mu ba”

Da sauri Shamsiyya ta shiga dakin domin sako riga.

Lantana ta kalli Uwa!dake tsaye tana zazzage kud’i a cikin banki irin na gwangwani,tana lissafawa, tace”Uwa!yanzu, waye zai kula da Sallau gashi a kwance, kin san nima futa zanyi,yau na tashi bani da ko kwabo”

Hararta Uwa!tayi tace”Ai yau dole ki hak’ura da zuwa ko ina ki tsaya ki kula da d’anki daga nan har zuwa lokacin da zan dawo, domin kema zaman jiyya ya kama ki”

Lantana ta karyar da kai gwanin tausayi tace”To tunda kince haka shikkenan zan zauna, nasan dai zaki sammin abunci da zansa a baki na”

Uwa!tace”Idan Shamsiyya ta dawo daga talla ta ciri dari biyu tayi cefa ne,ina da sauran garin kwaki,sai ta tuk’a muku teba,daga nan har dare,in kun ga bamu dawo ba to ku rufe Gida kawai domin in na futa yanzu sai inda mai ya tsaya”

Lantana tace”To to shikkenan ai,Allah dai ya bada sa’a, a samo nasara”

Uwa!tace”Ameen, ai in kana da kudinka komai me sauk’i ne, dama Dan me nake neman kud’in duk dan “yayana,saboda haka yau ranar sune”

Tafad’a tana lissafa kudinta sun kai kusan dubu goma sha bakwai.haka ta zufa basu cikin wata karamar jaka, ta rataya ta a kafad’a Shamsiyya ta futo daga daki.

Suna futa tsakar gida suka ci karo da Sadiya matar Kawu Mamman tana tsaye bakin k’ofar ta duk abunda yake faruwa a kunnenta.

Kallonsu tayi tana me tausaya musu,ganin suna nema su jefa kansu cikin halaka,tace”Uwa!kiji tsoron Allah, ki tuna akwai ranar tsayuwa, me Balaraba tayi miki kike nema ki jefa rayuwarta cikin musiba,ki sani da shi sharri d’an aike ne, zuwa yake ya dawo saboda haka Ina mai tunasar dake cewar babu abunda yake d’orewa a duniyar nan sai ikon Allah,duk sharrin ku gami da hassadar Ku a kan Balaraba,dukanin abunda Allah ya hukunta, a kanta na alkairi sai ya faru, babu makawa, sai dai Ku mutu da b’akin cik…… “Ke Sadiya rufe min baki munafuka”
Uwa!ta fad’a a fusace!ta cigaba da cewa” Wato ke dan baki haihu ba,shine kike min bak’in ciki, a dukanin lamarina da “yayana, to bari kiji, yanzu na fara bin malamai akan ” yayana, sai ki mutu,baki san bin malamai ma sai me kud’i ba, aikin banza kawai”

Shamsiyya ta rik’e hannun Uwa!tana fad’in “Don Allah k’yaleta munafuka ce zo mu tafi tana b’ata mana lokaci”

Futa sukayi suna zagin Sadiya, gami da kwashe mata albarka.

Ita kuwa Sadiya bayan futarsu girgiza kai tayi kawai ta shige d’akinta tana nema musu shiriyar Allah.

Wannan kenan


Sosai Sarki!ya sakarwa Halisa fuska sukaiyi hira ta fahimta, abunda yasa ya saki jiki da ita,shine ya fad’a mata maganar auransa da Balaraba yaga ta Saki jikinta, bata nuna kishi ba, yaji dadin hakan sosai,kuma suna tare Azima ta kirashi a Waya, nan ma bata nuna b’acin ranta ba, ta burgeshi sosai, har wajan magariba suna tare da juna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button