GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da ita da du Halisa Madabo ma taje,, Sarki kuwa dashi akayi jana’izar Sallau, unguwar ta d’auka wanda ma bai yi niyyar zama gurin mutuwar ba dalilin zaman Sarki! A gurin ya zauna,, ya sa aka kafa rumfuna sosai mutane suka zo suna kwasar girgi harda wadanda suka futa kasuwa, sai su dawo domin su kwashi abuncin gidan mutuwa, kullum sai sun zo har a kayi sadakar uku,, Balaraba suka dawo gida cikin jamami,, tayi mamaki da har aka share zaman makoki bata ga Iro da Mabaruka ba, har dai ta gaza hakuri ta tambayi Iya ina suke, sai tace”Mabaruka dai tafi sati hudu rabon ta da gida, shi ko Iro tun kafin ki bar gidanan aka neme shi aka rasa, tace”Shamsiyya fa”? Iya ta girgiza kai tana goge kwalla tace”Tana cikin daki ta d’auko abun kunya shiyasa take buyarwa jama’a” Balaraba ta dunga share hawaye tana tausayawa rayuwar su,, Shamsiyya kuwa tana jin ance ga Balaraba tazo zata dunga lekowa tana taga tana kallonta tana fad’in ina ma itace.



Duk abubuwan da Mak’asudu ya ce a nemo sun nemo kuma sun aiwatar da aikin kamar yarda yace d’in abunda ya rage wa Waziri shine zuwa bakin ruwa ya yanka rago shima ya sa d’amba gobe da Asuba zai futo domin an samo ragon irin wanda Mak’asudu ya buk’ata…

Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,, jiki a sanyaye take yin komai, k’arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k’aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d’inkin Riga da sket ne,, tayi fuskarta fayau,, ko kwalli babu sai mai leb’e da ta goga,, a nutse ta dunga d’ibar kayan abuncin tana kaiwa part d’insa,, su Amina da Hadiza bayinta sukayi-sukayi ta barsu su d’aukar mata tak’i tace”su barshi itama ladan take so, sai suka hak’ura suka k’yaleta ,, lokacin yana sama ta gama shige da fucen ta, ta koma part d’inta sai bayan tayi Sallahr magariba ne, sannan ta kimtsa, da niyar komawa part din nasa.

Da shirin zuwa masalaci ya sauko hankalin sa bai kai kan daining ba, sai Mai dafa masa abunci fa ya gani a tsaye tsakiyar falo ya sunkuyar dakai kasa, gyaran murya yayi da sauri ya dago yana masa barka da sakkowa, Yace”Kana tsaye gashi ana shirya-shiryen tayar da sallah” Yace”Allah ya taimaka ke Nazo zan jera abunci na ga an jera wani nace Allah yasa ba laifi nayi ba”
Kallon daining teble din yayi yaga wasu had’addan kuloli ba Wanda aka saba zuba masa abunci ba,, girgiza kai yayi kawai, yasan aikin Gimbiya ne, yana k’okarin tafiya yace”Yau an hutar sheka, gobe ma kar kayi gudun asara ka futar muku da Wanda ka girka” Yana gama maganar ya futa,, Shi kuma ya koma kicin, cikin zuciyarsa take cewa amma wannan matar tasa ta tarbiyantu ba kamar sauran ba, Allah ya kyauta.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????107

Sai bayan sallahr Isha’i ya shigo, zama yayi a falo da carbi a hannunsa yana ja,, a hankali ya dunga jin wani sanyayyen k’amshi na ziyartar hancin sa, d’aga kansa yayi yana kallon inda yake jin motsi, Balaraba ce take saukowa daga matattakala cikin nutsuwa, a sirance ya sauke ajiyar zuciya ya su kunyar da kansa wani Abu na tsunkullin sa,, ta k’arasa daining cikin nutsuwa ta gyara komai ta tako a hankali ta zauna kujerar dake kallon sa, kansa na k’asa bai dago ba, a hankali tace”Barka da dare” d’ago kansa yayi yana kallon ta, minti biyu yace”Barka kin wuni lafiya”? “Lafiya Lou ta fada’a tana wasa da hannunta,, yace” Ya k’arin hakuri kuma” ? “Alhamdullahi” Shiri falon yayi sak’e-sak’e take a zuciyarta, shi kuma yana k’okarin ya cika carbin sa,, sai da ya kammala sannan ya aje ya d’auki wayar sa, numbar Halisa ya kira tans d’auka yace”Ki futo muci abunci ” kashewa yayi ba tare da ya saurari abunda zata CE,ba, numbar Azima yake nema, sai gata ta shigo cikin uban kwalliya ta k’ananun kaya wanda suka d’ame ta,, b’ata fuska yayi lokacin da yayi arba da ita, kusa dashi ta zauna tana gaishe shi cikin wani irin salo,, a dakile ya amsa, yace”Wannan wane irin iskanci ne zaki futo da wannan kayan na jikin ki”? Azima ta sunkuyar da kai tana fad’in ‘Yallab’ai me ye laifin su” A fusace! Yace”Ba duguwar magana na nema ba,, magana ta farko ta k’arshe kar ki sake futowa da irin wannan kayan in zaki saka kayan ki ki saka Ke ka dai a daki ba sai kin nunawa jama’a ba, gida cike da mutane ki futo min da wannan shashancin” Ganin ransa ya b’aci yasa ta fara bashi hakuri , ko sauraron ta baiyi ba ya mike ya nufi gurin cin abunci ransa in yayi dubu ya baci”! Balaraba kuwa taji dadin abunda yayi wa Azima ta lura tayi shigar ne Dan Taja hankalin sa, a randa ba girkin ta ba, dariya kawai take mata Cikin zuciyarta tace”Wallahi wani lokacin mutumin nan na burge ni da halinsa baudadden mutum ne!

Gyaran murya yayi Balaraba ta mike da sauri kar ta samu rabon ta,, Azima ma ta mike jiki a sanyaye,zama tayi, daya daga cikin kujera ita kuma ta fara zubawa kowa nashi cikin nutsuwa, Halisa tayi sallama ta shigo,,, itama ansha kwalliya kamar masu zuwa gasar fidda kyau!! Gwara ita material ne, a jikinta dinkin riga da sket kusan irin na Balaraba kala ce kawai ta banbanta,, gaishe shi tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,, sama-sama suka gaisa da junansu ko wacce na danne Kishi a zuciyarta. Balaraba ta zubawa kowa nashi ta zauna ta fara cin nata cikin nutsuwa.

Sarki! Yaji dad’in girkin Balaraba sosai ya bude ciki ya ci ya k’oshi ya yagi tissue ya goge bakin sa,, da kuzari a jikinsa ya mike daga gurin, falo ya koma ya zauna,, to suma dai su Halisa sunji dadin girkin shiyasa babu wacce tayi k’orafi suka cinye plate din tass ko wacce ta tashi tana goge bakinta,, Balaraba ta gyara gurin tsaff!! Ta isa in da suke,, k’asa-k’asa yake kallon ta ganin tana k’okarin futa,, yace”Ina zakiji kuma? Duk gashi muna zaune da juna” A takure take jin jikinta kasan cewar tana cikin halin rashin tsarki,, wannan motsa jikinta da tayi Duk pad din ta ta jik’e haka take a rana sai ta sanya sau biyar,, tace”Yanzu zan dawo zan Dan watsa ruwa ne”” Nan ma akwai toilet kin shigo kenan ki dawo ki zauna” wannan halin nasa yana bata haushi wallahi, to in ta dawo ta zauna yana da pad din da zai bata oho masa,,, zama tayi kujerar dake daf da bakin kofa ranta a bace, duk ya lura da yanayin da take ciki,, Azima sai watsa mata d’an iskan kallo take,, Ita ko Halisa sai hira take masa yana biye mata,, goma shaura, sukayi masa sallama ko wacce ta wuce part d’inta, falon yayi shiru da shi sai ita mik’ewa yayi ya nufo inda take zaune,, Balaraba ta sunkuyar da kanta tana jiran taga me zaiyi,, kulle k’ofar yayi ya cire key din,,, ta kalle shi bakin ta na rawa tace”imm… Ina da Uziri a gurina fa,, yanzu zan futane in je in dawo naga kuma ka kulle kofar” Tsayuwa yayi a kanta yayi mata rumfa! Cikin wani irin voice yace”Me zaki je kiyi? Uhumm kin ce wanka nan babu toilet ne”? Girgiza kai tayi yace”To kin gani, tashi muje ki gyara min shimfid’a ta”” ta d’ago dararan daran idonta tana kallonsa,, lallai akwai rigima kenan mutuk’ar ya san halin da take ciki, yaya za’ayi ta fada masa,,, hannunta ya kama ya mikar da ita tsaye,, zura hannusa yayi ya rungumo k’ugunta suka fara tafiya, a haka suka dunga hawa mattatakala duk rabin jikinsa na jikinta,, lokaci guda ya soma neman nutsuwar sa,,, zama tayi gefen gado ya shiga toilet ya futo daure da alwala yace”Ki shiga kiyi wankan sai ki dauro alwala kizo muyi nafila” babu musu ta mike ta shiga toilet din,, Wanka tayi sosai,, ta sanya towol ta goge jikinta ta maida kayan jikin ta,, tana futowa taga ya shimfid’a dadduma yana tsaye yana jiran ta,, hijab ya mik’a mata, ta karb’a amma bata sanya ba,, ik’ama yake so ya tayar ya kalle ta yana fad’in”Ki sanya mana” A nutse tace”Bani da tsark” Yaji wani irin fad’uwar gaba, amma dake Namijin duniya ne,, sai ya maze Dan kar ta gane,, yayi minti biyu yana nazarin ta daga bisani ya tada sallahar shi,, zama tayi gefan gado jikinta a sanyaye , Ya dade kan dadduma yana addu’a har ta fara gyangyad’i,, ya mike a nutse ya kashe wutan dakin,, bed din ya nufa Balaraba tayi tsuro tana kallon inuwar sa,, sai da yw zauna sannan ya cire jallabiyar da take jikinsa,, babu zato taji ya jawo ta jikinsa, gabanta ya dunga fad’uwa duf!!duf!! Zif din yake k’okarin zugewa tayi saurin dafe hannusa,, kansa ya zura tsakanin wuyanta yana sakin ajiyar zuciya daki-daki,, k’okarin hanashi take, amma sai da yayi nasarar zuge mata zuf din ya cire rigar ya jefar kwantar da ita yayi k’asan shi yayi mata rumfa, Balaraba sai motsi take da bakinta taka cewa komai duk inda ya kai hannunsa sai ta kai nata duk a k’okarin ta na hana shi abunda yakeyi ya ta kasa,, sai ma jikinta da yayi la’asar sakamakon uban soyayyan da yake zuba mata,, Balaraba taji kamar ba a duniya take ba,, ta shagala Wanda ba san ma yayi nasarar cire mata brziyya ba,, aikuwa ta gigice amma yanai mata wani salo tuni ta bada kai bori ya hau suka hau soyayyar su irin ta ma’aurata,, Sarki! Ya sha mutukar wahala lafin ya samu nutsuwa,, Balaraba kam jin ta take a sama, ta manta a wace duniyar take, ita dashi sai sauke nuffashi suke,,,,, wani irin kullewa mararsa take,, shi kansa yasan ba duka ya zubar da abun ba, yanzu shine damuwar sa, zai iya shiga mugun hali, mutukar bai samu yayi sex ba, domin shine katt! Shine za samu sukuni,, a galabaice ya kira sunanta, ta amsa murya na rawa yace”Ki yarje min na je gurin “yar Uwar ki na biya buk’ata ta, ina Cikin wani hali” Sosai ta tausaya masa,, cikin raunin murya tace”Babu damuwa, ai dama amfaninmu kenan, na yarje maka kaje kawai” mik’ewa yayi yana zura jallabiyar sa,, Albarka kawai yake sa mata,,, sauka yayi daga bed din ya d’auki key zai futa, ta kira sunansa juyo wa yayi yace”Menene uhumm? Kiyi hakuri Yanzu zan dawo”‘ shiru tayi haka kawai taji kwallah na k’okarin zubo mata,, ya fuce da sauri,, Azima tafi Halisa dauriya, saboda haka shashen ta ya nufa Cikin duhun dare, dam ma akwai hasken futulu a wasu guraran,, Azima na zaune a gefen gado ta zabga uban tagumi sai tunani take kana kallonta kasan akwai abunda yake damunta,, taji ana bugu tana k’okarin tashi taji karar wayarta,, tana dubawa taga Sarki! Ne hannu na rawa ta d’auka, yace”Bude min kofa” jiki na rawa ta je ta bud’e masa ya shigo ta mayar da kofar ta rufe,, kai tsaye bed din ta ya nufa,, ta bishi a baya,, tana shiga ta ganshi yana k’okarin cire Riga, tace”Lafiya Yallab’ai “? Kwanciya yayi bed din ta yace” Zo” Azima ta gane me ke da akwai,, zuciyar tace mata Allah ya kawo miki shi har dakin ki,, da sauri ta nufi friji ta d’auko Lemo mai sanyi ta k’araso kusa dashi,, tace”Yallab’ai tashi ka fara shan Lemo nasan ranka a b’ace yake”” sama-sama yake jinta ya mike ya karb’i lemon dake hannuta ta bud’e masa ya shanye Tass! Ta karb’i robar ta aje,, kashe futular tayi ta rungume shi,,, cikin mawuyacin hali ya biya ma kanshi buk’ata,, yana gamawa yaji wata irin muguwar kasala ta rufe shi,, da k’yar ya koma part d’insa, Balaraba na zaune ta rafka tagumi jiran dawowar sa kawai take, ya shigo ta bishi da kallo ya shigowa ya kwanta babu abunda yace mata,, kusa dashi taje ta kwanta gabanta na fad’uwa,,, da k’yar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai! Asubah ya farka tare!dashi, ya d’aga kafa zai sauka k’afar tak’i d’aguwa yayi-yayi taki motsi sai wani yammmmmmmmm!!! Take masa.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button