GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shahid ya kalleshi yana fad’in “Kaine Waliyyin ta”

Kamar wani k’aramin yaro Sallau ya d’aga kansa, yana sauraron abunda zai biyo baya

Shahid yace”Ga kaya can daga gurin Mama Fulani tace akawo muku a matsayin Ku na iyayen Balaraba mata ga Sarki! Me jiran gado wato Sarki! Almansur insha Allahu gobe za’a d’aura mata aure dashi”

Ihu!! Shamsiyya ta kurma ta afko cikin dakin tana fad’in “K’arya kukeyi Wallahi baku isa, ni za’a yaudara da muna furci billahillazi bazan lamunta, wannan kayan nawa ne, kuma gobe dani za’a d’aura auran ba da wancan shegiyar ba”

Cikin ihu da tashin hankali Shamsiyya take maganganun sai dara take tana tsalle, Uwa! Ta dunga zabga zagi tana habaice habaice

Sallau da Lantana kuwa Shiru sukayi suna mamakin wannan al’amari

Ganin sun gama abunda ya kawo su yasa suka mike cike da mamakin dabi’ar mutanan gidan tsallake Sallau sukayi Wanda yayi rashe-rashe a bakin Kofa suka futa cikin tashin hankali domin Sam Shatima baya San hayaniya da yawa yanzu kansa zai fara ciwo.

Ganin sun futa yasa Lantana mik’ewa da sauri ta bi bayan su, sai kuma ta dawo da sauri ta koma cikin d’akinta ta d’auko wani Abu tana boyewa cikin hijab, rad’a tayiwa Uwa a kunneta ta futa a sukwane!

Lokacin Buba Direba har ya kunna mota ta karasu gurin tamkar sabuwar mahaukaciya tana fad’in Ku tsaya kutsaya”

Shahid yace da Buba ya tsaya Lantana ta iso gurin tana haki!! Tace”Inaso in biku gidan sarautar domin a gudanar da harkokin buki dani, a matsayina kamar Balaraba.

Shatima yace”Bud’e mata Kofa ta shigo, aikuwa Buba ya bud’e kofar mota Lantana ta shiga ta zauna tana k’ara damk’e abun da yake hannuta.
[9/8, 9:34 PM] Akwai Citta????????: **



Wata irin fad’uwar gaba taji lokacin da taji abunda yake cewa, kar dai wannan mutumin zarginta yake.

Take fad’ar haka cikin zuciyarta.

Tamkar wacce aka aikowa da mala’ikan d’aukar rai! Haka ta kicin-kicin da fuskarta, cikin yanayi irin na b’acin rai tace”Wannan ba hurumin ka ba, cewar maza nawa na kula ko nayi mu’amula dasu lokacin ina sana’ata, kai bari kaji wani abu da baka sani ba, yau kasan dashi, na Dade da sanin dama kanai min kallon “yar tasha me sai da abunci cikin kasuwa, babu irin maganganun da baka fad’uwa Moddibo ba,kan kar ya aure ni, kushe da hassada basa hana gamji toho nida Moddibo soyyaya ce ta tsakani da Allah, ina mutukar alfahari da sana’ata,kuma duk inda na shiga na futa naji ana zagin masu irin Sana’a ta sai inda karfina ya tsaya, saboda haka tun kafin magana tayi nisa mutukar kasan da wani k’uli a ranka a game da aure na, sai ka janye kawai babu Lallai babu dole a ciki”
Ta k’arashe maganar tana sauke ajiyar zuciya.

Fuzgo hannuta yayi tafad’a kansa, ya rungume ta tsam! K’irjinta ya dunga fat-fat! Shima nashi haka, muryar shi a tsark’e yace”Ni kike k’okarin zagi ko saboda kawai na tambaya ki, abunda nake da hakki akansa”

Da sauri ta fuzge jikinta tanai masa kallo na wani irin mutum mai baud’adan ra’ayi yasan yayi Abu ya nuna bai yi ba, babban abunda yake bata haushi dashi shine son ya tab’a mata jikinta.

“Sama-sama tace” Babu maganar zargi a magana ta,ai gaskiya ce tun yanzu naga take-taken ka, kayi hakuri idan na b’ata maka rai,da kalaimai na”

Tana gama maganar ta shige d’akin da suke kwana.

Kallonta yake babu k’iftawa har sai da ta shige dakin sannan ya d’auke kansa, yana sauke wata irin zazzafar ajiyar zuciya, kwata-kwata a “yan kwana kin nan, yana yawan jinta a cikin zuciyarsa, duk sanda ya tuna da cewar tayi mu’amula da maza ta shiga cikin kasuwa ta saida abunci,sai yaji wata irin kibiyar kishi ta soke, ranar sai ya yini yana kwance duk ransa a b’ace! Yana kishinta sosai da sosai.
Kasa daurewa yayi yasa yayi mata maganar.




Lantana na bayan mota duk tayi tsuru-tsuru sai zare ido take, burinta kawai ta isa gidan ta ganta gata ga Balaraba sai ta fara gudanar da aikinta.

????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????93

Kai tsaye shashen Mama Fulani suka nufa,, bayan Buba yayi parking d’in mota suka futo cikin nutsuwa, Buba ya bud’ewa Lantana k’ofa ta futo daga cikin motar sai zare ido takeyi ganin wasu irin mutane manya-manya a shashen Mama Suna kaiwa suna kawowa kuwanne jikinsa sanye da kaya jajaye da k’aton ta wani, gefanta ya kalla taga wani tsaye hannusa rik’e da k’atuwar bulala sai zare ido yake ga idanunsa sunji kwalli rabad’au, saurin d’auke kanta tayi tana k’ara damke abunda yake hannunta.

Ganin suna ta zubewa k’asa suna gaidasu Shatima ne yasa ta shiga taitayinta, ta dunga bunsu a baya simi-simi har suka shiga falon a tare.

Lantana ta tsorata da ganin irin had’uwar falon Mama Fulani ko ina ta kalla sai taga kalarshi daban, ga kayan alatu na jin dad’i da more ta yuwa, wani irin mugun kamshi me dad’i yana shiga hancin ta.

Tun daga bakin Kofa ta zube tana gaida Mama.

Cikin mamaki Mama Fulani tace”Bisimilah mana ki shigo daga ciki sai mu gaisa sosai”

Da k’yar Lantana ta mike ta isa kusa da Mama Fulani ta zauna a k’asa sai washe baki take.
Tana fad’in “Ranki shi Dade ashe ina da rabon ganin ki a duniyar nan, ashe jinina zai had’u da jininku,gaskiya nagode Allah nagode Muhammadu rasililahi”

Mama tayi murmushi kawai tana kallonsu Shahid nan yayi mata bayanin Lantana

Cike da farin ciki ta kalli Lantana tana fad’in “Gaskiya naji dad’in zuwanki sosai,dama nace aje a sanar daku halin da ake ciki,Gobe insha Allahu bayan d’aurin aure zan tura a d’auko sauran mutanan gida suma suzo ayi hidimar buki dasu”

“Lantana tace” Ai naji dad’in wannan abu ranki ya Dade nace Ashe da rabonmu muma zamuci arziki mu bar shi inda yake, haihuwa tayi mana rana”

Murmushi Mama tayi batace komai ba.

Su Shahid suka mike. Inda Shatima yake tambayar Sarki! Mama tace”Ya koma Shashen sa. Sallama sukai mata suka wuce Shashen Sarki!

Lantana ta dunga b’arin jiki sai zuba take tanaiwa Mama labari,tace”Ina angon namu yake ne yazo ya zab’a ko ni ko ita”

Mama bata iya surutu ba saboda ba d’abi’arta b’ace,gashi bata San wulakanta mutum sai ta dunga biyewa Lantana kawai domin karrama ta.

Jakadiya Shafa’atu ta shigo suka gaisa da Lantana, nan Mama take sanar da ita cewar kakar Balaraba CE,Jakadiya ta kara gaida Lantana cikin girmamawa, Mama tace, taje ta kira Balaraba dasu Sadiya su gaisa da kakarsu sannan Balaraba ta bata abunci, Sadiya da Usuman ne a gaba kafun Balaraba, da sauri suka ja tunga suka tsaya ganin Lantana a gurfane gaban Mama sai surutu take sai kace wata tsuhuwar redio, Sadiya ta juya da sauri zata koma suka ci karo da Balaraba tayi saurib tare ta tana tambayar ta menene”?

Bakinta na rawa tace”Yayarmu Lantance”

Da sauri ta kalli inda Sadiyar take nuna mata, Lantana ce, kuwa hankalinta na kan Mama basu ga futowar su ba, fad’uwar gaba taji, tana mamakin me ya kawo Lantana gidanan,, wata zuciyar tace mata kika sani ko Mama ce tasa aka d’auko ta.
Da kuzari a jikinta ta nufi inda suke, Binta sukayi a baya suna cike da tsoran abunda zai faru Usuman addu’a kawai yake a cikin zuciyarsa Allah yasa Lantana kar ta gudu dasu shikam yaji dad’in zaman gidan nan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button