GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama jikinta yayi sanyi sosai da sosai tace.” Dama ni kaina banyi na’am da wannan hadin ba wallahi oh! Mugu bashi da kama yanzu Azima itace ta bawa yarona guba yaci domin ya nakasa.”? Kattime tace.” Kina mamakin wannan duniyar wallahi.”

Mama tace.” Yanzu zan sanya ayi min kiran su ki zauna a gaban ki za’ayi komai, Jakadiya ta kira ta umarce ta ta kira mata Azima da Halisa BALARABA

Wayar ta ta d’auka ta kira uban gayyar, suna tare da me girma governor suna shirye-shuiyen yanda za’a gudanar da nadin sarauta,domin an tsai da rana jama’azuwa ,Yaga kiran Mama a nutse ya d’auka tace.” Kazo yanzu shashena.” “Insha Allahu ganin zuwa.” Ya fada yana kashe wayar.

Sallama sukayi da governor suka futo tare me girma ya shiga mota tare da mutanansa shi kuma ya. Nufi shashen Maman shi tare da jama’ar sa, duk suna zaune suna jiran isowarsa yayi sallama ya shiga duk suka amsa, matansa na rige-rigen gaishe ya amsa mu a nutse ya zauna, yana gaida Maman shi tare da Hajiya Kattime, Fulani tace.” Kattime yi musu bayani da bakin ki.” Nan Kattime ta fara fada masa duk abunda ya faru tun daga farko har k’arshe da manufar Waziri akan auransa da Azima. Nan take Sarki! Ya tuno da ranar da ya shiga gurin Azima da daddare har yayi Tara da ita tunda lokacin nan ya tashi da wannan ciwo, Azima tayi tsuru-tsuru tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta tayi da tasani yagi cikin kwando shikkenan yanzu tasan karshen zamanta dashi ya kare ganin yadda ransa yayi mugun b’aci, shiru farlo na minti biyar yayi gyaran murya yana goge gumn da ke tsatsafo masa, yace.” Mama ki gafarce ni, da abunda zan aikata yanzu hak’ika zama da Azima babbar musiba ce saboda haka na sawwake mata igiya guda taje in ta samu miji tayi aure.” Yana gama fadin haka ya mike ya futa zuciyarsa babu dad’i.

Babu Wanda yace komai cikinsu,Azima ta dunga kuka tana rokan Mama ta sanya shi ya janye sakin Mama tayi shiru da rarrafe taje ta rike k’afafun Halisa tana rokonta Halisa ta fuzge kafarta tana maka mata harara tace.” Wallahi na tsane ki Azima muguwar azzalima kawai.” Cikin kuka Takarasa kusa da Balaraba tana rokonta wai tabawa Sarki hakuri Balaraba tayi shiru kawai tana Mamakin halin Dan Adam.
Fadawan dake waje mama ta umarta tace su futa da Azima kuma su tsaya kanta ta had’a duk wani ko matsanta ta kama gabanta. Aikuwa haka akayi aka tasa Azima a gaba har garin su.


????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????‍♀????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????‍♀

Rana bata karya

Yau juma’a uku ga watan uku, yau aka gudanar da shagalin nadin sarauta.

Wannan nad’i ya samu halartar dubban mutane kama daga shugabanin kasa she,governor ni shahararun malamai da limamai da shahararun ‘yan kasuwa duk sun samu damar halarta nad’in sarautar Sarki! Almansur YARO me dattako me halin manya me nagarta da sanin abunda takeyi kowa na masa fatan alkari tare da jagoranci me cikin adalci, lokacin da ake gudanar da wannan nad’i Waziri na kwance yana zurarar da hawaye duk an d’ad’e an barshi shi kadai kuka yake tukuro gami da nadamar abunda ya aikata,, labari ya riske cewar ga Almansur can an mik’a masa sandar mulki, ihu!!! Ya kurma yana buga kansa a bango nan take ya futa daga hayyacinsa .

Balaraba takasa nutsuwa sai shige da fuce take da hidima da mutane duk ‘yan gidansu sunzo tare da wasu ‘yan unguwar su, Wanda suke mata wani irin ladabi da biyayya tamkar zasuyi mata sujjada, ita kam sam bata son abunda suke mata. Lantana ce me sallamar baki da taga Balaraba ta motsa zata hanata wai saboda cikin jikinta, su Uwa da Iyalinta na gefe guda gwanin tausayi, Mabaruka kadai aka bari a gida saboda babu k’afafu, Shamsiyya kuwa danta ya girma har yana rarrafe, Walidi dashi ake komai yana can waje cikin jama’a yana shige da fuce.

Har magariba gidan sarautar babu masaka tsinke, shi kanshi me Martabar bai samu damat shigowa gida ba tun safe da ya futa sai bayan sallahr Isha’i lokacin jama’a sunyi sanyi, ya nufi part d’insa tare da dakarunsa.

Balaraba da Halisa sun shirya masa guri sosai suna tsaye bakin kofar shigowa sun ci uwar kwalliya ba’a magana, yana shigowa suka fara watsa masa wani abu me kyalkyali yana takawa wani. A jikinsa, murmushi yayi ya rungumo su gefan kafad’unsa yana manna musu kisses cike da so da kauna yace.” Allah yayi muku albarka.”suka amsa da amin. Sama suka nufa suna rungume a jikinsa.


Kulu me dakin kudu kuwa tun da taji labarin abunda ya faru da Waziri ta tattara inata-inata ta gudu domin tana jin tsoron tunowar asirinta, ba karamar sata ta labta ba, Sarki! Da ya samu labari yaji ciwon abun sosai saboda ‘yan uwansa su Shukura dole duk inda suka shiga ya sanya a nemo su.


Kwana biyu kura ta lafa me Martaba ya fara zama a fada cikin aminci yana gudanar da mulki cikin adalci da yanda Allah yace aikuwa jama’ar gari suka fara kiransa da “D’an karaminsu babansu, Babansu kuma a cikin sarakai mulki azo a koya a gurin shi, Sarki! Ya zama mutum na matasa na tsofaffi na dattijai na yara kanana.


Balaraba ciki ya tsufa sosai ya shiga wata tara yayin da Halisa ma NATA yake da wata shida,me Martaba kullum cikin sarauraren haihuwar ta yake tayi kib’a sosai ga wani girma da cikin yayi shiyasa sai ya shiga gida sau uku a rana har India lya futa sallah baya komawa fada sai ya koma ya ga jikin nata.


Ranar litinin misalin k’arfe goma da rabi na safe Allah y sauke ta lafiya inda ta haifi ‘yaya uku rigis duk maza, cikin hukuncin Ubangiji haihuwa tazo mata cikin sauk’i ba tare da tasha wahala me tsanani ba, Ubangiji kenan me bayarwa da hanawa Allah ya azurta me Martaba da ‘yaya uku lokaci guda, gida ya d’auka gari ya d’auka tunda ga ranar aka fara shagali babu kama hannun YARO,Mama kullum a tafe take gurin ‘yayanku kullum cikin yi musu hidima take, shi kam me Martaba ai da k’yar yanzu yake zaman fada, kullum yana nanike da baby’s din sa tare da Queen d’inshi da yake jin yanzu ta zame masa wani b’angare na RAYUWAR sa, ranar suna yara suka ci sunan Abdullahi Abdulraham Abudr jabbar, shagali da aka gudanar har sai da na wajan gari ya San dashi domin gidanan tv ne suka dinga d’auka suna watsa shi duniya me jego da ‘yayanta tare da me girma Me martaba sunga kauna da soyayyar mutan gari,. Iya ce ta zauna mata har sai da akayi arba’in, sannan aka had’a mata shatara ta arziki aka kaita har gida, tare dasu Sadiya da Usuman zasuje Hutu kafin a koma makaranta. Tofaaa! Yallab’ai fa na ganin ta fara sallah ya bud’e huta domin can gurin Halisa babu bayani cikinta ya tsufa gashi daman can raguwa ce bata d’aukar laluransa, Balaraba ta karbe shi hannu biyu ta fara shayar dashi madara da Zuma irin na aure, sai ga Yallab’ai yana kin zuwa fada, kullum yana kan aiki ????Balaraba tace batasan wannan ba, sai da yaga ranta ya b’aci sannan ya cigaba da zaman fada, hakan ma tana raya masa zai gudu ya biya buktarsa sannan yayi Wanka ya koma, aikuwa ciki ya samu babu shiri.

Watansu Abdulrrahan uku Halisa ta haihu ‘yan ta gwaye duk mata, Wai-wai murna gurin Yallab’ai ya samu ‘yan mata masu kama dashi, ranar suna an dagargaji buki babs suka ci sunansu Hasana da husaina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button