GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ta cigaba da cewa.” Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba.” Balaraba tace.” Kai angode sosai wallahi ai Mama alk’urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi.” Mama tace.” Haka maganar ki take Balaraba.” Su Shahid ne suka k’araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace.” Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya.” Shahid yace.” Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k’alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake.” Cikin farin ciki Mama tace.” Nasan zata aikata fiye da haka, k’okarin tura while chair d’in yake, da sauri Shatima yace.” Kabari mana inzo.” Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k’araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad’in”Da ka bari an turaka.” “Akan me zan bari hannuna aikin me yake.” Yafad’a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad’in” Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba.”
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA

ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.

DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????114

Shiru yayi masa har suka k’arasa kusa da Mama,ya fara k’okarin saukowa Mama tace.” A’a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k’ara lafiya.” Suka amsa da “Ameen” Cikin kauna irin ta d’a da uwarsa yace.” Mama kin tashi lafiya.”? Tace.”Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad’i kuma na godewa Balaraba.” Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace.” Ina fatan ka karya ko.”? Balaraba tace.” Ga kayan karin can kan daining.” ” To maza je ki d’auko masa in ga yaci a gabana.” Kallon ta yayi yace.” Mama sai kace wani k’aramin yaro.” Murmushi tayi tace.” K’aramin Yaro kake a gurina.” Shahid yace.” Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had’a tea me kauri tace.”fara bashi ya d’umama cikinsa.” Balaraba ta mik’a masa kofin tae sai yak’i karb’a Mama tace.” Ki cika ladanki mana.” Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d’in, a hankali ya bud’e bakinsa ya fara kurb’ar tea d’in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k’arni, a hankali yace.” Ki aje Wannan ki had’a min bak’i.” Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had’a masa wani,hannu ya mik’a ya d’auki cake guda d’aya ya fara ci, sosai yayi masa dad’i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d’in yadda zai fi masa dad’i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak’i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d’in, sai da ya ci guda shida sannan ya d’aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k’okarin yagowa, ta ya ciro masa mik’ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had’a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had’u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k’wari suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b’oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa Balaraba a ciki kamar ba itace ta bangaje ta d’azu ba, ita ko Halisa sai shan kunu take tana hira da Mama kawai, cikin wannan hali me girma governor ya iso, suka gaisa da Mama cikin girmamawa, Halisa ta kalli Mama k’asa-k’asa tace.” Mama ina gani tafiyar nan ayi ta dani domin yau girki na ne, kinga sai in kula dashi” Mama tace.”aikuwa kin kawo shawara me kyau dama ya kamata a d’auki daya daga cikinku a tafi da ita, to amma kinga Balaraba bata futa daga lokacin ta ba, ina ganin da ita za’a tafi, in yaso in ya dawo sai ya sauka a dakin ki, kin gane ko”?

Halisa ta b’ata fuska bata ce komai. Me girma governor yaji dadin ganin jikin shi yayi kyau, sosai ba tare da wani b’ata lokaci ba, suka mik’e domin tafiya Shahid shine yake tura shi har suka futa harabar gidan jama’a a tsatstsaye Suna sauraron futuwarsu kowa na addu’a da fatan alkairi, tare da samun lafiya. Waziri na fada zaune shi da mutanan sa labari ya riske shi cewa gashi can an futo da Sarki! Zasu tafi Saudi’a sai ya kece da dariya yana fadin “Duk inda zasuje suje su dawo shida ya taka doran kasa da k’afafunshi to sai dai idan lahira yaje” mutanan sa suka ce “Wannan haka yake,takawar ka lafiya gyara kintsi dai!!!!!! Wani mugun dad’i ya rufe shi, jin yadda suke faman zuba masa kirari,abunda yake mutuwar so kenan a rayuwarsa.

Azima da Halisa, na tsaye sai gani sukayi kawai Mama ta rik’o hannun Balaraba ta zaunar da ita bayan mota kusa da Sarki! Ta maida kofa ta rufe, fad’i take.” Ubangiji Allah ya bada nasara a rayuwa Yarona ka dawo da k’afafun ka.’ Sarki! Yayi mamakin abunda Mama tayi,sam ba son daya daga cikinsu ta bishi saboda ya San rigima ce, yana kallon b’acin rai da zallahr kishi a idon Halisa, amma bai san manufar Mamanshi ba, Wambai da Galadima da Liman suka shiga motar su,suna dagawa Mama hannu, Shahid da Shatima motar me girma governor suka shiga, shi kuma tashi daga shi sai Balaraba sai direba, d’ayan bayan d’aya suka futa daga gidan da niyyar zuwa eirport. Addu’a sosai Mama takeyi, har suka futa, ta dawo da hankalinta Kansu Halisa kamar su d’aura hannu aka don bakin ciki, nan ta basu umarnin ko wacce ta koma shashen ta.


Bayan awa biyu da tafiyar su.

B’angaran Waziri Zayyanu, Khalifa ne da Ansar, Suna zaune a falo suna ciye-ciye sai dariya sukeyi da alama suna jin dad’i saboda yanda Babansu ya sakar musu kudi Sosai saboda duk cikin ‘yayansa yafi son su, sune zai ce suyi Abu kai tsaye suyi babu gar dama, Khalida ya kalli d’an uwansa yana fadin”Kai wai ya kabarin wancan gurgun ne,? Wallahi naso ma mutuwa yayi shege Dan asara,wato shi da yana zaune yana jiran mulki, kakansa yayi ubansa yayi Dan rashin imani,shine yake so yayi shima, ko an fada masa muma ba ‘yan sarautar bane oho,ai yanzu kuma mulki ya dawo hannunmu Dan uwarsa sai dai yaga anayi sai mun kashe shi da bakin cikin mu.” Ansar yace.” Kaii manta da wannan, sai muga da wace k’afar zai hau kujerar mulki ballantana ya zauna.” Hahahahahaha!!suka kwashe da dariya, kamar da wasa sai Khalifa ya k’ware ya fara tari!! Ansar ya mik’a masa ruwa ya kurb’a tarin yak’i tsayawa idonsa yayi jajazur har yana k’okarin fad’uwa daga kujerar ya damk’e k’irjinsa sosai yana ta tari idanunsa duk sun futo waje, Hajiya Kattime ta futo daga dakin taga abunda yake faruwa da sauri ta k’arasa gurin tana salati, har ya fado daga kan kujerar ya kifa sosai ya galabaita, Ansar duk ya gigice’ yan uwansa dasu kenan sunyi tsaye a kanshi, ji sukayi kamar anyi ruwa an d’auke, da saurin Al’amin ya d’ago shi, sai yaga wuyansa ya karye ya tafi luuuuuu ya fad’i kasa, salati suka saka, Hajiya Kattine tace.” Innalillahi, waina’ilahi raji’un.! Khalifana babana ka mutu ka barni babana kabi Dan uwan ka Moddibo, ya Allah ya jikanka Khalifa na.” Tana share hawaye take fadin Wannan maganar, aikuwa gida ya rude da kuka sosai, mutuwar ta girgiza su mussaman dai Ansar da suke, hira dashi, da sauri Al’amin ya nufi fada domin ya sanar da mahaifin su halin da ake ciki.
????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button