GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Allah ka azirtamu da “Yaya masu Albarka ,duk Dan da zai zame mana fitina a rayuwarmu Allah kar ka bamu,Allah ka sa mufi qarfin zuciyoyinmu

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
08089965176
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

✍????Writing by
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????

????19

Bissimillahi

Cikin Hafsatu ya isa Haihuwa , Halima Matar ,Maman ce ta tsaya Mata a gidan Lokacin Gwaggo Shatu babu Lafiya Abinka da jikin girma, Iya” Atika ita ce ta karbi Haihuwar ,su Lokacin Domin Lantana ta tafi tallanta Hakanan Uwa! Na waje tana Soyar Awara Tamkar ba matan Aure ba
Cikin ikon Allah ta haifi diyar ta Mace Sak! Mahaifinta Kamar an tsaga kara dashi Fara tas!! Ga hanci har baka, Ayuba ya ruqa Murna ,A take yayi wa jaririya huduba da Sunan Mahaifiyarshi, wato Suwaibah ,sai ya ke ce Mata Balaraba kasancewar An haifeta ranar Laraba

Ko da Lantana ta dawo taga jaririya tace ,Haushi Kamar ya kashe ta ganin Baiwa da kyau da Allah yayi mata ga Hafsatu Lafiya lau,ita San samun ta Hafsatun ta mutu kamar yadda Suwaibah ma ta Mutu , A ranar kwana tayi tana zage-zage Kamar ba tsohuwa ba,

Ita ko Uwa!! Tsabar kyashi bai bar ta ba ma ballan ta ta shi go ta ga Abinda Hafsatu ta Haifa ,ta dai tura Iro gulma! Domin yaje ya gano mata ,Aiko Yaron ya dawo Yana Fada mata kyawun “Yar jinjinyar ,Bakin ciki kamar ya kasheta,ta waiwaya ta kalli Yarinyar ta Shamsiyya,a zaune ,duqun duqun!! Daga ita sai karamin ,Wando ga Wani Uban zarni! Da take yi,Yarinyar Baqa ce Sosai gashi Mummuna Dan Har Iro yafi ta kyau tunda shi ya Dan dauko kammanin Mahaifinshi,ito ko Shamsiyya Kamarsu daya da Uwarta!

Nan taci Alwashin Sake Haihuwa ,Domin tana Zaune Wata baza tazo tafi ta “Yaya a gidan Ba, kuma in sha Allah ita ma sai ta haifi Fari ,sabida Sallau yana da Haske dai-dai gwargwado

Ni ko nace kuji ni da Uwa! Da tsabar jahilci don Allah????

Har a kayi Suna Uwa! Da Lantana basu leqa sun ga Abinda a ka Haifa ba,Balle Sallau” Wanda ya tsiri gaba! Da Ayuba babu gaira babu dalili ganin yadda yayi komai Na Haihuwa ,Hatta hakika, biyu ya yankawa Maijego,shine yake Bakin ciki ,yana tunanin a ina ya samu kudin da yayi wannan Hidimar


Kafin Hafsatu tayi Ar’ba’in Uwa! Ta samu Ciki sai tun qaho take tana hora hanci ita zata haihu ,Shiga Dari fita Dari sai ta yadda Habaici tamkar Wacce bata taba Haihuwa ba ,Ita ko Hafsatu bata ce Mata komai ,in tagama Ai kace Aikacen ta ,sai ta tafi bangaran ,Suyi zamansu Har Magari ba

Balaraba ta saba da Halima Sosai in Kusan Kullum tana Hannunta ,in ko bata gurinta tana can gidan ,Iya Atika, Haka jama’a suke Kaunar ta daga An fita da ita kowa son ta dauke ta yake,Sabida farin jinin ta, Uwa! Ko babu shiri ta bazama, Gurin Malamai a kan Yarinyar ,Wai a Sanya Mata Bakin jini a ida nun Jama’a kuma a saka Ta ta fandare ta zama ga gararriya, Malamin nata yaga Tsubbu bace Tsubbacan Sa ya yi Mata Baya nin Yadda zata yi da kayan Aikin da ya bata Mutukar ta kuskure to babu Makawa “Yayanta zasu Lalace domin Aikin kansu Zai kuma,

Haka ta dawo gida tana Haki ga tsohon Ciki a jikinta, Sai da ta bari dare yayi Sosai kowa ya shige dakinshi ,sannan ta Fito ta daga Manyan dutsinan da suke girgi dashi ta tona Gurin da Wuqa yayi zurfi Sosai ,sannan ta saka Wasu Manya Manyan Layu! Guda biyu ,tayi Sauri ta Mayar da kasar gurin ta Binne ,sannan ta Dora dotsen a kai.

Ashe tayi shuka a idon Makwarwa Domin dai tun lokacin da tafito ,Halima ta ganta ita ma ta ta shine domin Zuwa ban daki har ta fito sai ta Ja da baya ,ta labe jikin kofar ta ganin Uwa!! A Gurfa ne a gaban Murhu ta dage tana To na wa.

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
08089965176
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

✍????Writting by
Binta Umar
Maman Abdul Wahabu

ZAMANI WRITES ASSOCIATION

????20

Bissimillahi

Uwa! Na gama binne Layun ta Mike ,tana karkade jikinta sai wai ge wai ge take Na rashin Gaskiya, tayi Sauri ta shige dakin ta

Ita ko Halima sai ta bari ta dai najin Motsin Uwa! Daga dakin ta,Sannan ta fito a hankali,ta aje botar hannunta gefe ,ta Dauke katon dutsen ,sannan ta sa Wuqa tafara tone Abinda Uwa ta Binne! A gurin
Can ta tonu Layu daure jikin Wani Jan yanki, tayi Bissilimih gami da sanya Hannunta ta dauke ta aje gefe ,ta fara mai da kasar gurun tana Rufewa,Tsaf ta Gyara gurin ,ta mike tana Addu’oi ta dauki Layun ,ta je ta aje a gurin ta,Sannan ta dawo tayi Uzirin ta dama Abinda ya tashe ta kenan,
Jin Motsin bude kofar ban daki ne yasa Uwa futowa da Sauri ,Tana kallon Bakin Murhu,Ajiyar Zuciya ta Sauke ganin Babu Abinda ya faru yadda ta bar gurin haka yake, Kallon- kallo sukayi ita da Halima,Sai ta buga tsaki ,ta joya ta shige dakin ta ban ko kofa!

Girgiza kai! Halima tayi kawai,tana Mamakin Zuciyar Uwa Tamkar ta kafurai, A fili tace Allah ya shirye ki Uwa!”

Ta shige dakin ta ita ma

Safiya nayi Uwa! Ta fito ta aza tukunyar Awara ,A wuta ta dinga Hura huta Sosai sabida Malam yace Mata ,In ta binne layun ta saka Wuta sosai a gurin yadda Aikin zai fi saurin kamawa, Ai kuwa haka tayi sai Faman Saka ice take, duk a kokarin ta Na taga Balaraba ta lalace,
Allah ka sa muda ce

Can Bangaran Halima kuwa ,babu Wanda ta fadawa Abinda ya faru ,kawai Safiya nayi ta boye Layun Cikin Hijab din ta ,ta fita daga gidan,kai tsaye gidansu ta nufa,dama kusa ne,ta sanya kannenta ,suka kwance Layun ,tare da yi musu futsari Sannan tace ,su jefa a Masai!

Ai kuwa haka yaran sukayi Abinda ta Umar cesu, Nan ta rarraba musu Goma-Goma suka tafi suna Murna,

Maihaifiyar ta take Tambayar ta Mai nene”?

Nan ta warware mata komai

Tace “Gaskiya Uwa! Bata da imani Wallahi narasa Abunda Hafsatu ta tsare mata,Bai wuce ita tayiwa Asiri ba”

Halima tace”Tabbas ita za tayi wa ,in sha Allahu sai dai sharrin ta ya bi ta,tunda ita ba ta nufe ta da shi ba,


Wannan Shine sanadiyar Lalacewar Iro ,Uwa!Na zuba Ido taji an ce Balaraba tafara sace-sace sai Hakan tafaru kan Dan ta Iro, Kwatsam! Suna Zaune daf da Magariba dukkaninsu a tsakar gida har Lantana ,ta dawo daga yawon Tallanta, Tafito da ciniki tana lissafawa Sallau! Ma shigowar sa kenan ,yana gyara tsayuwar Kekensa, Ita Kuma Tana Aikin Awara Wacce Shamsiyya take Zama gidin bishiya tana Soyawa da daddare,

Kawai! Suka ji ihu! Ana barawo barawo Kafin suyi Wani yunkuri! Iro yafado gidan Yana Haki! Gashi sai Warin ganye! Yake yi,idonshi yayi ja,da gudu ya shiga dakin Lantana ya kulle ,

Matasa ne suka shi go sun kai su goma ko wannesu riqe da Abin duka! Suka Zagin Iro ! Wai sai ya fito sun dake shi,

Lantana ta Mike a zabure! Tana gyara daurin Zaninta bayan ta Kwashe kananun kudinta da ta baza a kasa tana qirgawa ta boye cikin ,Wani burgujejen Sket din ta Mai Aljihuna,Wanda take sanyashi a ciki kafin ta daura Zani, takarasa In da suke tsaye Suna Hayaniya! Sallau Sai Rarrashin su yake Sabida ,dama shi tuntuni yaji Labarin Abinda Dan shi yake Aikatawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button