GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace”Ku tsinannu! “Yayan Mutsiya ta, Mai jika Na yayi muku ,kuka biyo shi da Abin duka sai kace ,Wanda kuka kama shi da kayan Wani!
Daya daga cikinsu, Yace “ke! Tsohuwa Kar ki rainawa mutane Hankali mana! Eh! A kwai tsinanne irin Iro! barawo Mai kwatar Wayoyin Mutane, Kinga Wannan Yaron ya fizgewa Waya,yanzu An ai keshi ya kai chaji ,Sabida haka kushiga Ku fito dashi ,Billahillazi Ku mu balla kofar! Mu Saba masa Kammani,dama ya ishe mu da Sace-Sace’ A Unguwa babu dama a Aiki Yara da kudi ,sai ya kwace.
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
08089965176
[04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????????????????
????????
????????
????????
????????
????GIMBIYA BALARABA????
????Writting By
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU
ZAMANI WRITES ASSOCIATION
????21
“Sai dai idan kune barayi To kaji”! Lantana tafadi Maganar Kamar zata kaiwa Yaron Duka! Taci gaba da Cewa “Nasan Halin jikana baya Sata ,haka Kawai zaku kala Masa Sharri, Mutsiya ta”
Wani Yaro Da suke kira Umaruru Dan zafin Kai Ne ,Sosai Bai Saurari Kowa ba Yayi Hanyar Dakin da yake Hango iro tun dazu yana Leqo da kai ta taga, Ya daki Kofar dakin da kafarshi daya,ta bude wai sunan an San ya Mata Sakata , Ya kamo Iro suka fito ,Yana turjewa, Nan Mata San suka yo kansa ko wanne da Abin duka ,suka fara jibgarshi suna Tambayar inda ya kai Wayar da ya kwace
Nan Uwa! Tafa sa ihu! Tayi kan su Tana tutturesu Wai kar su kashe Mata da! Su fadi ko nawa ne kudin Wayar Zata biya su
Lantana ta rika dura Musu Ashar tana bangaje su Lallai sai ta shiga tsakiya ta Hanasu dukan iro
Umaruru ya Sanya Hannu daya ta ture ta tafadi a gurin ,Amma duk da Haka bata dai Na Zaginsu ba gami da Yi Musu mugun Baki
Shi ko Sallau Shiru yayi yana kallonsu yana tsaye jikin bango yasan ko yace Suyi Hakuri ba za su hakura ba ,Sabida yasan Dama sun Dade sunaso su kama iron, Shi tsoro yake Ma kar su hada dashi,
Halima da Hafsatu suka fito suna rokarsu suyi hakuri ,Amma Ina!! Sam sun ki hakura sai dukanshi suke Suna Tambayar inda ya kai Wayar Mutane, Amma Yaki Magana Sabida tsabar Taurin Kai!!
Makota cike da gidan suna Kallon ikon Allah ,dayawa daga cikinsu cewa suke Alhakin Hafsatu ne ya fara kama Uwa!
Uwa! Ko Na can tana zagi Sallau Cikin Rashin kunya tace”So lubiyo Namijin hotiho ,kana tsaye a shigo har gida ana dukan Dan ka ka kasa tabuka komai, kai dai kayi Asara Wallahi
Balaraba ce ta shi go gidan Jikinta Sanye da kayan Makarantar Isilamiyya Riga da wando da Hijabi ,Kafadar ta sakale da jakar buhu ,Wacce ta sanya Alkur’ani hade da Sauran Littatafan Addini.
Da kyar! Ta samu ta Ku tsa cikin Mutane ta isa gurinsu,Hsnkalinta Nakan su Umaruru ,Ganin suna dukan Iro babu Imani gashi kowa yayi shiru,
Lantana Ta kalleta ta Watsar Tace”Kunga barauniya nan ita zaku doka Ba iro ba domin ita ke min satar “Yan kudade na idan naje Tallah Na dawo ko tausayi Na,bata ji Sabida tsabar Rashin Imani”
Ta karashe Maganar tana mikewa Tsaye
Dukan ninsu suka joyo suna Kallon Balaraba jin Abinda Lantana take fada a kan ta,
Hakan yaba Iro da mar tserewa da gudu yayi Waje hanci a fashe yana jini ,ga jikinshi yayi budu budu Rigar da yake sanye da ita ma ta yage! Tsabar Wahala
Umaruru Yace”
Balaraba kin dawo daga Makarantar”?
“Eh Umaruru Balaraba ta fada cikin Nutsuwa
Umaruru ya Kalli Lantana ,yace” Wallahi kuji tsoran Allah da ranar Lahira tsohuwa ,Ku dinga fadin Alkairi a kan Dan Wani Balaraba yarinyar kirki ce,Domin ba ‘a taba kamata da kayan Sata b…..
Uwa ta katse shi ta hanyar Cewa”Dole kafadi haka mana Munafiki Allah ta Allah ,sabida kana kama ta ka latse a lungu da sako ,Ai mun San duk Abinda yake Faruwa ,Babu Abinda bamu Sani ba” Ehee!!
Kuka Mai cin Rai Hafsatu ta fashe dashi ,ta shige dakin ta da gudu,ita ko Balaraba Tana tsaye Babu Cikin dakiya idon ta tar! Duk da a lokacin tana da kananun Shekaru ta Gama gane Bata Da babbar Makiyya kamar Uwa!
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
08089965176
[04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????????????????
????????
????????
????????
????????
????GIMBIYA BALARABA????
????????????????
????????
????????
????????
????????
*by*
BINTA UMAR
MAMAN ABDUL WAHABU
ZAMANI WRITES ASSOCIATION
????22
Uwa!
ta cigaba da cewa “dama duk wannan yawon da take yi da sunan zuwa makaranta ,mun san iskanci take tafiya tunda dama “yar nagada ce ,sabida haka kufadi kudin wayar ku a biya ku domin ana da abin da za’a biya,
Ta karashe maganar cikin kuri! da cika baki,sabida tasan bata da wasu kudi idan ba jarin a wararta ba,
Umaruru mamaki ya cika shi jin abinda uwa take fada,sai ya girgiza kai kawai yana mamakin sharrin wasu matan ,shiyasa a kace ko shedan yana gudun sharrin mace,
Balaraba kuwa tana tsaye babu damuwa a tare da ita domin in da sabo yaci ace tasaba da irin kiyyar da suke nuna ma ita da iyayenta, shiyasa abin baya damunta da yake yarinya ce mai taurin zuciya ,sai dai abin yai ta damun mahaifiyar ta,itama babu abinda take iya yi idan ba kuka ba.
Umaruru ya kalli uwa! dake tsaye tana hura hanci! yace”kudin wayar nan dubu bakwai da dari biyar ne ,sabida haka tilas a biya ,hakan kuma ba ya na nufin cewar in muga iro baza mu damka shi ga hukuma ba,tundadai kowa ya shaida da hakan.
Sallau yayi saurin tarar sa yana kwantar da kai yace”umaruru kuyi hakuri a kashe magana anan don Allah za muyi masa fada ,in sha Allah bazai kara ba.
Uwa
Kuwa da taji maganar dubu bakwai gabanta ya yanke ya fadi sabida tasan dudu-du jarin a wararta bai kai na dubu uku ba,kuma dashi take joyawa suna cin abinci sai tafara sake-saken yadda zatayi,
“Tun yaushe kake fadar haka,cewar zaka ja kunnesa naji labari cewar ai kai yake kawowa kudin kuke rabawa shiyasa kake daure masa gindi
Sallau ya gigice sai rantse rantsa yake yace”ni ko kwabo baya bani ban sani ba ko uwarsa yake kawowa gatanan a gabanku ni babu ruwana”
Dama umaruru ya fadi maganar ne domin ya tsoratar da shi.
Cikin uwa! ya duri ruwa sabida tasan idan suka gane tana karbar wani abu daga hannun iro itama ba kyaleta zasuyi ba,
Tayi sauri ta katse sallau dake basu hakuri,cikin rashin kunya tace”dallah malam matsa kabawa mutane guri solobiyo kawai,kai umaruru nawa kace ma kudin wayar,? tafadi maganar sai kace wacce zata iya biya
“Dubu bakwai dari biyar ne”
Ta kalli Lantana wacce tunda zu ta kasa furta ko a sabida taji ana maganar biyan kudin waya, ita kam bata da ko kwabo ba zata bayar ba.
“Lantana ki fito da kudin nan danaga kina lissafawa a biyasu kudinsu ,tunda dai kema iro yana mora miki kullum da daddare sai kin ce ya siyo miki balangu ko kifi”
Lantana tayi tsuru-tsuru tana motsa baki ,da kyar! tace “mai nake dashi “yannan ! da zan bayar so kike na rusa jarina”
Cikin rashin mutumchi Uwa tace “Lantana dole fa kifito da kudin jikinki ko kinqi ko kinso wallahi domin bazan bari su kashemin da ba,ehee”!!
Da kyar! Lantana ta kwance zaninta tana daga zaune ,sai surutai take tafito da “yan ashirin ashirin da “yan goma goma ,kwata kwata a kudin babu hamsin ko daya
Uwa tazo ta kwashi kudin da sauri ,tafara lissafawa,
*Balaraba ko na tsaye cikinta kamar ya kulle dan dariya sai boye dariyar take dan kar ta fito amma INA! sai da ta subuce mata ta zauna kasan gurin tana yi tana kallon Lantana dake faman share gumi! Sai tsine-tsine take,wai sam bata yadda ba kalawa Iro sata a kayi