GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

,Aiko Lantana ta dauki wata sanda da suke tone kwatarsu idan ta toshe ta kaiwa Balaraba duka da ita tana faman zaginta ta uwa ta uba.
Balaraba ta mike da sauri ta shige dakinsu tana jiyo Lantana kamar mahaukaciya tana ta dura mata ashar tamkar ba tsohuwa ba.
To da kyar! dai Uwa ta samu ta hada dubu uku da dari biyu,domin kudin gun Lantana ko dari biyar basu kai ba,ta mikawa Umaruru gami da cewa”gashinan Abinda ya samu kenan,Shamsiyya bata dawo daga tallaba,kuje kubawa mai wayar hakuri idan an kwana biyu za’a cika masa kudinsa,domin Allah ya hore abin da za’a biya
Umaruru ya karbi kudin yana lissafawa tsaf!
Yace “kifadi ranar da zaki ciko kudin kawai bama son jeka ka dawo”
Tabe baki tayi tace”ku dawo rana ita yau zan Baku kudinku”
“To Allah ya kaimu kar muzo kice wani abu fa”
“Mtssss nifa nace kudawo Ku karba ,akin banza akin wofi,Uwa! tafada a zafafe ,bakin cikinta yadda ta rusa jarinta yanzu kafin ya tashi ma aiki ne
Umaruru yaja ta wagarshi suka fice daga gidan,suna fita Uwa tace dawa Allah ya hada ta duk wanda ya kwana ya tashi a gidan sai taci masa mutumchi kar dai Sallau yaji labari,
Simi-Simi ya kama hanya zai shige daki ,tayi saurin janyo masa riga gar wuyanta ya yage ,tace”kama hanya ka fita ka nemo mana abinda zamu ci ehe! wallahi baza ka shigarmin daki ka zauna min ka kashe min katifa babu abinda kake min sai dai in nema ,in ci da kai in ci da “yayanka”
Bai ce mata komai ba ,ya fizge rigarshi gami da gyara wuyanta in da ta yaga masa,ya sakai ya fice daga gidan babu abinda ya dameshi,can mahadarsu ya nufa,abokanshi na Zane suna ta faman karta! (Caca) nan ya zauna cikinsu a ka fara yi dashi.
ina so Ku fahimci ko wane marubuci da nasa salon,gaskiya ni babu yadda za’ayi in yi rubutu batare da na fadi jogon labari ba ,domin shine ginshin fara karatu, So dan Allah kuyi hakuri kuci gaba da bina a yadda nake za azo in da kuke so
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
[04/05, 03:17] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
*By*
BINTA UMAR
Maman Abdul Wahabu
ZAMANI WRITES ASSOCIATION
????23
Bissimillahi
To haka rayuwa take, Ayuba ya yi ta fafutukar naman abinda zai rufawa kanshi,asiri ,yayin da “yan uwanshi suka tasa shi a gaba har sai dai suka ga ya kwanta, ba ya iyayin komai da kanshi sai dai ayi masa,gashi lokacin nauyi yayi masa yawa dalili kuwa yayarshi Atika mijinta ya rasu,sai ta dawo gidan ta zauna dakinsu na gado ita da “yan uwanta ,da suke can garinsu ,suna aure,a lokacin Balaraba na da shekara goma sha uku, sai kanwar ta ,wato sadiya, tana da shekara tara,sai qaramin kaninsu Usuman dan shekara bakwai.
Sosai Ayuba yake ciwo an rasa gane kan ciwon anyi na asibitin har an hakura ,sai aka dawo yin na hausa,sabida yadda kafarsa guda ta kumbura take fitar da ruwa abin babu dadi , wani mai maganin hausa da yazo ya dubashi ,yace jifansa a kai (Asiri) sabida haka kar a kara yin maganin asibiti domin zai kara rikita ciwon,cikin ikon Allah ya hada magani ya bashi nasha da wanka gami da shafawa, a kafar,sai a ka fara samun saukin abun, domin wani lokacin yakan tashi da kan shi yafito waje yana dafa bango,
Tunda yafara wannan ciwon tsakanin Sallau da Lantana da Uwa babu wanda yazo ya duba shi ballan tana yace dashi sannu ,gwara Mamman shi yazo dalilin tursasawar matarshi Halimatu,
Lantana tace yadda uwarka ta tafi tabarka haka kai ma zaka tafi kabar naka “yayan gyyar tsiya arna a idi, kullum in zata fita yawon tallanta sai ta tsaya a tsakar gida tayi surutai ,sannan take tafiya ,tana fatan Allah yasa kafin ta dawo ta tarar ya mutu kowa ya huta
Allah mai yadda yaso a sanda yaso ,an kwanta da Ayuba lafiya daran alamis ,domin kafin yayi bacci ma sun dade da matarshi da yayarshi Atika ,gami da “yayanshi suna hira,ashe ta bankwana ce, da asubah Hafsatu ta rika tashin sa taji shiru ,sabida ta saba duk asubar fari shi yake riga kowa tashi a gidan,shiyasa ta gigice ta fice daga dakin da sauri,tayi dakin Iya Atika,ta daga labulen ta ce”Iya fito kiga babansu Sadiya yaki tashi,
Da sauri Iya ta mike daga kan dadduma ta fito tana salati a zuciyar ta domin dama jikinta ya bata ,tunda ta kwanta take munanan mafarkai,
Ta shiga dakin gami da zama kusa da qanin nata ,tana kallon yadda idon shi suka kakkafe tasan lallai Ayuba ya amsa kiran Ubangiji, salati take tana sallallami ,Hafsatu tace “Iya ya mutu ko”?
Iya Atika tarasa mai zata ce mata sai kawai ta kama hanya zata fita daga dakin tana sharar hawaye,
Kafin ta daga labule,taji abu ya fadi, rigif!! wanda yayi dai-dai da farkawar Balaraba daga bacci a furgice! Iya ta dawo dakin da sauri tana Salati ganin yadda Hafsatu tafadi kan Ayuba dake kwance,
Tana daga ta taga ta kwanta yaraf! alamun babu rai! a jikinta,
INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN
Abinda Iya tafada kenan,
Balaraba ta mike tsaye a zabure tana kallon iyayen ta biyu a kwance ,dukkaninsu babu rai! tace”Iya mai nene Iya kar kice min babana ya mutu,! Iya ki tashi Umma na kin ga tafadi, a kasa, sai ta fita waje da gudu bata saurari abinda Iya take fada mata ba,
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
08089965176
[04/05, 03:17] +234 808 996 5176: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
GIMBIYA BALARABA
????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
*By*
BINTA UMAR
MAMAN ABDUL WAHABU
BISIMILLAHIR RAHAMANIR-RAHIM
Page
24
Lantana dake tsugune bakin rijiya tana daura alwala,ta juyo da sauri ganin Balaraba ta fito da gudu daga dakinsu tana ihu,sai ta mike tsaye gami da sakin botar hannuta,tace”ke Balaraba kina hauka ne,dan ubanki ko Ayuba ne ya mutu abinda zakiyi kenan,shashasha mara hankal….
Kafin Lantana ta karasa maganar ,Iya ta tare ta ,da cewar “to ai zan ce ya kare Ayuba da Hafsatu ,sun koma ga Allah,wanda yake ganin zai zauna jiran duniyar gashinan ga tanan.
Lantana ta zabura ,cikin rawar jiki tace “me kika ce Atika, kina nufin Ayuba ya mutu”?
Iya tafashe da kukan da yake cin zuciyarta tun dazu,tace “ai ba’a wasa da mutuwa Lantana ,leqa ki gani,
Jikinta na rawa ta nufi dakinsu Ayuba,
Ai kuwa abinda ta gani ya daga mata hankali sosai ,babu Ayuba babu Hafsatu, Lantana ta furgita sosai ,sai ta fito da sauri,ta fasa wani ihu! da ya ta da mutan gidan gaba dayansu har da makota,
Kankace kwabo gida ya cika da jama’a ana ta kokawa da wannan mutuwar mai abin mamaki.
Balaraba kuwa ta dai na kuka sai dai na zuci idanun ta sunyi mici mici kallon kowa kawai take,takama kanne ta da ke kuka ta rungume itama tana kukan zucci.
Uwa da Lantana kai har da Sallau , mutuwar nan ta gigitasu ta firgitasu,sosai jikinsu yayi sanyi,amma abin mamaki ana yin sadaqar uku ,shikkenan ,suka watsar,mussaman ,yanda suka ga irin mutanan Ayuba ,suna kawo taimako, sai Sallau yayi uwa yayi makarbiya yace”ai shine wakilin yaran, sai Iya tayi da gaske sannan yake barinta ta karbi sadakar,komai idonshi na kai,ita ko Balaraba ,in an bata ,sai ta mikawa Iya,Ashe Sallau duk yana lura,sai yaga babu idon Iya sai yayi ta zuga Balaraba wai ta karbi kudin ta tabashi ,ya aje mata sabida in tazo yin aure shi zai yi Mata kayan gado,