GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Iya ce ta fito daga ban daki hannuta rike da buta ta tace”Balaraba kin dawo kenan”

Tana kokarin bude kofar dakinsu tace”e wallahi Iya, ya gida”?

“Lafiya kalau ai tun dazu nake cewa shiru baki shigo ba gashi ba kya kawai magariba”

“Wallahi kuwa lokacin da zan fita muka hadu da cinkoso a titi haka ma yanzu abinda ya tsai dani kenan, ga mariba ta wuce ban yi sallah ba”

“Ai kuwa sai ki yi harama yin sallah sabida kin san sallahr magariba lokacin ta kurarre ne”
Iya tafada ta kokarin daura Alwala

Lantana ta hau surutai na ha baici, tanayi tana tauna goro babu abinda ya dameta,

Iya da Balaraba suna jinta babu wanda ya tanka mata a tsakaninsu

Uwa tace”ke ma dai Lantana da wata magana kike wanda a ka rai na shi za’a fadawa haka ya yarda,mu babu abinda za’a rufe mana duk abinda mutum yakeyi muna da labarinshi,

Sadiya matar Kawu Maman ce ta fito daga wurin ta, ta dan tsinci magan ganun da Uwa take a kan Balaraba, tace”ke dai Uwa kinyi a sara wallahi, ki tsaya kina shirme da “yar cikin ki, ki tsaya ki gama kashe wutar dake gabanki mana, amma kin bi kin sanya yarinuar nan a gaba kullum da irin sharrin da zaki kulla mata,kuma kullum kina cin arziqinta duk abinda kikeyi a na sani, haihuwa ce kema kinyi,duk abinda kasowa kanka to ka sowa dan uwanka, amma gaskiya abinda kikeyi ba kya kyautawa wallahi”

Saura kadan Uwa ta kifar da kaskon tuyar awarar ta wanda yake cike da mai gefe ga uban a wara nan cikin roba ok

Tayi kan Sadiya da masifa “ke kinga sarkin kinibibi da kankan ba, kwadayayya kawai, au! sabida in ta taje yawon iskancinta ta dawo tana kawo miki ajiyar kudi kuyi raba dai-dai shine kika fito zaki tare mata, iyi, to bari kiji babu ruwanki da ni da ” yayana wallahi, bakinki ya sari dayan kashi,duk cikin zuri’ata ban haifi lalatattu ba ehe! ke da baki san ciwon haihuwa sai ki fadi haka, in kinyi zuciya yau ki haihu banza juya wacce bata haihuwa kawai”
Uwa ta kare maganar tana buga cinya bakinta duk ya tara yawu sabida sabida tsabar jaraba da masifa

Sadiya tayi wani murmushi mai ciwo ta kalli Uwa tace”Babu abinda yake damunki sai jahinci, wannan “yayan naki da kike magana a kansu,ni a gurina da haihuwarsu gwara babu,sabida zasu iya yi miki sanadin shiga wuta, sabida haka babu abinda zan ce yanzu sai dai in ce Allah ya shirye ki, kuma Balaraba da kike wanna tada jijiyar wuya a kanta tafi karfin ki daga ke har ” yayan ki”

da mara Uwa taci ta dinga cusawa Sadiya zagi gami da gore-gore tace “karya kike ki ce wancan mutsuyaciyat yarinyar tafi qarfina wallahi sai dai idan banga dama ba,ke dai kawai kice kina yi min bakin ciki kawai ganin ke baki haihu ba,

Lantana na zaune tana jinsu uffan bata ce ba, dama in suna fadansu bata saka musu baki, Iya kuwa sauri takeyi ta idar da sallaha tafito,

Balaraba ma sa taji abin yayi yawa tafito ta kama Matar Kawu da yake haka take kiranta dashi, tana bata hakuri da kyar ta mayar da ita gurunta, tafito ta daura alwala, kowa yayi shiru, sai Uwa ce kawai take zage-zage ga yara nan sunyi cirko-cirko suna kallonta taqi tazo ta sallamesu,

Walidi ne ya shigo gidan kafadar sa rataye da wani katon buhu cike da robobi da gwangwanaye da kwalebe gami buhun-buhuna, ya tadda Uwarshi tana ta sirfa asahar sai kace ba magujiya

Ya na wani ciccije baki yace” ke kuma Uwa wai menene? tun daga waje a ke jiyu masifarki ke dawa ye ne ehee!!
Ya karashe maganar yana cije baki

Tana kokarin zama kan kujerat suyar a warar ta tace”yo ni da waye ne in ba wacan “yar iskar yarinyar ba, ita kuma waccan juyar mai zaman kashe wando ta fito tana min maganar banza, sabida bata san darajar haihuwa ba take fadin wai da hai huwarku gwara babu, shine nake ci mata mutunci,domin ina raye babu mahalukin da ya isa ya tabaku in kyaleshi ko da ko sarkin garinan ne Almusfah”

Bai tsaya ya gama sauraran abinda take cewa ba, ya nufi gurin Sadiya gadan- gadan, yana wani irin zagi irin na marasa tarbiya, ya daki kofar gurin da karfi abinka da kofar da babu kwari sai ga ta tabude da kanta, kokari yake ya shiga gurin, Iya tana tareshi yace”dallah iya saurara mana, wannan matar har ta isa ta ai bata mu ko tafada mana magana dan Uwarta! yau sai na farke mata ciki da kwalaba wallahi,ki kyauce kawai na afka mata, sai na nuna mata waye ni, yawa kike Iya!!!

“Walidi wato ni ban isa in fada maka kaji bako, yanzu Matar wan mahaifinkan naka zaka cakawa kwalaba,iyi yaushe ka zama haka”
Iya tafada tana rirriqeshi

Matar Kawu ce tafito jikinta sanye da hijabi hannunta rike da carbi da alama bata dade da idar da sallah ba

Tace”Iya sake shi gani na fito yazo ya caka min kwalabar, in ya cika shi mara kunya ne, yau zasu ga gatana daga shi har Uwarshi”

kafin Iya ta ankara Walidi ya kwace daga hannuta, ya nufi inda ya jibge buhun shi na gwan-gwan ya ciro kwalbar maltina guda ya basa ta a kasa yayi kan Sadiya cikin zafin zuciya!

YANZU A KA FARA✍????
[22/06, 15:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

®BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

????30

______Da gudu Balaraba ta kara so gurin tace”wai kai Walidi me yake damunka ne,? wane irin zafin zuciya gare ka, kanaso ka aikata aikin da nasani a rayuwarka, ni in dai a kai na kuke wannan abin zan tafi in bar gidan sai ku sake a ciki, amma duk tsiya nan ne tushe na, kuma da nan nake gadara,ni wannan masifar ta ishe ni wallahi”

Jin furucin da Balaraba tayi yasa Lantana ta mike a zabure ta nufi inda a ke rigimar tace” kai Walidi ka kiyaye ni wallahi, wato kanaso ka jawo mana musiba,ko bisimillah ka caka mata kwalba mugani,wato uwarka tana daure maka gindi ka yi abinda kaga dama,ai uban naka zai shigo ya same ni, ehee”!

Ta kalli Balaraba dake tsaye tace”ke kuma da kike cewa zaki bar gidan,gidan ubanki zaki je, kinaso ki kara nunawa duniya dama zaman kanki kikeyi ko, kina min bakin cikin abinda kike bani kullum ta Allah to babu inda zaki je,kina nan kina cigaba da samo min kudi ehee!!
Lantana ta karashe maganar tana gyara daurin zaninta

Tsaki Balaraba taja kawai ta bar gurin domin cigaba da tsayuwarta a gurin zai ya janyowa ta zagi Lantana ko ta gaya mata magana,shi yasa tabar gurin ranta a bace

Uwa kuwa jin abinda Lantana tace yasa ta dinga ga ya mata bakaken maganganu, tace”wallahi Lantana sai tau na kara tabbarwa cewar ke muguwar kwadayayyi yace, wato duk abinda nake miki ba kya gani, ai sai kije ki tayi”

Shiru Lantana tayi mata sabida tasan masifar jarabarta, ta mike taje ta dauki buta ta shiga ban daki, batare da ta saurari cin mutucin da take mata ba,

Wannan kenan

GIDAN SARKI

Yana zaune a lambu dake shashen shi, wasu dogarawa masu manya-manyan riguna da manyan rawani, su biyu suna tsaye a kanshi, daya da wani katon mafici daya kuma a tsaye yana bin gurin da kallo, daga yaji motsin abu zai duba,

Shi kuma yana kishin gide kan wani tuntu ja da adon zane irin na sarautar garin, yana sanye da wata shadda milk colaur mai mugun tsada,wacce a kai wa dinkin “yar shara da dogan wando gaba da baya na rigar surfani ne irin mai dauke da alamun gidan saurata, duk kayanshi na zaman gida haka suke dai-dai da jallabiyoyinshi,a kwai tambarin sarauta, wani kara min littafi ne na addini a hannunshi yana dubawa, ta cikin farin tabarau din dake idanshi, duk wanda san Sarki!Almansor ya kalleshi a yanzu ya san da akwai abinda yake damunshi,sabida walwalar shi ta ragu kuzarinshi ya ragu duk da cewa dama tun fil’azal shi ba mutum ne mai fara’a da dariya ba, kafin ka ga dariyarshi sai kayi da gaske, sannan kullum fuskarshi a tamke take tamau, to a ” yan kwanakin nan abin yakara karuwa wanda har sai da Mahaifiyar shi ta fuskanta, lokacin da ta tsirashi da tambaya yace mata babu komai, sam bata yadda da abinda yace ba,tafi zaton ko maganar da tayi mishi ce a kwanaki, take damunshi, sabida haka, tasa Jakadiya Shafa’atu mai mata hidama taje can shashensa ta kira mata shi,tunda takira wayarshi yaqi ya dauka, tasan halinshi da muguwar bakar zuciya da muskilanci, ba ai masa komai ba ma sai ya tsiri share mutane ko yayi kwana da kwana ki bai kula kowa ba, yanzu ma haka tun shekaran jiya da sukaje daurin aure gwarzo shida su Waziri bai kara fitowa daga shashensa ba, shi kadai yake rayuwarshi shida hadiman sa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button