GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

daya daga cikin wayoyinsa ne tayi kara,
cikin ginshera gami da kasaita ya karbi wayar daga hannun daya daga cikin fadawan nan guda biyu,ya kalli scerin din wayar yana ya mutse fuskarshi,
“Muddibo na! sunan da ya gani kenan yana yawo ka screen din wayar
Wani murmushi ya saki wanda ya fito masa da kyawunsa da zatinsa,ganin sunan Abokinshi kuma dan Uwanshi amininshi, ba tare da bata lokaci ba ya daga wayar, cikin Yanayin muryarshi kasa-kasa yace”ya akai ne, ka shigo garin ne”?
YANZU MUKA FARA✍????
[23/06, 13:45] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
????????????????????????????????
_*Na*_
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
Zamani Writes Associatio
Bisimillahir rahamanir rahim
????31
________Daga 6angaran Maddibo yace”yau kwana na biyu da dawowa, nakira wayoyinka jiya shekaran jiya da jiya duk a rufe, ko jiya nazo gaisuwa fada ban gan ka ba, shine Fulani tace kana gurin ka kwana biyu a kulle ka ki saurarar kowa, hakane ko”?
Zakuda kafada yayi ranshi ya soma baci jin irin maganar da Maddibo ke masa sai kace wani ubansa,yace”Ubana ne kai da zaka turkeni kana tambaya,in kana bukatar ganina ai kasan in da nake, meye sai ka tsaya tambaye-tambaye, zan kashe wayata in magana zaka fadamin,
ya karashe maganar yana kokarin datse wayar, cikin zafin zuciya
Sanin halin sa da yayi na saurin daukar zafi yasa yace”zaka fara halin naka ko, daga magana sai hayaniya, baka tsaya ka saurare ni ba, dan Allah ka rage wannan zafin zuciyar taka”
Shiru yayi masa,
Maddibo ya cigaba da cewa “zan shigo in anjima, muyi wata magana, kwana biyu akwai abinda yake damuna wallahi”
Da kyar yace”ina sauraron ka,
bai saurari abinda Maddibo zai ce ba kawai ya kashe wayar,
Da sauri Dogari ya karbi wayar ya aje ta kusa dashi, ya koma ya tsaya inda yake
Ko minti biyar ba ai ba wani kiran ya kara shigowa daya wayar tasa, mika hannunsa yayi ya dauka sabida ba ya san irin abinda suke masa ko zama zai gyara duk sai su zabura suna dube-dube,wani lokacin in abin yayi yawa sai ya hanasu, to ko ya hanasu din ba sa dai nawa
Ummina! sunan da ya gani yana yawo kan scerin din wayar
sai da takusa tsinkewa sannan ya daga,
“Yayi maka kyau, Fulani tafada ranta a bace, ta cigabah da cewa, yau ni kake gwadawa halin naka ko, sabida kawai na yi maka fadan gaskiya,wato kai ba a isa ai maka fada ba ko,shikkenan kazo ina ne manka in kaga dama”
tana gama fadar maganarta ta kashe wayar bata saurari abinda zai ce ba
Ya fi minti biyar kanshi a kasa yana latsa wayar, zuciyarshi tana masa wani mugun zafi, sam Ummi takasa fahimtarsa da inda ya dosa, shi ba auran ne ba yaso ba, yarinyar da takawo masa a matsayin wacce take so ta zama matarshi kuma uwar “yayanshi itace sam bata kwanta masa ba, Halisa kwata-kwata bata cikin tsarin matan da yake so ya aura
Mikewa tsaye yayi, da sauri daya daga cikin hadimanshi ya gyara masa ta kalmanshi wasu masu gashi masu kalar ja da baki, saman su a rufe, ya zira cikin kafafunshi masu dauke da zara zaran ya tsu tamkar wanda bai taba taka kasa ba,Yadda yake tafiya sai ka zaci tausayin kasa yake ko baya san taka kasa, cikin kasaita yake tafiya, hakan ya zamar masa jiki tun yana yaro haka tafiyar shi take,
Mama Fulani na ki shingede a wata katuwar dadduma da wani katon tuntu, suna hira da Jakadiya Shafa’atu, tana yan ka mata lemon zaki,dake Fulani tana san shan kayan frut shiyasa kullum bata rabo dashi a gabanta,
Yayi sallama ya shiga cikin yanayin tafiyarshi ya karasa ciki sosai
Tunda ya shigo Shafa’atu tayi kasa da kanta,har sai da ya zauna sannan ta dago kanta,ta kai gaisuwa sannan ta mike ta bar dakin cikin ladabi
Mintuna goma tsakani babu wanda yace komai tsakanin Ummi da shi,
Gyaran murya yayi ya ce”Ummi an tashi lafiya”?
Shareshi tayi ta cigaba da shan lemonta
Matsawa yayi kusa da ita ya rike kafafunta, ya wani marairaice yace”Ummina an tashi lafiya”?
Harararsa tayi tace”sai yanzu kasan dani, zaka dameni da tambayar tashi lafiya, da ban tashi lafiya ba baza ka ganni ba”
Shiru yayi mata tunda shi maganar ma wahala take mishi, har yanzu kafafunta na rike a hannunshi
Tace”sakar min kafa mana”
kin saki yayi ya kara rikewa tamau
Tasan halin rigimarshi, shiyasa ta saki fuska kadan tace”Lafiya lou nake shikkenan ko”?
Gyara zama yayi sosai yana kallonta fuskarshi dauke da wani kayataccan murmushi wanda ita kadai ce take ganinshi, yace”Masha Allah Ummina,
“Me sa kaki daga waya ta kwana biyu jiya kuma na aiko kazo kaki zuwa,?
Kasa yayi da kansa sabida yasan halin Ummi da saurin fahimtar mutum,gashi shi sam bai iya karya ba, yace ” Ummi bani da lafiya”
“Karya kakeyi”
Ummi tafada kai tsaye”
Baki ya bude yana kallon Ummin jin abinda tace saura kadan dariya ta subce masa,sabuda yasan halin Ummi ba ai mata karya
“Ko nai maka karya ne”?
Ummi tafada hankalinta kwance
” Baki ba Ummina”
yafada yana boye dariya
“Yawwa ko da naji, in ban yi karya ba, sai in ce yaji ka daka min sabida nai maka maganar Halisa ko”?
Shiru yayi
Tace” ko ba haka bane”?
“Hakane Ummi”
yafada babu wani boye-boye
Kallonshi take cike da mamaki tace”har yanzu kana nan a kan bakanka kenan”?
Zama ya gyara sosai yana fuskantar mahaifiyar tasa, domin maganar da yakeso ya da ita muhimanci ce, yace”Ummi ba wai ina kin Halisa bane, a’a ina kin halinta ne, Halisa bata da tarbiya sam bata cancanci ta zama matata Uwar “yayana ba kamar yadda kikeso, amma tunda kina so shikkenan sai ayi amma dukkanin abinda ya biyo baya babu ruwana”
Shiru tayi tana nazarin maganarahi, tasan Yaron ta da tunani da hangen nesa yana da nutsuwa, nutsuwarshi ce ma tasa Maimarta ba ba ya zartar da wani abu da ya shafe shi ko na menene sai ya nemi shawarar dan nasa
Cikin nutsuwa tace” duk na fahimci abunda kake nufi, ina so ka yi min biyyaya da dukkanin abinda na umarceka dashi, sabida kasan halin yadda nake rayuwa cikin kishiyoyina, da sauran matayen waziran Mahaifinka, mutukar kaki yadda da wannan abu to babu shakka zasuce nice na hanaka auran “yar uwarka, kasan halin mahaifin ka shi babu ruwanshi da kananun maganganu na gidan nan, sabida haka nake neman alfarma a gurinka ka daure ka aureta, na san yadda kake a tsaye duk fitinar Halisa sai tayi laushi, sabida nasan baza ka yadda da shirme ba”
Ummi ta karashe maganar tana sauke a jiyar zuciya
Shiru dakin yayi na tsawon minti biyu sannan yayi gyaran Murya yace” Ummi na amince da abinda kika umarce ni, zan auri Halisa domin in faranta miki rai, amma kin san ba zan yadda da kananun maganganu na cikin gidan nan ba, za’ayi rigima dani, mutukar naji wata magana ta biyo ba,domin ba zan lamunci wani ya zage min ke ba rayukan zasu baci, maganar Halisa ce, na kuma amince zan aureta shikkenan sai su bar maganar”
Yanzu muka fara
[26/06, 22:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
???????????????? ????????????????
∆∆∆∆∆∆
_*GIMBIYA BALARABA*_
∆∆∆∆∆∆
????????????????????????????????
_*Na*_
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
Zamani Writes Association????????
Bisimillahir rahamanir rahim
????32
______Cikin nutsuwa Ummi tace”alhmdulilahi in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkairi,sai dai ina san ka rage zakin zuciyar nan taka kuma ka din ga fitowa cikin jama’a kwata-kwata kwana kwana biyu na lura baka zaman fada ko zaka iya fadamin dalili”?