GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yafi minti uku baice komai ba daga bisani ya dago kanshi yana kallon mahaifiyarshi yace”Ummi kin san halina bana ganin ana yin ba dai-dai ba in yi shiru duk ranar da mai martaba bai fita fada ba in ya wakiltani na lura su galadima basa su mussaman Baba waziri,Ummi su mulki ya dama sam ni bana sha’awar shi zaman fadar ma dan dai Mai martaba yana so ne,shine dalilin da ya sa kawai bana son zama sabuda zakiga suna yin abunda bai dace ba, kuma ba’a isa ai magana ba”
Shiru Fulani tayi tana nazarin maganar dan nata tasan a kwai badakala a cikin gidan duk ranar da Mai martaba ya fadi ya mutu,domin dukkaninsu abinda suke wa kenan mulki, shiyasa suka tsaneta in banda tana da karfin arziki a gidan da tuni sun koreta babu irin jifan da basa mata tunda suka lura tana da ciki shikkenan ko wanne ya tashi hankalinsa, kishiyoyinta tamkar su mutu Asiri ko ta ina,in da Allah ya taimaka itama ba a kwance take ba maca ce mai addini da addu’a shiyasa duk asirinsu baya kamata ko ya kamata bayayin wani tasiri yake karyewa, a taikaice dai sai da cikin Almansor ya kai wata goma da wata goma sanan ta haifeshi lafiya sumul gida ya kace me da murna,da hayaniya sarki Almustap ya haifi da namiji kasancewar duk “yayanshi mata ne su goma sha uku uwargidanshi kawai ta haifi ” yaya maza uku, kuma suka dinga mutuwa daya bayan daya, shine malamin ta yace mata kishiyar ta ce take kashe matasu sabuda tana so ta haifi danta wanda take so ya gaji kujerar mahaifiyarshi dole sai ta tashi tsaye, nan ta daga hankalinta ta dinga kiran malamai gami da “yan bori suna mata aiki a gidan, a kan duk dan da Mai martaba zai haifa in dai namiji ne to kawai ya mutu tun kafin yazo duniya,sosai take aiki da aljanu a gidan duk dan kar wata tazo ta haifi da namiji Abin da bata sani ba shine sauran “yan uwan Maimartaba Almustapah basa so ya haifi da namiji sabuda gudun kar mulki ya koma hannunsa bayan babu shi. Babu irin abinda basa yi na shirka domin ganin bayan Sarki dan su samu damar hayewa kujerar mulki
Fulani ita ce matar maimartaba ta uku lokacin da sarki ya aure ta sai a ka dinga surutai cewar ya auri ” yar malaminshi kuma ba “yar sarauta ba ce, nan kishiyoyin ta suka sanya ta a gaba lokacin tana bata da shekaru da yawa batafi shekara sha uku ba, da yake yarinya ce mai hankali sam bata musu rashin kunya in suna zaginta sai dai ta shige gurinta tayi kuka ta gayawa Allah damuwarta, kusan shekarar ta goma sha biyar a gidan,sannan Allah ya bata ciki da yake doguwar maca ce sai cikin ya boya in banda Maimartaba babu wanda ya sani a cikin gidan,sai ko jakadiyar ta mai suna Shafa’atu da yake ita take hidima da ita,
Cikin ikon Allah da lokacin haihuwa yazo ta haihu lafiya babu matsalar komai.Jakadiya Shafa’atu ce ta gyara jariri tsab ta kwantar dashi a wani kayataccan gado mai kyau irin na yara,sannan tazo ta taimakawa mejego itama ta shirya tamkar ba itace ta haihu ba,
Nan ta zube a gabanta tanayi mata sannu tace” ranki ya dade ki fadi abinda kike bukatar ci yanzu sai a kawo miki,sai ki kwanta ki huta”
Fulani ta sauke ajiyar zuciya kana kallonta kasan tana da damuwa tace”bana bukatar komai yanzu kawai kije fada ki kira min maimartaba”
Da sauri ta mike ta fita daga dakin domin cika umarnin da a ka bata,
Lokacin da ta isa fada cike take duk su Waziri Zayyanu da Galadima da Wamabai hade da dakatai duk suna gaban sarki a gurfa ne, ta karasa taje ta kwashi gaisuwa,sannan ta isar da sakon Uwar dakinta
nan fada tayi shiru kowa yana mamaki yarinya karama zata aiko kiran sarki,kowa jira yake yaga zai je ko bazai je ba, abin mamaki! maimartaba ya mike a nutse ya kalli mutanan gurin yace”zan shiga in fito yanzu a cigaba da tattauna maganar da muke kai insha Allahu in nadawo za’mu samu mafita”
yana gama fadar maganarshi ya wuce wasu dogarawa uku suka bi bayanshi suna baza babbar riga,tare da fadi takawar lafiya gaba salamun baya salamun Sarki mai adalci a fito lafiya, Jakadiya Shafa’atu ta bi bayasu itama tana nata kirarin.
Nan baki kofa suka tsaya bayan Maimartaba ya shiga bangaran Fulani
Tana zaune ita kadai tana tunanin irin rikicin da zai tashi mutukar mutanan gida suka ji cewar ta haihu kuma da namiji wadanda basu san sa zaman cikin ba ma cewa zasuyi karya ne,ita tsoranta kar taje a sabauta mata yaro
Maimartaba yayi mamaki ganin ta tsaf tamkar bata haihu ba.Sannan ga yaronsa mai kama dashi mutuka tamkar an tsaga kara, a hannuta tana shayar dashi, sai ya karasa kusa da ita da sauri fuskarsa dauke da murmushi yace” Fulani mai halin manya mace ma kara da kawaici da kunya,yau na kara tabbatar wa cewa ke alkairi ce a gare ni”
A nutse ta mika masa jinjirin tana murmushi tace”gaskiya naji dadin wannan yabon da kayi min, yau Allah ya sauke ni lafiya kaga bawar da Allah yayi mana”
Hannu biyu yasa ya karbi jariri cikin farin ciki yace”masha Allah dukan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da yayi min wannan bai wa Allah shine abin godiya”
Kunneshi ya kara dai-dai na dan nashi yayi masa hudu ba kamar yadda Annabi ya fada sannan ya kira shi da sunansa sau uku, sai ya mike tsaye gami da rungumeshi ya ce zamuje fada dashi domin tasan da zuwansa”
Hankalin Fulani ya tashi amma sai ta dakewa zuciyarta tayi addu’a tasan babu abinda zai samu dan ta face da sanin ubangiji, nan Maimartaba ya fita da jinjirin a hannunshi fuskarshi dauke da walwala
Fada na cigaba da tafiya kawai suka ga sarki ya shigo rungume da yaro nan hankalin kowa ya tashi aka fara rige-rigen karbar yaron
Waziri Zayyanu ne yayi nasarar karbarshi daga hannun sarki lokacin da ya zauna yace”ranka shi dade a ina muka samu yaro mai kama da kai sak, sai kace an tsaga kara”
A nutse Maimartaba ya ce”yau Allah yayi min baiwarshi Allah ya sauki Fulani lafiya shine dalilin kirana”
Saura kadan Waziri ya yar da yaron jikinshi ya dinga karkarwa kafin kace kwabo gumi ya jika masa riga sai yafara mutsu mutsu da baki kwata-kwata ya rasa abinda zai ce, fada ta dauki murna kowa yana fadin albarkacin bakinsa wasu na boye damuwarsu ban da Waziri domin mikewa yayi ya bar fadar yana sabe babbar riga tamkar zai tashi sama haka shige gidansa dake cikin gidan sarautar,
Kafin kace kwabo Labari ya watsu cikin gidan, Uwar gidan Maimartaba ta turo Jakadiyar ta domin ta tabbatar sannan tasa a ka kira mata malaminta domin yayi mata binkice,
malamin yace”wannan yaron da a ka haifa ba zamu iya kashe shi ba sabuda yin haka zai janyo mana shiga hadari dani dake, amma abinda zamuyi masa guda daya ne zamu iya cire masa son mulki a cikin zuciyarsa sai dai yaga ana yi”
Tace”dama ai abinda nake so kenan kamar yadda ban hafi namiji ba haka bana so wata ta zo ta haifi namiji wanda zai gaji sarauta sabuda haka kawai a cire masa son mulki inda hali ma a sanya masa tsanar gidan nan ko a kada shi ina nufin ai masa kurciya kawai ya bar garin gaba daya”
“Zamuyi kokari iya iyawarmu ke dai duk abinda muka umarce ki kiyi kar ki fasa,yanzu dole zamuyi yanke-yanke kuma zamuyi kwanan bori in gari ya waye sai ayi sadake sadake zakiga abin mamaki”
Haka suka dinga dauki ba dadi kan zuwan Sarki Almansor duniya dan ganin sun sabauta shi tun yana yaro amma da yake yana cikin kariyar Allah hade da addu’ar iyaye babu abinda ya sameshi dan gane da mugun abun da suke masa kullum cigaba yakeyi har kawowa yau da ake masa maganar aure.