GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan kenan

Wayarshi ce tayi kara ya dauka yana dubawa. Maddibo2 sunan da ya gani kenan, a hankali ya daga yayi gyaran murya gami da cewa, ka shigo ne”?

Daga daya bangaran Maddibo yace”Eh gani a fada muna gaisawa da mai maimartaba yanzu zan shigo”

“Ok in bangaran Ummi”

“Shikkenan zan shigo yanzu dama ina so mu gaisa da ita wallahi”

“Sai ka shigo”
yafada yana kakarin kashe wayar

Ummi tace”kai da waye”

“Maddibo ne”

Murmushi tayi tace”ai shi babu ruwanshi wallahi na lura baya biyewa sauran “yan uwanshi, ya kan zo lokaci zuwa lokaci muna gaisawa”

“Shiyasa muke shiri dashi sosai Ummi kin san bana shiri da mutum munafiki”

“Nan Maddibo ya shigo ya zube gaban Ummi yana kwasar gaisuwa.Cikin sakin fuska Ummi ta amsa masa tana tambayarsa mutanan gida,yace” Ummi ni yau kwanana biyu da dawo wallahi gidan ma sai jiya na shiga”

“Ayya to masha Allah, in ka kara shiga a mika min gaisuwa gurin iyayen naka”

“Zasuji in sha Allah Ummi”

Nan suka mike tare Ummi tana ta shi musu albarka tana musu fatan dorewar zumuncinsu

Ban garan Sa suka nufa suna tafiya suna hira yayin da hadiman da suke harabar gurin suka dinga kawo gaisuwa Maddibo ne kawai yake amsawa shiko uban gayyar tafiya kawai yake kansa a kasa tamkar wanda ba ya son kallon rana,

Wasu hadaddun kujeru suka zauna wanda suke kewaye da kayattacan falon wanda ya sha shimfido irin na gidan sarauta ga wasu manya-manyan tuntu can kan wani tudu shima ya sha shimfidu masu kyau, kafin ka hau sai ka taka matattakala nan yake zama in zai huta in baya son fita waje

Maddibo yace”na lura sam baka iya tarbar baki ba wallahi baka ji yadda makogaro na ya bushe ba, a ko ruwa ka bani in sha”

Wani irin kallo yayi masa yana ya mutse fuska yace”in har nine zan kawo maka ruwa zaka kwana a nan”

Dariya yayi ya mike yace”masifaffe kawai kar Allah ya sa ka bani,ai ina da kafafu”

Tsaki yaja yana lumshe ido yace”kasan kana da kafafu meye na magana”
Sabuda ka rai namin hankali ni zan kawo maka ruwa ko kar Allah ya sa ka sha”

Maddibo yace”dan Allah kar kadame ni da masifa ka tsaya ka saurari abinda nazo dashi, Yafada yana zama kusa dashi yana kokarin bude ruwan goran sake hannunsa

Muje zuwa
[28/06, 06:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????33

_____Cikin Yanayin maganar shi yace”Allah yasa magana ce me muhumanci, kazo kana wani damuna matsalata tafi taka”

Ajiye robar ruwan yayi bayan ya gama sha yace” magana ce mai muhumanci mana, tun kafin inyi tafiya naso mu zauna muyi maganar Allah bai nufa ba sai yanzu”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba da cewa”akwai yarinyar da na hadu da ita wallahi a garin yawace-yawace na na resturant, kasan ni dai da son abinci mai dadi,kawai kwanaki Buba ya dauke ni muka shiga kasuwa gurin wani abokinshi, a lokacin yunwa duk ta ishe ni, dole tasa muka futo daga kasuwar domin mu samu abunda zamuci, kawai Buba yace a kwai gurun cin abinci mai kyau bakin kasuwar mu tsaya muci ba sai mun futa wajan gari ba.Tunda muka shiga gurin idona yayi tozali da yarinyar naji duk duniya babu macan da ta dace da ni kamarta, yanzu abinda nakeso da kai kawai ka shige min gaba gurin neman auranta domin nikam nayi mata”
Maddibo ya karashe maganar tashi yana sauke ajiyar zuciya, fuskarshi cike da farin ciki da annushuwa.

Wani irin tsaki Sarki! yaja yana wa Maddibo wani irin kallo yace”Lallai ka rai namin hankali wallahi , duk ka gama ya wace ya wacen ka kazo ka kare a gurin mai tuwo-tuwo sabuda tsabar ka rai na ni kazo kace in shige maka gaba, kar Allah yasa ka aure ta din”

Maddibo ya karyar da kai kamar wani maraya yace”Kasan kuwa yadda nake son yarinyar nan, wato na kawo maka kuka na kai da nake tunanin zaka sharemin hawaye ka mara min baya a kan al’amarin zaka sace min gwiwa, bai kamata kayi min haka ba, Alhaji”

“Kaga malam nifa ka fitar dani daga cikin wannan al’amarin haka kawai kai karasa wacce zaka ce kana so sai ” yar tallah a bakin kasuwa, kai ka san “yayan tallan nan ba tarbiya ce da su ba, ka sani ma ko tana biye-biyen maza kawai kaje ka kwasowa kanka datti da karzuwa, ka bata mana zuri’a kar ka kara sani a cikin wannan shirmen naka”
Cikin fusata!Madibbo ya dakatar da shi, yace”kayi karya kace wannan yarinyar tana da karzuwa ko karuwa ko kuma me zaman kanta,yarinya nutsatstsiya kamila, maitarbiya, sana’ar siyar da abinci da takeyi domin rufin asirin kanta ne sabuda na lura iyayenta basu wasu masu karfi bane, amma bari kaji duk izzar ka da takamar ka wannan yarinyar tafi ka, sabuda haka in kanaso mu shirya da kai kar ka kara ai bata min ita,sabuda zuciya ba zata iya jurewa ba”

Dariya Sarki!ya kama yi masa ba yana nunashi da hannu yace”amma ka bani kunya wallahi,yanzu a kan “yar towo-towo kake wannan tada jijiyar wuyar”?

Shareshi Maddibo yayi.

Har yanzu da murmushi a fuskarsa yayi gyaran murya gami da kara gyara kwanciya cikin ginshera yace” zanso in ga wannan yarinyar, da dai ban yi niyyar zuwa ba amma ganin yadda ka hakikance a kanta yasa dole zanje na ganta,yanzu yaushe ka shirya tafiyar”

Sakin fuska yayi ya juyo yana kallon Sa yace”ai a inda ke sakar kwata-kwata yarinyar taki amince min zuwa gidansu, yanzu ma da kyar na karbi numbar wayarta wallahi, amma dole insa a buncika min gidansu”

Shiru Sarki!yayi yana nazarin maganarsa ji yake tamkar ya tsinka masa mari,sabuda yadda ya bashi haushi,gashi bashi da halin magana yanzu zai hayayyako masa da masifa ya lura abokin nasa ya yi nisa sosai kan son yarinyar,sai kawai ya masa shiru yana ji yana magana bai tan ka ba.

“Kayi min shiru ina ta magana ni kadai”

“Me kakeso in ce maka yanzu”
yafada hankalinshi a kan wayarshi, ya cigaba da cewa “kace yarinyar taki baka dama kaga kenan bata son ka sabuda haka sai ka hakura kawai,domim wahalar da kanka zakayi gurin macan da bata son ka”

Shiru Maddibo yayi yana jin tsoran fada masa maganar dake bakinsa,da kyar dai ya samu yace”abinda zamuyi kawai muje can gurin inda take sana’ar tata, kafin musamu gidan nasu”

“Wannan ne kuma baza ayi dani ba,kome zakayi sai dai kayi,in ka damu ka sa a duba maka gidan iyayenta,ni kuma nayi maka alkwari zan maka jagora insha’Allah”
ya karashe maganar batare da ya kalle shi ba

“Ai kuwa dole gobe na me adress dinta ko ta halin kaka ne”

Tabe baki yayi yace” yace mubar maganar haka, muyi wata wallahi raina baci yakeyi dan dai babu yadda zanyi da kai ne”

Dole tasa Maddibo barin maganar badan zuciyarsa naso ba suka shiga wata hirar daban.
Can wayar Sarki! ta yi kara,a nutse ya duba fuskar wayar,Halisa ce

dauke kansa yayi daga kan wayar har ta katse, wani kiran yakara shigowa a karo na biyu,nan ma ta katse bai dauka ba, Maddibo yace”matsala ta da kai kenan sai ai ta kiranka a waya dan tsabar wulakaci kaki dagawa”

A ya mutse yace”kasan ko wacece ne”?

“Sai kafada”

“Wannan shashashar yarinyar ce Halisa”

Dariya Maddibo yasa yace”wai kai har yanzu baka sallama mata bane”?

“Tsaki! yaja cikin damuwa yace” Zaman da ka ganni inayi gurin Ummi zancan take maimaita min wai dole sai na aureta,babu yadda na iya dole in yi musu biyyaya amma kai kanka kasan yarinyar bata burgeni sabuda dabi’unta duk babu masu kyau”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button