GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Addu’a zakayi kasan dole ne muyi wa iyayenmu biyayya kan dukkanin abun da zasu zo mana dashi mutukar bai sabawa shari’a ba , amma ina ganin zaka iya da ita duk taurin kanta,tunda na lura ta sonka da yaw……..Kafin Maddibo ya rufe bakinshi daya daga cikin, bayin dake tsaye bakin kofar shiga falon yayi sallama,ya zube nan bakin kofa kai a kasa yace” ranka shidade Gimbiya Halisa ce tazo da jamar’arta”

Shiru yayi kawai yana latse-latse a waya

Maddibo yace”je ka shigo dasu”

Da sauri ya mike gami da cewa”angama ranka shidade, Allah ya taimeka ,yanzu zan cika umarninka”
ya fuce da sauri!

Maddibo ya kalleshi a fakaice ya na kunshe dariya yace”kaga mutuniyar taka ko muna zan canta sai gata tazo,gashi bakace komai ba”

Uffan! bai ce ba masa ba har Gimbiya Halisa suka shigo ita da masu take mata baya.

MUJE ZUWA
[29/06, 05:20] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????34

Cikin kasaita ta shigo falon kai tsaye in da yake zaune ta nufa,tana wata irin tafiya cike da izza da takama.
Nan jama’arta suka zube bakin kofa suna kwasar gaisuwa,daga bisani suka fuce daya bayan daya, Wani irin zama tayi kan kujerar tamkar zata shige jikinshi tace”Yayana ya kake? kwana biyu duk kasa hankalina ya tashi in na kira wayarka sai kaki amsa min, kasan ko yadda na damu da kai kuwa”
Fuskarshi a hade yace”ki matsa daga kusa dani mutukar kina so in saurare ki da abunda kikq zo dashi,kin san bana son wannan dabi’ar taki yana daya daga cikin abunda yasa sam ba kya burgeni”
Jikinta a sanyaye tace”wai me yasa kake fadamin duk maganar da tazo bakinka,yanzu me ye laifin wanda yace yana sonka,kasan fa ban rasa masoya ba”
Wani irin kallo yayi mata mai kama da harara cikin kasaita yace”ni ina ruwana da wasu masoyan ki kin san kina da masoyan zaki makale dole kice sai ni zaki aura,kije ki zabi daya daga cikin masoyan naki ki aura zai fi miki alkairi”

Shiru tayi na minti biyu tana tunani tasan halinshi mugun dan wulakanci ne da girman kai,ya zama dole ta lallabashi tunda dai ita ke nema dole ta kwantar da kai har Allah yasa burinta ya cika.
Kwantar da murya tayi tace”kayi hakuri insha Allah zan gyara,ni dai burina kawai ka dinga kulani kana daga waya ta idan na kira”
Shareta yayi ya cigaba da duba wayarsa.
Maddibo ta kalla tace”Ya Maddibo ka sanya baki mana wallahi ina jin tsoran wulakancin abokinka kullum da irin kalar da zai min gashi zuciya ta takasa hakura dashi.”

     Cikin dariya Maddibo yace"kar ki damu insha'Allah komai zai wuce,amma dole kiyi hakuri da halinshi domin ba ke kadai yake wa,so tun yanzu ya kamata ki gane wane irin namiji zaki aura"
Ajiyar ta sauke tace"bakaji yadda nakeji a cikin zuciya ta ba amma babu komai"

   Cikin dariya gami da barkwanci Maddibo ya kalli abokin nasa yace"mutumina kana ji fa ya kamata ka aje wayar nan ku fuskanci juna da mutuniyar kafin zuwan lokacin"

    Hankalinshi na kan wayar yace"ba kaji abunda tace min ba yanzu,wai tana da masoya,kajifa wani zance dan Allah, tasan tana da masoya me yasa ta nace min, "yar rainin hankali kawai"
  "Ni dai nace kayi hakuri"

Halisa tafada muryar ta kasa kasa
A ya mutse yace”in ban hakura dake ba yaya zanyi,ai dole ki kuyi iya magana,domin ni bana son shirme”
“to zan koya in sha Allah”
Nan dai ta lallabashi ya hakura suka cigaba da hira sama-sama, Maddibo yace”to ni zan wuce sai munyi magana a waya kafin gobe,insha Allah zan sa a duba min”

“Allah ya kaimu”
abinda yace kenan,Halisa tace”Ka gaida gida Maddibo a gaida su Mama”

Sosai Halisa ta dinga jansa da hira, wani ya amsa wani ya share ta,to inda sabo ta saba da haka,cikin zuciyarta tace a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe,yanzu ni burina kawai in ga na mallaka duk wulakancin ka zan jure


Maddibo da ne ga wazirin Sarki,inda Waziri ya kasance kani ga Maimarta ba Sarki Almustapah,Uwarsu daya ubansu daya, Waziri yana da “yaya goma sha shida, bakwai mata sauran duk maza ne, matanshi hudu ko wacce tana da ” yaya dashi, Waziri mutum ne shi mai bala’in san mulki sosai domin ji yakeyi tamkar ya kwace sarautar daga hannun dan uwanshi,kullum burinshi da kokarinshi yaya za’ayi taga sarautar ta dawo hannunshi, shida iyalinshi,shiyasa da yaga Maimartaba bai haifi da namiji ba,sai hankalinshi ya kwanta, yana jiran ranar da Maimartaba zai kwanta dama,ya gaje sarautar tunda shine namiji,cikin hukunci ubangiji Allah ya azurta Maimartaba da haihuwar Sarki!Almansor, in da ya zamo daya daya kwal cikin “yaya mata goma sha bakwai shi ya zama cikin na sha takwas, lokacin waziri kusan zaunce wa yayi,ya dinga shige sa fuce gurin ganin ya ga bayan Sarki!Almansor, Allah bai bashi iko ba,dan duk wani kulunboto da yake shiryawa sai ya koma kanshi ko kan iyalinshi,duk rabi” yayanshi maza sun zama “yan shaye-shaye in ka cire, Yusuf(Maddibo) duk ciki shine nutsatstse a cikinsu,shiyasa suka fi shiri da Sarki!Almansor kusan a tare suka yi makaranta komai iri daya suke sawa, duk inda daya yake dayan ma ba gurin, halayyarsu ce kawai bata zo daya ba,inda Sarki Almansor ya kasance mugun muskili wanda magana take masa wahala,sai ya kwana ya yini bai kula kowa ba har in dai ba kamawa tayi ba,shi kuwa Maddibo mugun saukin kai ne dashi gami da wasa da dariya, in ka ganshi sam baza kace yana da alaka da gidan sarauta ba,sabuda da kowa mu’amala yakeyi,babba da yaro,
Tsakaninsu basa boyewa juna sirri duk abunda ya dami daya daga cikinsu, tsakaninsu suke warware matsalar basa taba yadda maganar ta futa waje, shiyasa kai tsaye Maddibo shi ya fara kawowa maganar Balaraba,

 Kiranshi da suna Sarki! da mutane keyi na gida da jama'ar gari ya samo a sali ne daga gurin mahaifinshi,shine take kiranshi da sunan tun yana yaro in yaga yana wata irin tafiya cike da kasaita, ko cin abuncin sa abin kallo ne,balle yadda yake magana, Yadda Maimartaba ya fuskanta abin a jininsa yake, shi kanshi yaron ya san ya fishi kasaita, shine dalilin da yasa yake kiranshi da sunan, mutanan gida suka kama hade da jama'ar gari

    Halisa kuwa " yar kanwarsu ce wacce ta kasan ce autarsu wato Fulani Mariya maca ce mai mutukar kirki da sanin ya kamata sam bata kin talaka kullum cikin jawo jama'a take gidanta, tana can tana auran sarkin garin Wani gari jaja Amare, tun Halisa tana yarinya rikonta ya dawo hannun, me babban daki, wato Uwargidan Sarki, ta hada da "yayan ta ta rike kamar gaske, tun ta so warta take mutuwar son Sarki!Almansor, tun tanayi a boye har abu ya fito fili kowa ya fahimta,har maimartaba, nan kuwa Me babban daki ta tsaya kai da fata tace lallai dole ne a kulla wannan al'amarin domin dorewar zumunci, Maimarta ba ma ya nuna yaddarsa, a kan al'amarin, Shi kuma wanda ake domishi ya nuna bayaso da kyar dai mahaifiyarshi ta lallabashi ya dadda gudun bakin mutanan gari

Wannan shine kadan daga cikin tarihin abunda ya faru a baya

Cigaban Labari

Da asubah Maddibo yasa drevar ya futa dashi suka shiga kasuwar sha tambaya,can gefan titi yasa drevar yayi parking din motar, yana kwance cikin motar yana kallon masu shigowa cikin kasuwar duk da cewa safiya ce,
Wajan karfe takwas da rabi ya hangi Napep din Ashiru Balaraba na kokarin fitowa daga ciki yau tana cikin wata irin doguwar riga baka ” yar saudia rigar taji adon duwatsu sosai da sosai tayi nan nade kanta da veil kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi mai igiyoyi,sai ta kara tsayi sosai takalmin shima baki ne sosai kafarta tayi kyau a cikin talakmin hannuta rike da wayarta da wata “yar karamar pose ta tsaya suna magana da Ashiru

     Maddibo kuwa suma ne kawai bai yi ba lokacin da ya hangi fitowar ta sai ajiyar zuciya yake saukewa, yana wa Allah tasbihi cikin zuciyarsa yace" tabbas Allah ya aje baiwarsa gaskiya yarinyar ta hadu sosai,  dole maza su rika rikice wa a kanta, in da take burgeshi , kamun kai da rashin kwadayi gami da dogaro da kai shiyasa duk abunda a ka fada masa a kan ta yake kauda kai,sabuda yana ganin babu mahalukin da ya isa ya hanashi auranta, 
    Ya na can yana tunani Ashiru yaja Napep dinshi ya na kokarin hawa titi,can ya hangoshi, da sauri ya bawa drevar Umarnin bin bayanshi duk in da ya nufa.

Muje zuwa
[30/06, 04:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????34

Sosai Ashiru yake gudu a kan kwalta,kasancewar babu cinkoso sosai na ababan hawa, sauri yake shima ya isa gurin aikinsu, kawai sai yaga katuwar mota ta tari gabanshi, sai ya rage gudu, ya fara tafiya a hankali gabanshi yana faduwa!
Cikin sauri drevar dake jan Maddibo ya yi parking din motar gefan titi ya fito,yana dagawa Ashiru hannu.
Ashiru ya tsayar da Napep dinshi ya fito daga ciki duk hankalinshi a tashe,ganin mutum sanye da wasu manyan kaya ja da baki kanshi nade da wani katon abu,yana gani ya fahimci daga gidan sarauta ne,
Hannu ya bashi suka gaisa yace”Yallabai ne yake son yin magana da kai”

Jiki na rawa Ashiru ya bi bayan dravar suka karasa inda yayi parking din motar, Maddibo ya mika masa hannu fuskarsa a sake yace”barka da asubah”
Cikin dari-dari Ashiru ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna,kana yace”barka dai yallabai,fatan katashi lafiya”

“Lafiya kalau Abokina”
Maddibo yafada fuskarshi dauke da murmushi ya cigaba da cewa”in baza ka damu ba inaso in nemi alfarma a gurinka”
Jiki na kyarma Ashiru yace”babu damuwa Yallabai”

“Masha Allah, Menene alakar ka da Balaraba”?
Cikin rawar baki yace” babu wata alaka a tsakaninmu kawai ina kaita bakin kasuwa kullum”
“Ok shiga muje ka nuna min gidan su”
Maddibo yafada babu wata damuwa a tare dashi.
Ashiru duk ya rude yace”Yallabai Allah dai yasa ba wani abun tayi muku ba,sabuda na fahimci bata kaunar Sarki!Almansor, in wani abu tayi muku, ku gafarce ta dan Allah, Balaraba marainiya ce bata da uwa babu uba,kusan itace take daukar nauyin gidansu”
Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke, wani irin tausayin Balaraba yana ratsa zuciyarsa.
Yace”Babu laifin da tayi mana, alkairi ne zai kai ni gidansu,ka kwantar da hankalin ka”
Da kyar Ashiru ya je ya gyara parking a gefan titi kana ya sanya key ya kulle Napep din nasa, ya shiga motar suka kama hanya har unguwarsu Balaraba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button