GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai Maddibo yayi mamakin irin unguwar da Balaraban shi take rayuwa, wani irin lukuna masu dauke da dagwalan katoci ku ina kwata tabi hanya abun babu kyawun gani, hankalinshi bai kara tashi ba ma sai da yaga lokwan su Balaraba,mai tattare da tarkacan, kayan gwan-gwan ko ina gasu nan wasu a daure a buhun-huna wasu kuma a washe a hanya, in ban da wari babu abunda yake tashi a gurin,
Kasa shiga ciki yayi sosai ya tsaya daga baya, Ashiru yace”Yallabai ga gidan can, in da waccan budurwar take soya a wara to nan ne gidansu”
Yara ne suka fara taruwa a gurin suna kallon Maddibo,wasu na rugawa gida da gudu suna fada cewa ga Sarki yazo, ai tuni Yara suka cika gurin,kasancewar Safiya ce wasu duk sun fito domin tafiya makaranta, da sauri ya juya, ya bar gurin drvar shi ya bi bayanshi yana baza babbar riga, Ashiru ma ya mara musu baya,cikin zuciyarshi yana mamakin abunda yasa wannan mutumin yake neman gidansu Balaraba,
Maddibo ya shiga mota hankalinshi a tashe yana tunanin yadda za’ayi Sarki! ya iya shigowa wannan unguwar, shida yake da mutukar tsabta da mugun kyam-kyami! Wani lokacin in yaga abunda kyam-kyami, tsigar jikinshi ta dinga tashi kenan kuma kwana yake tsartar da yawu,ko ya yini bai ci abunci ba, yasan halinshi, sai dai kawai ya daukoshi suzo ba tare da yafada masa yadda yanayin gurin yake ba, kuma dole zuwan dare zasuyi, shawarar da ya yanke kenan cikin zuciyarsa.

Misalin karfe takwas shaura na dare, Maddibo na Shashen Sarki yana fama dashi ya tashi ya shirya, su tafi kar dare yayi, sai da ya gama yan garshi sannan ya mike ya shiga bedroom dinshi yayi wanka, ya fito a nutse ya tsaya gaban tafkeken dressing miroow dinshi wanda yake dauke da wasu mayuka masu tsada hade da manya-manya turarrika masu bala’in kamshi, da tsada.
Mai ya dauka yana shafawa a lafiyayyir fatarshi, sai sheki takeyi ko fatar wata macan albarka, Sarki!yana da kyau na ban mamaki ba lokaci guda kake ganin kyawunshi ba, sai ka yi kamar minti biyar kana kallonshi,a san nan ne zaka rinka ganin zallar kyawunshi yana bayyana wanda har kaji baka san ka dauke idanka da kanshi, Wata irin fata ce dashi chacolet, ga ta a murje ga wani lafiyyan gashi da yabi jikinshi ya kwanta baki sidik dashi, hatta da ya tsun kafar a kwai su a kwance,hakanan gefe da gefan fuskarshi, nan ma yabi ya kwanta, an yi masa wani irin gyaran fuska wanda yafito masa da dogan hancinsa hade da karamin bakinshi,kasan habarshi gashin yafi yawa ya barshi yayi tsayi kadan, hakan yayi masa mugun kyau, Sarki!Bashi da fara’a sosai, haka in baka sanshi ba zakayi zaton yana da girman kai, gami da wulakanci sabuda,dabi’ar shi, amma in kayi mu’amala dashi sau daya zaka gane mutum ne shi mai mutukar kirki gami da saukin hali, baya son rai ni ko kadan, shiyasa basa shiri da Halisa sabuda ya fuskan ci halinta,
Sarki!yana da wani abu da ya boye yake aikatawa babu wanda ya sani daga shi sai Ubangijinsa, cikin zuciyarsa baya son wannan abu da yakeyi, shiyasa kullum cikin rokan Allah yakeyi da ya sa ya dai na.

Wata Muguwar shadda ya dauko wagambari blue coulor anyi mata ire-iren dinkin da ake masa, wanda hausawa suke kira”yar shara, wani irin aiki akayiwa rigar da zare kalar shaddar, gaba da baya,in banda maiko babu abunda take, ya dauki agogo na zallar azurfa ya daura a hannunshi, bayan ya fesa turaranshi na ka’ida, kai tsaye inda takalmanshi suke jere ya nufa.
Anutse ya sanya wani takalmi shima mai bue colour duk jikinshi gashi, samanshi a rufe, duk dai ka na gani kasan na masu mulki ne,

   Cikin nutsuwa ya fiti falon inda Maddibo yake zaune yana sauraron fitowarshi, ya kalli agogon hannunshi yace"ka kyauta tun misalin karfe takwas da minti biyar ka shiga ciki, sai yanzu ka fito dubi time, fa"

Yafada yana nuna masa wani dan kareran agogo dake manne a bangon dakin, ya cigaba da cewa”yanzu har yaushe mukaje mu ka dawo,ka zauna kana wani feleke a daki sai kace wani mace”
Fuskarshi ya shafa yana sosa Gemunshi,cikin sigar Zolaya yace”mutumin da zashi zance gun budurwa ai dole ya kimtsa duk da dai ni a matsayin dan rakiya zanje, kuma mai gabatar da kai kaga dole in tsaya in shirya sosai domin kada budurwar taka ta rai na mu, duba ka ganka dan Allah, duk kabi ka wani susuce, ni da zan maka jagora ma watakila in fika mutumci a gurunta”
Da sauri Maddibo ya kalli jikinshi yana so yaga inda ya kakare wanda har zai sa Balaraba, tayi masa mummunan kallo,
Shi kanshi sai da ya bawa kanshi dariya, ganin jallabiya ce a jikinshi tun ta dazu da safe, shaf ya manta da ana wata kwalliya in za’aje gurin budurwa shi dai burinshi kawai yaje yaga mutuniyar shi,
Dariya yasa, sosai Sarki! yana taya shi, yacr”kasan Allah na manta da cewar wannan rigar ce a jikina,in banda ka tuna min,bari in shiga in canza kaya yanzu in fito”
Tsaki!Sarki ya ja yana kokarin zama kan kujera, yace”Wallahi har na ka gara inje in ga yarinya nan da ka rude a kanta,
ka dai yi sauri lokaci yana tafiya”
“Yanzu zan fito insha Allah”
Maddibo yafada yana kokarin shiga bedroom din domin shiryawa.

Comment
Vote and Share
[01/07, 17:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????35

Tsaf Maddibo ya fito cikin wani yadi mai santsi anyi masa wani irin dinki a gaban rigar ya dora falmaran ita ma duk jikinta surfani ne, ire-iren kayan Sarki! kenan, wannan ma da Maddibo ya sa sabbi ne dal,a ledarsu, kafarshi sany da takalmi kwatankwacin na kafar Sarki! yayi kyau babu laifi,amma bai kai Sarki!Almansor ba, haka suka fita daga farlon suna hira,cike da kasaita Sarki!yake tafiya, yayin da hadiman gurin suke zubewa suna kwasar gaisuwa.
Direba shi ne ya taso da sauri ya nufi wata katuwar mota cikin jerin motocin dake aje a gurin a je motocin ya je ya bude yana sauraron karasowar su,
Zubewa yayi kasa hannushi a dunkule yace”ranka shi dade barka da fitowa,Allah yaja zamanin ka, Sarki!me jiran gado”
“Barka kadai Haladu, ya aiki”?
Yafada yana kokarin shiga motar,

” Alhamdulilahi ranka ya dade”
Haladu ya fada yana kallon Maddibo yace”barka da fitowa yallabai”
Maddibo ya mika masa hannu cikin barkwanci da wasa da dariya suka gaisa,sannan ya shiga mota ya zauna kusa da mutumin nashi,

  Haladu ya kunna mota cikin nutsuwa suka fita daga gidan,

  Hira suke irin ta abokansu wanda sukai yi karatu tare, Maddibo yace"kaga Harisu Galadima yaran shi uku kasan da mata biyu ya fara,jiya munyi waya dashi yake ce min daya amaryar tashi ma ciki gareta, zai na hudu, shi kuwa Yakuba Buba" dama kasan ya riga kowa aure yanzu in banyi karya ba sai in ce maka zai haifi yara biyar,duk da cewa matarshi daya"

  A nutse yace"ka rabu da Harisu Galadima wannan ai mayen mata ne,ko ka manta lokacin muna skul yadda yakeyi in yaga mace,shege ji yakeyi kamar ya bita yayi mata fyade, in bai yi mace biyu ba me zai yi, muna nan da kai zakaji ance maka ya kara ta uku"
Dariya sukayi duk su biyun har da tafawa.

Maddibo ya gyara zama yana fuskantar Sarki! yace”kai ai ni in na samu wannan yarinyar nagama dacewa wallahi,nake gaya maka yarinyar ta cika mace ta ko wanne fanni, bazan iya yi mata kishiya ba”
Wani irin kallo yayi masa yace”yar towo-towo din ce kake wani cewa ta hada komai na mace wanda,kake so, kar fa ka mance cewar yarinyar “yar bakin kasuwa ce”
Shan kunu Maddibo yayi yace”Yasin zanyi maka rashin mutumci, wallahi Balaraba tafi karfin wulakanci a gurinka,kar ka kara ce mata “Yar bakin kasuwa”

 Dariya ya sa har sai da dimful dinshi ya fito yace"Wallahi har ka tuna min da wata   mara kunyar yarinya kwanakin baya, da sukayi saukar al'kurani,makarantar tasu ta kawo saukar gaban sarki, Sunanta Balaraba, bazan taba mantawa da kallon banzan da tayi min ba, kai in ka gani sai kayi mamaki, lokacin kana can Swiziland, abun ya bani mamaki, sosai"
 Murmushi Maddibo yayi yace"nafada maka duk me wannan sunan ba karamar mace bace, mybe ka nuna mata halinka ne shiyasa ta nuna maka nasu halin"

  Tabe baki yayi yana dan sosa sumar kanshi wanda hakan ya zame masa jiki in dai zai yi magana sai yw sosa kanshi yace"me ya dameni da ita,kasan ni mata basa gabana,wallahi, kai ni fa zan iya kare rayuwata batare da wata mace ba"

“Wannan kuma mahaukaci zaka fadawa wanda bai san wanene kai ba”

Dariya yasa ya dan sosa kai yace”Wallahi nake gaya maka yarinyar nan wai a na cewa gani na fito, ita ta riga kowa tashi domin ta ganni ina lure da ita, daga baya kuma ta fara yimin kallon banza,sai kace wani sa’an ta”
“Maddibo ya ce” ka ishemu da zan wata yarinya ko ka na ciki ne, dan ban taba ganin ka ka zauna zance wata ba,ko Halisa bata da wannan matsayin”
“Kai me zanyi da wannan yarinyar” yafada yana gyara fuska ya cigaba da cewa”kawai dai inai maka kwatance da ita ne, Allah yasa taka Balarabar ba irin halinsu daya da waccan din ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button