GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

  "Zamuje ka ganta ne ai sam tawa daban take da kowa"

“Ok Shikkenan, Allah yasa”

Nan suka cigaba da hira har suka karasa Unguwarsu Balaraba,

Maddibo ya kalli Haladu Direba yace"yi parking dai-dai can"
da sauri Haladu yayi parking din motar inda a ka umarce shi,

A nutse ya dago kanshi yana bin unguwar da kallo, Kallon Maddibi yayi yace”wannan wace irin unguwa ce ka kawo mu, guri duk tarkace da kazanta, ko ina kango,da kwatoci, kasan bazan fito ba wallahi,kaje kasa a kira maka ita”

  Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke  domin yasan dole za suyi haka dashi, yace"kake maganar kango duk gidajan jama'a ne, duk babu wani kango a cikin nan unguwar, wannan tarkacen kuma da kake gani yaran unguwar ne suke sana'ar gwan-gwan"

  Ya mutse fuska yayi yace"gaskiya Maddibo baka da kirki, yanzu da kasan a irin wannan unguwar budurwar taka take ka gayyoto ni,kamar baka san halayyata ba, kai yanzu ya dace"kazo ka nemi matar aure a irin wannan guri"?
"Kaga bana son ka bata min rai dan Allah, kafito mu shiga ga lukon gidansu can,yanzu duhun dare ne babu wanda zai gane ka"

  "Billahillazi, babu inda zanje nayi iya yi na, in ka damu kai ka futa ka kurawo ta sai mu gaisa,amma bazan fita daga motar nan ba,haka kawai kwalabe su fasa min kafafu,kan wata shashashar budurwar ka wai ita Balaraba"

ya karashe maganar yana gyara kwanciya cikin motar babu abunda ya dame shi.

  Sanin halin taurin kai irin na Sarki! yasa Maddibo jan tsaki ya bude motar ya fita sabuda yasab duk nacin da zai masa bazai fito ba kamar yadda ya fada 

Dariya Sarki! yasa bayan fitar Maddibo daga cikin motar yace”duk Abinda zakayi kayi amma bazan fita in cuci kai na ba”

Haladu Direba ya fito ya tsaya a bakin motar yana kalle-kalle, ganin fitowar Maddibo, yasa ya karaso Maddibo yace”ka tsaya kawai zan fito zan shiga gurin can”

“A fito lafiya yallabai”

Haladu ya koma bakin mota ya tsaya,

Ganin motar gidan Sarauta yasa yara suka fara, taruwa

Comment
Vote and Share
[02/07, 14:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

          ∆∆∆∆∆∆
           _*GIMBIYA BALARABA*_
         ∆∆∆∆∆∆
                ????????????????????????????????





             _*Na*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir rahamanir rahim

????36

Kasancewar babu wutar nepa a unguwar shiyasa yara basu ankara ba sosai, dabi’ar yaran cikin gari kenan in suka ga bak’o cikin mota zasu zo su tsaitsaya suna kallo wasunsu kuwa har zuwa suke su dinga taba motar suna dariya suna rugawa gida da gudu,Sarki!yana kwance cikin motar yana bin unguwar da kallo, cikin zuciyarsa yace”yanzu haka jama’ar dake cikinta suke rayuwa, wasu gidajan gasu nan duk babu kofofi, wasunsu an sanya musu buhu an kare sabuda kar a gano cikin gidan, a fili yace”da gani gurin zai yi sauro sabuda tarin shirgi da datti da kazanta, dole a kawowa unguwar a gaji,
Shi kadai yake wannan sake-saken cikin zuciyarsa, gefe guda kuma ya zaku yaga wannan yarinya da Maddibo ya makance a kanta.

A nutse Maddibo ya kutsa kansa cikin lungun su Balaraba wanda yake dauke da tarkace iri-iri haka ya dinga tsallake kananun langa-langa da robibi har ya karasa kofar gidansu Balaraba,inda yara da matasa suke tsaye kan Shamsiyya wacce take ta faman soya awara da kwai,
Gefe guda ya ja ya tsaya ya kira wani yaro wanda yake tsaye kan Shamsiyya yana jira ta sallame shi,
“Kai Salmanu ungo awarar taka, in sallame ka in huta”
Shamsiyya ce ta dago tana wa Salmanu magana,kawai sai ta ganshi ya nufi gurin wani mutum can gefe, fitilar wayarta ta kunna ta haske fuskar Maddibo tana wani ya mutse fuska tace”wancan wanene a tsaye a can ne”
Da Sauri Walidi dake tsugune kusa da ita yana zukar wani abu a tsumma ya mike yana wani ciccije baki yace”yana ina ne yanzu in farde masa ciki”!
“Gashi can naga ya kira Salmanu ko uban me zai yi masa oho! je ka gani”

Walidi na tafiya yana hada hanya ya nufi inda Maddibo ke tsaye tare da Salmanu

Matasan dake tsaye a gurin ne suka rufa masa baya suma cikin rashin tarbiya suke cewa”bari muje muga wane dan iska ne,yanzu mu kaddamar masa”!

Maddibo yana hangen zuwansu gurinsa sai ya gyara tsayuwarsa, har suka karaso gurin,suka tare Salmanu, cikin tsageranci Walidi yace”kai ina zaka ne? me wancan guy yace maka”?

Jiki na rawa Salmanu yace”Cewa yayi in kira masa Gimbiya ta gidanku”

“Kai!! dan uwarka wacece Gimbiya a gidanmu”?
Walidi yafada yana dukan kafadar yaron.

” Balaraba fa yake nufi”
Salmanu yafada jikinsa na rawa domin wani irin tsoran Walidi yake ji
Cikin tsawa!Walidi yace “kai! kauce daga nan dan uwarka ko in yaga ka, yanzunan”

Da gudu Salmanu ya bar gurin,

Cikin wata irin tafiya Walidi ya karasa kusa da maddibo ya tsaya yana masa wani irin kallo, duk da cewa a kwai duhu a gurin bai hana shi ganin irin kallon da yake masa ba.

“Kai waye ya baka izinin shigo mana lungu ehe,! mufa duk inda mukaga bakuwar fuska babu yadda, gurin wace Gimbiya kazo a lungun nan”
Dariya ce taso takama Maddibo ganin yadda yaron yake wani ciccije baki yana wani tangadi tamkar zai kai masa duka, gashi sai warin ganye suke dukkaninsu, girgiza kai yayi gami da gyara tsayuwa yace”Sannuku “yan samari, ni bak’on alkairi ku kwantar da hankalin ku, Gurin Balaraba nazo”

Walidi ya gyara tsayuwar gami da zira hannu cikin aljuhun wandonsa ya fito da wata wayarsa wacce duk ta sha dauri ka da kyaure sabuda tsabar ganin duniya,ya kunna fitar wayar cikin sigar rashin mutumci ya dallare fuskar Maddibo da ita,
Sai wayar ta kusa faduwa sabuda razana da yayi, ganin Fuskar Sarki!Almansor da yayi, sabuda Maddibo suna dan yanayin kama da Sarki!amma ba sosai ba, sai dai duk inda jininka yake za’a ga kama ko yaya ne”
Bakinshi na rawa yace”ranka ya dade, kace Balaraba kake son gani”?

“Kwarai kuwa”
Maddibo yafada fuskarshi a sake,

Washe baki Walidi yayi yace”ai kuwa bata dade da dawowa daga kasuwa ba, wallahi ai yaya ta ce, bari in shiga in kira maka ita”

Fuska a sake Maddibo yace”Ok nagode Abokina, kace”mata Yusuf ne”

“E ai insha Allahu zan yi mata bayani”
Walidi yafada gami da juyawa da sauri!
Maddibo yace”jimana”

Walidi ya dawo da sauri ya zube kasa bai sani ba,
Maddibo yace mike tsaye mana Abokina”
Cikin yake Walidi ya mike tsaye sam ya kasa hada ido da Maddibo sabuda tsabar kwarjin da yayi masa,
Hannu ya zira cikin aljihu ya fito da kudi daurin “ya dari-dari guda uku ya mika masa, Hannu na kyarma Walidi ya karba yana ta zabga godiya,
Gyaran murya yayi yace” ka dauki dauri daya ku raba da kai da abokanka, sauran dauri biyu ka bawa mutanan gida”
Godiya kawai Walidi yake bakinshi yaki rufuwa,sauran matasan dake gurin suka sanya ihu!suka bi bayan Walidi da gudu,
Shamsiyya ta dago kanta tana kallonsu har suka karaso gurin basu bar ihun murna ba, ranta a bace! tace”kai wannan wane irin iskanc……kafin ta karasa maganar tata Walidi yazo yayi fatali da kaskon suyar awarar wanda yake cike taf da mai gami da awara cikin kwai, da sauri! ta dauke kafafunta tana kurma ihu! sabuda yadda mai duk ya zuba a kafafunta, kafin ta dawo hayyacin ta Walidi ya daki! Katuwar rubar dake cike taf!da awara an soya ta gwanin sha’awa, duk ta watse a gurin cikin kasa da tarkacan kazanta, ihu! ta kurma ta mike da sauri tayi kan Walidi tana dura masa ashar! ba ta sani ba ta tsumbula kafarta cikin kaskon awarar wanda ke dauke da ragowar mai da bai karasa zubewa ba, durkushewa tayi a gurin tana rike kafarata sosai ta kone, a kafafun da hannunta guda.

Cikin Ihu!da hargowa Walidi yq shiga gidan, sauran matasan dake biye dashi a baya suna tayashi,
Lantana ta mike da sauri! har sai da zanin jikinta ya sabule ya fadi kasa tayi saura daga ita sai dan tofi, Cikin gigita tace”shikkenan Walidi ya jawo mana musiba ooo ni Lantana!
Uwa! ma fitowa tayi daga dakinta kanta babu ko dankwali,gabanta yana mugun faduwa tace”kai Walidi menene kake mana ihu! ne”?

Banza yayi musu ya nufi dakin Balaraba da gudu, yana fadin” Aunty Balaraba Gimbiya ta gidan sarki! ki fito kinyi babban kamu, daga yau nine zan zama yaronki, Allah ya yanke min wahala”

Tana zaune kan dadduma hannuta rike da carbi idar da sallahr ta kenan, taji shi yafado mata daki yana mata sambatu,

Jin abunda Walidi yake fada yasa Lantana, bankada labulen dakin Balaraba da sauri ta shiga har tana kokarin faduwa, tace”kai Walidu me kunne na yaji kana fada ne”?

Muje zuwa

Comment
Vote and Share
[03/07, 14:29] +234 808 996 5176: ????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button