GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

   ∆∆∆∆∆∆   
    _*GIMBIYA BALARABA*_
    ∆∆∆∆∆∆
             ????????????????????????????????



         _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir-rahamanir-rahim

????37

Almuminu,Almuhaiminu ya Allah

Wani kallo Walidi yayi wa Lantana irin nasu na marasa tarbiya yace”kinga Lantana duk wani zancan bakin ciki da hassada ya kare, ni daga yau wallahi na dai na biye muku ku cuce ni, Balaraba dai Allah ya rufa mata asiri,dan Sarkin garin nan shine yazo gurinta gashi can a waje”
Lantana bata bari ta karasa jin zancan Walidi ba ta nufi hanyar waje tamkar zata kifa sabuda sauri,
Iya ce tayi sauri ta tari gabanta tace”ina zakije haka Lantana dubi jikinki babu zani daka ke sai dan tofi”

“So nake inje in ganewa idona zancan da Walidi yazo dashi”
Lantana ta karashe maganar tamkar wata zautacciya
Sadiya Matar Kawu tasa dariya tace”yanzu ke Lantana idan a kace ki futa haka sai ki futa,to in kin futa waje me zakiyi”?

Iya ta riko hannuta ta dawo da ita tsakar gida ta zaunar da ita kan tabarmar ta,sannan ta leka dakin Balaraba tace”me kike yi baki futo ba kije kiga ni ko waye”

A nutse tace”Iya babu inda zani ni domin ba muyi da wani zai zo gurina ba,sai dai idan wata Balarabar a ke nufi bani ba”

Walidi kamar ya dora hannu a ka yace”dan girman Allah aunty Balaraba kizo kije ku gaisa,kin san dai bazan miki karya ba, wallahi da gaske nake”

Shamsiyya ce ta shigo cikin gidan tana durawa Walidi zagi ta Uwa ta Uba, sai jan kafa takeyi, Mahaifiyar su ta gani tsaye bakin rijiya tayi shiru, kamar babu ita a gurin, cikin jin radadin zafin ciwo tace”Wallahi Uwa!yau sai nayiwa Walidi rashin mutumci, kinga yadda ya kona ni, yayi miki barna,gashi can duk ya zubar miki da awarar gaba daya”

Wani uban zagi Uwa!ta kurma tana kwalawa Walidi kira wanda yake dakin Balaraba yana tw zabga mata magiya kan ta taje gurin Maddibo.

“Wai me yake a cikin dakin waccan mutsiyaciyar ko tafara koya masa iskanci ne”
Shamsiyya tafada tana daga muryar ta dan Balarabar ta ji ta.

“Rabu da shashasha kwadayayye kawai,makarya cin banza da wofi wai dan Sarki ne yazo zance gurinta shine yazo yana yiwa mutane shirme”

“Kan Ubancan”!
Shamsiyya ta kurma wani uban zagi,ta cigaba da cewa” shine ya kona min jiki a kan waccan,wallahi bazan yadda ba,sai nayi musu wulakanci, wane dan Sarki kawai yace Farkanta ne ya biyo bayan ta meye ba mu sani ba”
ta karashe maganar tana buga cinyar ta

Lantada dake zaune kurum tun dazu bata ce uffan! ba tace”shiyasa ai nake so in futa in ci masa mutumci in koreshi, sabuda nasan babu wani mutum mai mutumci da zai zo gurin wannan lalatacciyar sai lalatacce, O ni Lantana,yanzu in da gaske ne dan Sarki ne yake son yarinyat nan ina zan sa kai na”
ta karashe maganar har da rike haba!
Sadiya matar Kawu tace”Ko wane irin miji Balaraba zata aura, duk mulkinsa da dukiyarsa gami da nasabar sa, Lantana baki isa ki hana abunda Ubangiji ya tsara a kan ta ba,Balaraba dai ta zama murucin kan dotse wallahi,bakin cikinku babu in da zashi a kanta”
Kuka Lantana tasa har da fyace majina tace”Ni kikewa rashin kunya Sadiya har kina kokarin zagina tsofai-tsofai da ni”

Uwa!ta tabe baki gami da cewa”muna furci dai dodo ya kanci meshi,ehe!! ai gashinan ke da kike daure mata gindi tana kokarin zaginki ,gaskiya naji dadin wannan abu”
Sadiya matar Kawu dakinta ta shige tace”gaskiya ce ba kyaso Lantana dole in fada miki”

Ganin Nacin! da Walidi yake mata ya ki karewa yasa ta mikewa tsaya har yanzu tana cikin hijab dinta har kasa ta kalleshi gami da cewa”muje shikkenan ai sai ka sakar min mara in sake”
Walidi ya washe baki gami da cewa”Yawwa matar Manya,aike yanzu kin zama kadara a gidan nan, ba irinsu wadancan “yan iskan ba”
Yana sane ya fada da karfi dan Shamsiyya taji,aiko ta ji shi, yana futowa ta dinga zaginsa, tana hadawa da Balarabar, shiru kawai Balaraba tayi mata,shi kuwa Walidi kallonta yayi shekeke!yace”mahaukaciya kawai a haka zaku shegu “yan iska, kawai” Da gudu Shamsiyya tabishi tana zaginsa, kamar wata “yar maguzawa, Balaraba tayi saurin kaucewa tabata hanya, tana mamakin ta tamkar wata dabba haka take ganin Shamsiyya sam!bata da nutsuwa balle kamun kai.
Tuni Walidi ya fuce daga gidan, sai ta tsaya bakin kofar gidan tana kalloshi yana tsaye can kusa Maddibo,ta dinga kurma masa zagi babu ji babu gani, sai da tayi mai isar ta sannan ta juya ta koma cikin gidan tana jan kafarta suka ci karo da Balaraba tana kokarin futowa,
Kaucewa tayi ta bata hanya a karo na biyu,ganin tana nema ta bangaje ta, tsayawa tayi ta na mata wani dan banzan kallo tace” Haka zaki kare,karuwa kawai”
Murmushi Balaraba tayi kawai ta raba ta gefenta ta wuce tabar ta tsaye a gurin,tana cizon ya tsa taso ta tanka mata suyi kokawa kamar yadda suka saba shekarun baya da suka wuce.

Can gefe ta hango Walidi tsaye da Wani mutum a tsaye,sabuda haka kai tsaye inda suke ta nufa cikin nutsuwa.

Tunda ta fito ya nemi nutsuwarsa ya rasa har sai da Walidi ya fuskanta yayi saurin waiwayawa yana kallon bayanshi sai yaga Balaraba, washe baki yayi yace”Yallabai dama nace maka yanzu zata futo wallahi”
Fuska a sake Maddibo yace”nagode Abokina”
hannu ya mika masa,Walidi ya saurin mika masa nasa sukayi musabaha yana mamakin mugun sauki kai irin na Mutumin,
Tun kafin takaraso ta fahimci Yusuf ne, (dan anace) sunan da tasa masa kenan, sam bata taba zaton zai nemi gidansu ba, lallai ta yadda yana sonta da gaskiya kamar yadda yake fada,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa gurin.
Walidi yayi saurin wuce yana fadin “Yallabai a sauka lafiya, mungode sosai”
Hannu kawai Maddibo ya daga masa,duk ya rasa nutsuwarsa,dalilin futowar Mutuniyar tashi,

Anutse ta gaida shi, ya amsa yana mata wani kayataccan murmushi

“Ya akai ka kawo kanka gidanmu”?
kai tsaye tayi masa wannan tambayar.

Murmushi ne dauke a fuskarsa yace” ke kin dauka son da nake miki na gaibu ne? duk inda kike zan biki wannan shine soyayyar gaskiya”
Murmushi ne a kwance a kayatacciyar fuskarta, tace”gaskiya kam yau na yadda da kai dari bisa dari”

Wani dadi gami da farin ciki ne suke ratsa zuciyar Maddibo,jin abunda tace, sam bai yi tunanin zai shawo kanta da wuri haka ba,
“Alhamdulillahi Gimbiya ta, yau ranar farin ciki ce a gurina,nagode da tarbar da kika yimin”

Shiru kawai tayi tana sakar masa murmushi mai kayatarwa.
Gyaran murya yayi yana kallonta yace”tare muke da dan uwana kuma abokina aminina, yana can cikin mota, kizo muje ku gaisa dashi”

Wani irin kallo Balaraba tayi masa, tace”kamar yaya inzo muje mu gaisa,shi bai isa yazo nan din ba kamar yadda kazo har sai an bishi inda yake”
A nutse yace”Mutumin nawa ne akwai tsirfa, baya son hayaniya, kinga yanayin unguwar taku”
ya karashe maganar yana son boye mata abunda yake da akwai,dan a zahirin gaskiya bazai iya futowa ya fada mata kyamkyamin ne ya hanashi zuwa inda take.
Shiru tayi tana nazari, a cikin zuciyarta, a yanzu Maddibo ya wuce wulakanci a gurinta,mutumin da ya tako yazo har inda take duk da tarin arzikin da yake dashi,ita sam bata san yana da alaka da sarauta ba tunda bai taba fada mata ba,wannan dalilin ne kawai zai sa taje har inda abokinsa su gaisa kamar yadda ya fada din, baya ga haka kuwa, bai isa ta taka taje har inda yake ba.

A nutse ta kalli Maddibo tace”Muje kawai amma fa sabuda darajar ka, zani har mu gaisa dashi dan gaskiya ni babu wani mahalukin zai nuna min isa da mulki, idan ba mahalaccina ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button