GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Comment
Vote and Share
[06/07, 13:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????

   ∆∆∆∆∆∆   
    _*GIMBIYA BALARABA*_
    ∆∆∆∆∆∆
             ????????????????????????????????





         _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Real Bintu Batula????

????39

Hannu kawai ya dagawa Buba Dreba da sauri ya karaso gurin, Cikin nutsuwa ya mai da idonshi kan Maddibo yace”Ni zan wuce, naga alamar baka da ranar tafiya, ka kawoni gurin yarinyar mara tarbiyya tana neman ta zageni”

Cikin daga murya Balaraba tace,”to in na zageka me zaka yimin karkari kasa a daure ni to ka dade baka sa an daureni ba,kuma zakasan wanda ka tofawa miyau dinka,wallahi sai na rama kaji na rantse”
Cikin hayaniya take fadar maganar,hawaye yana kokarin zubo mata,
Babu zato taji wani sabon yawu a fuskarta ya kara tofa mata a karo na biyu, baice komai ba ya shige mota Buba Direba ya shiga ya kunna mota suka bace daga gurin.

Maddibo kamar ya dora hannu aka domin takaici da Sarki! ya kunsa masa, ya dauko shi domin yazo ya gyara masa lamarinsa gurin Balaraba, yazo ya bata daya goma bata gyaru ba,yanzu yaya zaiyi?
Cikin muguwar kunya gami da jin nauyi ya kalli Balaraba tana goge hawayen bak’in ciki,tana sane ta matse kukan batayi a gabansa ba,sabuda kar yaga gazawar ta, sai bayan ya tafi hawaye ya balle mata,kamar me tunda take a duniya babu mahalukin da ya taba yi mata tozarci irin na yau,dole ne ma sai ta rama wulakanci da mutumin nan yayi mata.
“Kiyi hakuri dan girman Allah,Balaraba, hakan ba halinshi bane, dana san abunda zai faru a tsakanin ku da ban gayyato shi ba,dama da yaya ya yarda zaizo din,kiyi hakuri dole zan dauki mataki akan haka,sabuda ke kanki kiba da daraja da mukami cikin zuciyata”
Fuskarta goge da hannuwanta duk biyun,fuskarta a hade tace” Ya kuke dashi,ma’ana menene alakar ka da gidan Sarki”?

Tsayuwa ya gyara sosai yana fuskantar ta, yace”Ni Sunana Yusuf kamar yadda kika sani, amma Mutan gida na kirana da Maddibo asali sunan kakanmu a gare ni shiyasa suke kirana da haka, Sarki Almustaph Wan mahaifina ne, Waziru Zayyanu”
Da sauri Balaraba ta dago kai tana kallonsa cikin mamaki!
Ya cigaba da cewa”Sarki! Almansor dan Uwana ne na jini kuma aminina abokina tare mukai karatu dashi tare muke rufewa mu kashe, amma halin kowan daga cikinmu daban yake da na dan uwansa, yana da saukin kai sosai in ka fuskance ki, amma bashi da hakuri ko kadan in ka tabashi, Mugun muskiline,sosai shiyasa nayi mamakin abunda ya hadaku haka kuke fadawa junanku bak’aken maganganu, da alama s kwai abunda ya taba hadaku a baya”

Shiru tayi na minti biyu ta kalleshi a nutse tace”kana kallonshi yayi min wulakanci har da tofa min miyau bakace komai ba, dama ka dauko shine domin yazo ya wulakantani ko, babu komai, Nagode”
Tana gama fadar maganarta ta kama hanya ta barshi tsaye a gurin,tafiya take kamar zata kifa jin zuciyarta take kamar zata kone sabuda tsabar turiri da take mata, da kyar ta kai kanta gidansu,
Maddibo ko binta da kallo yayi har ta bace masa, jikinsa a sanyaye ya futo da waya ya kira daya daga cikin Direbobin cikin gidan Maimartaba Sarki Almustaph ya fada masa unguwar da yake,yace yazo yanzu-yanzu ya dauke shi
Yana nan a tsaye a gurin, Sallau Direba ya karaso gurin Lokacin goma da rabi na dare,da sauri ya bude motar ya fito ya budewa Maddibo ya shiga suka bar unguwar,
Salihu Yana tukin mota yana mamakin me ya kawo Maddibo irin wannan unguwar, ya gaza hakuri ya yace”ranka shi dade nace Allah yasa lafiya, ko wani abune ya faru a unguwar ne”

“Lafiya kalau, nazo gurin wani abokina ne”

“Masha Allah Yallabai dafatan ka same shi lafiya”?

” Alhmdulilahi”
Maddibo ya fada yana jin zuciyarsa babu dadi,Sarki!
ya cuce shi, yanzu yaya zai yi ya shawon kan Balaraba,

Yana zaune a ka tafaran Falonshi shi kadai kwal, in banda karar AC babu abunda kakeji, yana zaune a wata kujera me cin mutum daya daga shi sai wando 3Quetar kafarshi daya kan daya kana kallon irin zaman da yayi kasan na masu mulki ne, Sigari yake zuka yana lumshe ido,zuciyarsa in banda zafi da turiri babu abunda take,jira kawai yake Maddibo ya shigo suyi ko wacce-wacce,domin yana ji yana gani bazai bari ya auri yarinya kamar wannan mara tarbiya ba babu yadda za’ayi ta shigo ta bata musu zuri’a.

Comment
Vote and Share
[07/07, 12:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????????????
∆∆∆∆∆∆
GIMBIYA BALARABA
∆∆∆∆∆∆
????????????????????????????????

         _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE

MARUBCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDICATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

®REAL BINTU BATULA????

????40

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Maddibo ne ya shigo falon cikin sallama,amma kana kallon fuskarsa kasan yana cikin bacin rai, kujerar dake fuskantar sa ya zauna sosai ya murtuke fuskarsa, yace” yace “Yanzu abunda kayi mun ka kyauta kenan, haka mukayi da kai ? a kan zakaje ka bata min lamarina a gurin yarinyar nan”

Hannu ya daga masa a fusace! ya mike zaune sosai ya gyara zamansa, yana kashe guntuwar tabar dake hannunshi cikin wani karamin plete wanda ke aje kan wani karamin teble dake gabanshi, a ya mutse yace “me nayi maka, zaka zo kana min wani shan kunu,ni ban yi magana ba,kai ne zakayi magana, haka kawai ina zama kazo ka dauke ni la kaini an ci mun mutunci, wannan bayi ba ne”
Ya karashe maganar yana huci!

Kasa Maddibo yayi da muryar shi ganin yadda Sarki! ya ke hayaniya, yasan halin bakar zuciyarsa yanzu sai ayi batacciya shi dashi,shiyasa ya kwantar da kai, dama kuma (Annabi muhammadu slw) yafada cewa idan mutum biyu na fada,to daya yayi saurin saukar da zuciyarsa gudun abunda zai je ya dawo,idan duk zucoyoyi biyu suka dauki zafi a lokaci guda,to shedan zai samu abunda yakeso,a kansu, Allah kasa mu dace

“Yanzu a matsayin ka na namiji mai hankali a kanta ya kamata ka biye mata duk abunda tayi, wannan ni kawai ka ciwa mutumci wallahi”

“Ok ” Ok wato ni ba kaga abunda tayi min ba,yariya karama tana nema ta zageni, abunda babu wanda ya taba yimin shi a rayuwa ta ita tayi min sabuda samun gurin kazo ka nai min wata maganar banza, Ok zan dauki mataki akanta mai tsauri wallahi sai inga yadda za’ayi ka aureta”

“Duk abunda zakace sai dai kace” auran yarinyar nan kamar nayi nagama,kuma duk abunda tayi maka kai ne ka jawo tayi maka, me ye ruwanka da sana’arta da har zaka dunga kiranta da “yar towo-towo wannan ai cin fuska ne, kuma a sanina da kai nasan wannan dabi’ar ba taka bace,kawai ka ara ka yafa ne”

A harzuke! Yace”an kira ta da “yar towo-towo din karya akai mata ne, in tayi wasa ma da ” yar tasha za’a kira ta watarana”

Zare ido! Maddibo yayi cikin mamaki yace”wai me yake damunka ne, kai me yarinyar nan tayi maka da zafi haka”?

Tsaki! yayi ya koma ya kwanta cikin kujera yana lumshe ido zuciyarsa sai zafi take

Maddibo yace”dan Allah kafada min meye alakar ka da yarinyar nan Balaraba naga alama kun san juna,ganin yadda kuka shaida juna da wuri”

Minti biyar bece komai ba,farlon yayi tsit! bakajin komai sai karar AC kadan-kadan,

Cikin Ginshera yace”Babu wani abu da ya hadani da ita, hasali ma ban taba ganinta ba,sai ranar saukar su, wacce sukayi ta wattanin baya da suka wuce, wannan shine ganina da ita na farko, tun daga ranar ban kara dora idona a kanta ba sai yau”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button