GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru da taji yasa ta kara kwantar da murya tace”ka ga babu abunda nake yanzu nima a kwance nake,bacci yaki zuwa sabuda tunanin ka,ko inzo ne, in tayaka bacci”

“Gyaran Murya yayi yana lumshe ido yace” Ke wai yaushe zakiyi hankali ne “? Shiru tayi gabanta yana faduwa sabuda tasan halin dizginsa

Tsaki!yaja kasa-kasa ya cigaba da cewa
“wannan shirmen da kike sam baya burge ni, ni nafison ki kama kanki, ki zama cikakkiyar mace, sabuda rashin hankali ke yanzu in nace kizo sai kizo,Ok toum in kinzo kiyi min me”?
Yafada cikin sigar tambaya

Shiru tayi kawai takasa cewa komai

” Ba magana nake miki ba”
Yafada a fusace! sabuda ya tsani ya na magana ana shareshi

Bakinta na rawa tace”yi hakuri,ni ai na dauka, babu komai tunda auran juna zamuyi”

Jin abunda tace kawai sai ya kashe wayar ranshi a bace, yace”Shashashar Yarinya kawai, aje wayar yayi gefan shi, ya lumshe ido yana tasbihi cikin zuciyar shi, har bacci ya dauke shi

Comment
Vote and Share
[09/07, 13:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????

            _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

????43

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Wannan, mafarkin da yake ne, ya tasheshi firgigit! ya mike zaune sai hada uban gumi yake, na yau mafarkin yafi na kullum domin kukan da wannan matashiyar yariyar take yafi na ko yaushe, tunda yake ganinsu cikin mafarkin bai ta ba yi musu magana sai yau Allah ya bashi iko, bayan Mahaifiyar yarinyar ta tafi ganin kukan da matashiyar yariyar take yasa ya bude baki yace”tayi shiru, tabarwa Allah komai zai yi mata magani, duk da maganar da yayi hakan bai sa tayi shiru ba, sai ya mike da niyar tafiya sabuda cikin mafarkin kukan ta ya dameshi yana taba masa zuciya, wannan karon ma hannunta ya rike cikin nasa yana janta tana turjewa, sai ya daka mata wata irin tsawa, wacce tasa ta bude ido da sauri, tana kallonshi, fuskar da ya gani ce ta sashi furgita ya farka daga baccin hankalinshi a tashe,

Ya jima Zaune a gefan gado yana mamakin yariyar da yagi cikin mafarkinsa, sosai yake mamakin meye alakar shi da wannan mara kunyar yarinyar wato budurwar Maddibo, dama ita ce yake gani cikin mafarkin tsawon shekara biyar, Allah bai bashi ikon ganin fuskar ta ba sai yau, kusan minti ashirin yana zaune yana saka wa da kwancewa, nan Maddobo ya shigo ya same shi, hannushi dafe da kai, sai kace wani mai ciwon kai,

Kanshi ya tsaya yana gyara link din rigarshi yace”Lafiya tun dazu nake kiran wayarka shiru”

“Bacci nake”
abunda yace kenan

Cikin Nazari Maddibo yace”Bacci fa kace”?

dago kansa yayi yana masa wani irin kallo, a ya mutse yace”Karya nake kenen”

Murmushi Maddibo yayi yace”mai da wukar malam, ni zani gurin Gimbiya in ci abunci, ko injiraka ne”

A hasale yace”wallahi zamuyi fada dakai, kar ka kara sakoni cikin maganar ka da wannan yarinyar in kana son kanka da arziki, kai daka ga zaka iya kaje kayi, amma ni, kasan nafi karfin inci kazantar ta”

Daga kafada Maddibo yayi alamun abunda ya fada bai dame shi ba,yace”Ni kam zanci har da side kwano, sai na dawo”

Banza yayi masa har ya fuce daga dakin.

Maddibo na futa wasu bayi suka shigo Maza biyu mata biyu

Wani irin kallo ya watsa musu cikin tsawa yace”wane shegen ne yace ku shigo min daki,”?

Kasa sukayi da kansu dukkaninsu

Cikin tsawa ya cigaba da cewa”ni kuturo ne da komai sai kuce sai kunyi min, nace bana so, nace bana so, amma sabuda tsabar naci! kullum sai kunshigo min daki da sassafe! kufuce ku bani guri”
yafada cikin tsawa!

Zubewa sukai gabansa, kamar wasu masu neman gafara, wannan abun ya kara tunzura masa zuciya, a zafafe! yace”me kuma zanyi muku,, bakuji abunda nace ba?

Mariya ita ce baiwar shi wacce take kula da gyaran bangaran shi da da kai masa abunci da daukewa in ya kammala goge-goge da share-share, ita ce tace
“Ranka ya dade don Allah kayi hakuri ka bari munai maka hidima a shashen ka, domin aikin mu ne,hakan ka gafarce mu, ranka ya dade, zamu maka gyare-gyare ne”

Wani kallo ya watsa mata, wanda yasa ta sunkuyar da kai kasa, babu shiri,domin idanunsa duka ya ware mata,tunda take dashi ba ta taba ganin ya bude idonshi haka ba, kullum a lumshe suke, ko kallon ka yake, baya budewa sosai kasa-kasa yake kallo.

Yace”kece Sarkin iyayi ko, wacce tafi kowa iyawa, kowa yayi shiru zaki damu mutane da magiya,Ok ku fuce min a daki, tukkuna inyi abunda zanyi in futa,sai kuyi abunda zakuyi”
Ya karashe maganar yana hararasu,sai kace su sukai masa laifi

Daya bayan daya suka fuce daga dakin, suka tsaitsaya a falo suna gulmarsa, kasa-kasa Mariya tace”yau da alama a kwai abunda yake damun Yallabai wannan masifa haka”

Wacce take kusa da ita tace”kuma hakan ba halinsa bane,shi dai kyaleshi da muskilanci gami da shariya”

Mariya tace”gaskiya akwai wani abu dake damunshi”
Haka dai sukayi cirko-cirko a falo suna magana kasa-kasa, gefe kuma suna jiram fitowarsa,domin su fara aikinsu

Yana kokarin mikewa ne daya daga cikin wayoyinshi ta hau gyara, ko kallonta bai yi ba balle ya dauka, toilet ya nufa, cikin zuciyarsa sai mita yake, ya tsani kamarshi azo ace sai an masa komai, yana da lafiya da kuzari Allah ya hore masa sai ya tsaya an masa bauta, shi sai yake ganin wannan cutar kai ne, a rayuwar shi ya tsani yaga ana wani jin tsoransa,kamar ayi masa sujjada, kamar dai yadda suke masa, shiyasa kullum cikin yi musu tsawa!yake, baya son wannan rawar jikin da suke masa, Sarki!bayason raini ko kadan, shiyasa abunda Balaraba tayi masa ya kasa bacewa a zuciyarsa,dalili kuwa shine tunda yake a rayuwarsa babu mahalukin da ya taba yi mishi abunda tayi

Toilet dinshi abun kallo ne, sosai in ka shiga baza kayi sha’awar futowa ba,domin har wani sanyi-sanyi yake,duk abunda mutum yake bukata a kwai a ciki

Jaccuzi kuwa har biyu ne a ciki, sabuda girman toilet din, a nutse ya shiga ya hada sabulai na mussaman yayi wanka, ya futo ya nannade jikinshi da towol ya dauki karami yana goge kanshi,

Kai tsaye dressing mirrow dinshi ya nufa, ya tsaya jikinshi a fara shafa mayukanshi masu kyau da tsada, ya taje sumarshi sai kyalli take,itama ya sanya mata mayuka, Kwantaccan gashin dake fuskarshi yake gyarawa sosai ya gyara Sajanshi ya tsaida gemunshi iya inda yake so, sai fuskar tafito tayi wani mugun kyau da haske,kalar fatarshi ta fito sosai,annuri ne kawai yake futa a fuskarshi,

Wayarshi ce take kara alamun kira,bai saurare ta ba,sai da ya futo da kayan da zai sanya,sannan ya zauna gefan gadon ya dauki wayar yana dubawa a nutse.

Khalifa sunan da ya gani yana yawo kan fuskar wayar,

Khalifa dai yaron Waziri ne, kani ga Maddibo, kenan yaron bashi da kunya ko kadan shiyasa basa shiri da Sarki! ko kadan yanzu ma yayi mamakin ganin kiranshi, sai da yagama yangarshi sannan ya dauko,

“Assalamu alaikum”

Daga daya bangaran Khalifa yace”Yallabai barka da asubah”

“Barka kadai, Khalifa ya kake”?

” Lafiya yallabai, dama Baba Waziri ne yace kazo yana neman ka”

Shiru yayi na tsawon minti uku,kana yace”Ok ya fita fada ko yana gida”?

“Yana gida”

“Ganinan zuwa”
Yafada yana kokarin kashe wayar,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button