GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Raurau rau idanunin Balaraba yayi jin Furucin Maimartaba sai ta fara kokarin mayar da kwallar da tataro a kwarmin idonta domin bata son zubowarta anan.

Tana tsaye masu hotona da Video sai daukarta a keyi.

Mai gabatarwa ya Mike yaje yatari lasiqa yace”Allah yaja da ran sarki mai Adalci wannan yarinyar marainiyace Ubanta ya rasu shekuru goma da suka wuce ita kanta batayi wayo ba Mahaifiyarta ma haka yanzu shekarunta uku da rasuwa sai ita da qqnnenta Guda biyu”

Mai martaba yayi gyaran Murya cike da tausayin Balaraba”yace Allah ya jikansu da Rahama to yanzu muna bukatar waliyyinta yafito domin ya karbar mata Abinda muka tanadar mata”

Diri Diri Maigabatarwa yayi yana waige wai ko zaiga Sallau ,Amma ko Alamarsa bai gani ba cikin mutuwar jiki yakara tarar Lasifiqa yace Allah shi taimaki sarki sarakuna ae wakilin nata bai samu damar halartar taron ba”

Girgiza kai Maimarta yayi yana Nazarin wani Abu kana yagara Murya A nutse yace”ina bukatar Sarki!! Yarima Almansor yafito na wakiltashi ga wannan yarinyar mai tarin Albarka

Yana zaune a hakimce yaji wannan Furucin na Maimartaba sai yaji faduwar gaba kadan Amma kwata kwata Fuskarshi bata nuna ba ,shifa ba kowane kare da doki yake so Maimartaba ya riqa Alaqantashi dashi ba yanzu fisabillahi inashi ina jera kafada da kafada da wancan “yar gidan fukara’u wacce ba’asan Matsayin taba.

A nutse ya mike cike da qasai ta gami da izza kamar yadda ya zame masa jiki ya karasa kusa da da maimartaba gami da mika gaisuwa domin yana mutukar girmama Mahaifin nashi sosai da sosai baya son bacin ranshi ko kadan shine yasa ma duk Abinda maimarta ba yace baya musawa ko dako Abin baiyi masa ba,

Cikin nutsuwa Mai Martaba ya mike tsaye wani bafade biye dashi a bayanshi riqe da tarin mukulai da wasu takkadu cikin Ambulan,

Maimartaba ya karbi Mukuuli guda biyu ya mika Sarki!! daya na gida ne da yake ginasu can bayan gari sabida irin haka daya kuma na wani katafaran shago ne cikin wata kasuwa datayi shura cikin jahar tasu nan ma ya mika mata a karo na biyu ko wanne da takkadunshi na mallaka hade da sa hannun shi maimartaba.

A nutse Sarki! Ya karba gami da karasawa in da take tsaye gabanta na dukan Uku Uku,

Da sauri wani bafade ya karaso gurin ya kara lasifiqa bakin Sarki! Domin yasan zaiyi magana dole.

Gyaran Murya yayi yana duba takkadar farko,

Ya Mika mata Cikin Wani irin Voice yace Maimartaba Sarki Almustapah ya Mallakawa Balaraba Ayuba tanko daya daga cikin gidajensa na bayan gari halak malak sakamakon kokarinta da tayi gurin saukar Alku’ani maigirma Allah yaja da ran sarki Yakara maka Lafiya Balaraba na godiya,yafada yana Dan ya mutse fuskarsa kadan gami da mika Mata takkadun ,Akwain guri ya dauki kabbara gami da kirari ga sarki Almustaph Masu photo da vidio suka fara Aikinsu ,duk wani Masoyin Balaraba a gurin ya tayata murna makiyanta kuwa tamkar su mutu.
Sallau wanda ke can rabe jikin katanga ji yake kamar yaje ya cinnawa kanshi wuta ya huta da wannan bakin ciki

Ta sanya hannu biyu ta karba fuskarta cike da walwala Amma taki yadda ko kadan ta kalli Fuskarsa haka masu photo suka riqa daukarsu.

Kamar yadda ya mika mata takkadar farko haka ya mika mata tabiyu hade da Dan mukkulin shagon da yin bayani domin kowa ya shaida

Zubewa Sallau yayi gumi ya tsinke masa yana mamakin yanzu Balaraba ce ta mallaki shago cikin kasuwar sha tambaya Wanda shiga wannan kasuwar sai wane da wane domin kasuwa ce ta masu kudi ,nuffashin sa ya riqa fita sama sama tamkar zai bar gangar jikinshi tsabar bakin ciki ae bai gama dawowa daga dimuwar da ya shiga ba yajiyo muryar Sarki!! Yace “Ni Almansor Almustapah na baiwa Balaraba Ayuba tanko kujarar Maka sakamakon hazakarta da kokarin ta muna fatan sauran dalibai zasu kara zage damtse gurin jajircewa da bada himma a kan karatu muna fatan wata shekarar daliban dazasu sauke Alku’ani mai girma su ninka na yanzu.

Yana gama fadar haka ya Fara kokarin barin gurin cikin ginshera wacce tazame masa jiki cikin kasaita yaje ya zauna gurin zamanshi yana kallon kowa daidai.

Gefe guda yana mamakin yarinyar da Girman kanta ganin ko kallon in da yake taqiyi ko dame take taqama oho!

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA

YARO DA KUDI

GIMBIYA BALARABA

????????????????✍????
[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????writteng by
Binta Umar
~MAMAN ABDUL WAHABU~

~MRS AHAMAD GWADABE~

WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU
08089965176

????5

Daya bayan daya dalibai suka riqa fitowa suna karbar Allonsu hannun maimartaba kamar yadda yayiwa Balaraba kyauta haka ya riqa yiwa kowa daidai da Matsayinshi.

Sulaiman Ahamad shine yasamu kyauta kwatankwacin ta Balaraba nan shima Sarki! Almansor ya bashi kyautar kujerar maka kamar yadda yabawa Balaraba,

Guri ya hautsine kowa yana taya nashi murna gami da karbar Allon ana sanya Albarka ,nan kaf dalibain da malamai gami da iyayen yara suka jero reras gaban sarki masu photo suka riqa daukarsu domin tarihi .

Sarki ya jiro wasu takkadu ya mikwa shugaban Makarantar wato Arrama Malam Idiris yace” ni Almustaph na malakawa wannan Makaranta Filina dake hayin diga halak malak kuma Na dauki nauyin ginashi da izinin Allah muna fatan zaku kara zage damtse gurin kula da tarbiyar yara da basu ilimi mai amfani.

Allahu Akubar Allahu Akubar Allahu Akubar

Guri ya hautsine da Akabbar Malam idirs ya zube gaban sarki tamkar zaifashe da kuka sabida dadi sai zanba godiya yakeyi

Kankace komai guri ya karade da busa irin ta gidan sarauta mai taken jinjina game sarki.

Sarki Almustaph ya mike da Alama gida Ai shiga Aikuwa fadawa suka baza manyan riguna domin take masa baya.

Dama A Al’ada sai sarki ya tashi sannan kowa yake tashi sabida girmamawa,

Mikewa Sarki!! Yayi tare da tawagarshi domin bin bayan Mahaifinshi ,wan an Dan kanzagin bafaden ya soma Aikinshi na banbadanci har ya Manta da gargadinsa na dazu

Busar da ake masa daban take da wacce a kewa maimartaba domin kanaji tasa yadda take tafiya slow tana tafiya da Yanayinshi na taqama!!

Gyara kintsi Dan sarki jikan sarki nan gani nan bari dawisu sarkin Ado dawinsun ma dole ya saurara Maka Farar Aniya Farar zuciya Farar Alkyabba Dan gado masu sarautar gaskiya arziqinku bai rufe muku ido ba Allah dai ja da kwana Dan sarki jikan sarki!

Tuni guri ya kacame Kiowa yanaso yayi ido hudu da wannan Dan sarki da’aketa wasa shi haka Mussaman Matan dake gurin da masu saukar da “yan kallo.

Balaraba na gefe duk tururrubin da’ake gurin gami da hayaniyar baisa ta zuwa gurin da yake kokarin wucewa ba sai zabga tsaki takeyi yana kallon bushira sai faman kutsawa take wai lallai sai ta ganshi.

Gefe can taja ta tsaya domin yadda a ke bangajeta gashi Sam Sam bata son hayaniya da jira da tana da damar tafiya da tayi tafiyarta wallahi domin kwata kwata bata son batawa kanta lokaci sanin da tayi cewar kannanta nacan na jiranta a gida,

To ganin yadda makarantar ta karramata a matsayinta na daliba ta farko yasa bataso ta watsa musu kasa a ido

Duk a zaton ta Sulaiman Ahamad shine na farko ganin yadda yake da kokari domin ko musa bakace shine yake cinyewa Amma Abin Mamaki sai taji sunanta a farko ,Tabbas ta yadda da kanta tunda Ita kanta tasan tana da masifar kokari domin wani sa’in itakewa “yan ajinsu kari idan malami bai shigo ba ita dai kyaleta da rashin kunyarta da gadara gami da takama gashi ita kuma ba “yar gidan kowa ba!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button