GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mamaki yake kiran me Waziri yake masa Allah yasa alkairi ne,

Tsaf ya shirya cikin wani uban yadin filtex me ruwan sararin samaniya, an mishi dinki irin na sarauta sosai yayi masa kyau, kafarshi saye da takalmi irin nasu shima kalar kayan jikinshi, wayoyin shi ya diba ya futa daga dakin, suna tsaye sukaji futowarsa, da sauri sukayi kasa da kansu, ko kallonsu bai yi ba ya fuce daga falo, Wasu bayi maza su biyu suna tsaye bakin kofa,suka zube suna kwasar gaisuwa, yana tafiya yake amsawa, suka mike da sauri suka rufa masa baya

Duk wasu bayin dake kaiwa da kawowa a filin gurin tsayawa sukai suna gaidashi, har sai da ya wuce sannan kowa ya koma bakin aikinsa,

Ikon Allah Sarauta da mulki sai mai shi????

Comment
Vote and Share
[10/07, 05:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????

            _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

????44

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Waziri na zaune a falo tare da uwar gidanshi, Hajiya Rahamatu, wato mahaifiyar su Modibbo, wacce suke kira da Mama, macace mai mutukar kirki da maida dan wani nata, tana da kara da kawaici,da kauda kai a kan abunda babu ruwanta, shiyasa kullum cikin tsawatar da “yayanta take, a kan su lura da duniya mussaman in taga suna jiji da kai da nuna su ” yayan sarauta ne, kullum takance musu,babu wanda Allah ya ware tsakanin tsakin bayinsa,me mulki ko mara mulki talaka ko me kudi,sai wanda yafi bauta masa.
Wani lokacin idan Waziri yana wani abun na son zuciya takan iya bakin kokarinta gurin ganin ta hanashi, haka zasuyi ta rigima dashi, Amaryar shi ce,halinsu yazo daya,duk wasu abubuwan da yake yi ita take ingizashi,yake da girmanshi da komai,bashi da gaskiya kullum cikin shirya manakisa yake.

A nutse Sarki! yayi sallama cikin falo,Mama ta amsa masa cikin sakin fuska, tana gyara masa gurin zama, fuskar sa ya saki sosai ya je ya zauna kasan kafafun ta kanshi a kasa yace”barka da asubah Mama”

Kanshi ta shafa tace”barka kadai, Almansor,yau sharabon da in sanya ka a idona”

Sosa kansa yayi irin na sabo yace”Yace Mama Ayi hakuri, a gafarce ni”

Dariya tayi kawai tace”ai nasan hali baka son mutane dama”

“Mama a dane wannan”
yafada yana sosa kansa

Wani irin kallo Waziri yayi masa yace”kema ai da neman magana kike wannan yaron da baya son jama’a ko kin manta da halinshi, wai kuma a haka akeso a bashi mulki”

Shiru Mama tayi jin abunda mijin nata yace, tasan yanzu zai kauce hanya

Girgiza kai kawai Sarki! yayi ya dago kanshi fuskarshi babu yabo babu fallasa yace”Khalifa ya kirani a waya dazu yace kana nema”

“Kwarai kuwa”
Waziri yafada yana gyara zamansa kan kujera

“To Masha Allah, ina sauraron ka”

Mikewa Mama tayi ta bar gurin dan ta barsu su sake suyi maganarsu amma tana mamakin abunda zai sa Waziri kiran Sarki! sabuda tasan basa jituwa ko kadan.

“Wato kana jina ko”?

“ina jin ka”
Yafada kai tsaye!

“Kasan abokina Maimarta ba Sarkin Yalwa, ko? Cikin nutsuwa yace” Eh nasanshi ” “To shine ya ke neman alfarma a gurina da gurinka, a kan yana so ka auri yarinyar shi Azima, ta nuna tana sonka, to shine na nake neman alfarma a gurinka, a matsayi na na Mahaifinka, kar ka bani kunya, a gurin abokina kaje ka nemi yarinyar nan, insha Allahu baka da matsala da ita, yarinya ce nutsatstsiya”

Kanshi na kasa tsawon minti biyar bece komai ba, daga bisani ya dago kanshi, a nutse yace” Zanyi tunani akai”

“Zakayi tunani akai”?
Waziri ya maimaita maganar da yayi cikin sigar tambaya,

“Fuskarshi ya hade sosai ya dago kanshi yana kallon Waziri, yace” Allah ya taimake ka, wannan maganar da kazo min da ita tayi min tsauri dayawa dole ne inyi nazari a kanta, kabani nan da kwana biyu,duk abunda na yanke zan maka magana”

Kwantar da kai Waziri yayi sabuda yana nema, yace”A’a baza muyi haka da kai ba, Magajin Sarki, ka fada min kawai yanzu, wannan abun me sauki ne, a gurinka, domin kasan ko ba yau ba, dole zaka hada mata hudu,sabuda muna saka ran zaka gaji kujerar mahaifin ka”

Wadannan maganganun da Waziri yayi sun bashi mutukar mamaki, wai yau da bakinshi yake kiranshi da Magajin Sarki, lallai akwai wani abu dake zuciyar shi wanda yake boye wa, Amma sabuda ya kyaleshi ya tafi yasa yace”Shikkenan na amunce da, Allah ya shige mana gaba,

Murmushi Waziri yayi yace”Allah yayi maka albarka Magajin Sarki, in sha Allahu zakaji dadin auran yarinyar, kaga sai a hada da Halisa ko”

“Duk abunda kuka yanke dai-dai ne a gurina”
yafada yana kokarin mikewa da niyar tafiya

Hannu ya mika masa suka yi sallama, Waziri sai shi masa albarka yakeyi, sai murna yake kamar ya ari baki, nan Sarki! ya barshi, cikin farin cikin amuncewar sa


Balaraba kuwa kwana tayi tana kuka a ranar kamar ranta zai futa, taji ciwon wulakancin da Sarki! yayi mata, wai ita yake kira “yar towo-towo ” yar bakin kasuwa, tayi kukan rashin iyaye, tasan duk rashin su ne ya jawo mata wannan wulakancin, gashi tana shigowa gidan Lantana ta tare ta tana zagi, wai sai ta futo mata da kudin da ta samo, in ba haka ba, zata shiga gidan ba, nan su Shamsiyya suka dinga ihu! suna dariya, tafi minti ashirin a tsaye a soro sai da Walidi ya shigo gidan, ya ga abunda yake faruwa,ya zage Lantana tas! har Uwa bai bari ba duk ya hada ya dinga dura musu ashar, ya rike hannun Balaraba suka shiga ciki, Su Sadiya da Usuman suna zaune, a tsakiyar dakin sai kuka sukeyi, babu haske,ga uban sauro sai tashi yake, a dakin, haka ta shiga takamasu ta rungume tana kuka, har sukayi bacci, kwata-kwata zaman gidan ya ishe ta, dole ne ta samawa kanta ma futa.
Sam, bata yi wani baccin arziki ba, da ta rufe ido sai ta hango shi lokacin da yake tofa mata miyau din bakinshi, bata jin bacin ran abunda Lantana tayi kamar wannan, sabuda tasaba, dashi,tunani kawai take, wace irin hanya zata bi ta rama abunda yai mata,

Tunda tayi sallahr asubah bata koma ba, tana zsune kan abun sallah tana lazimi, bacci yana fuxgar ta, kadan-kadan, ta jiyo muryar Lantana tana kwala mata kira,
“Balaraba, ke Balaraba”
Lantana tafada tana dukan kofar dakin kamar zata karya ta.

Tana jin ta tayi shiru har sai da ta ha’da carbi sannan ta mike a nutse taje ta bude kofar,

Lantana tayi mata wani kaskantaccan kallo, tace”au! kwana kikayi kina kuka naga idanunki sunyi jajazir!” tafada tana rike ha6a cikin mamaki!

“Me zanyi miki ki ke buga min kofa”
tafada kamar bata san abunda ya kawo ta ba,

“Au! tambaya ta kike me zaki min”?
Lantana tafada cikin mamaki! ” to kudin gasara zaki bani” ta karashe maganar tana gyara daurin zaninta

“Lantana yau bani da kudi, sai gobe”

“Baki isa ba wallahi”
Tafada cikin hayaniya da masifa

Rantsuwar da tayi ya mutukar bawa Balaraba,mamaki, ita ko yau batayi niyya bayar wa za taga inda wanda ya isa yasa ta bayar

Comment
Vote and Share
[11/07, 05:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????

            _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

Zamani Writes Association????????

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button