GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

????45

Bisimillahir-rahamanir-rahim

Kawu Sallau ne ya futo daga daki, hannushi rike da wata karamar redio yana kokarin dai-dai ta tasha, dake safiya ce , yana so ya saurari labarai, kofar dakin Balaraba ya nufa inda Lantana take tsaye tana karewa Balaraba zagi, tace”Jiya kinfi awa daya a waje,kuma ance me mota ne mutumin da yazo gurin ki amma sabuda kin raina mana hankali shine zakice baza ki bamu kudin gasara ba to ko sai kin bayar sannan zaki futa daga gidanan kinji na gaya miki”
Jin abunda Lantana tace yasa Sallau saurin karasowa gurin yana rage karar redio dake hannushi yace”Lantana wai me yake faruwa ne, tun daga daki nake jiyo hayaniyar ki”

Gyara tsawuyar ta tayi tace”Yo in banda sharri irin na wannan yarinyar, da tsabar mugun abu, wai yau bata da kudin gasara wanda take bamu muna siya muna karyawa dashi, jiya fa Wani me mota ne yazo zance gurinta, ta dade a waje,kafin ta shigo gida”

Walidi ne ya bude kofar bandaki ya fito,hannushi rike da bota, da alama sai yanzu zai yi sallar asubah, a jiye botar yayi nan bakin rijiya ya nufi gurin da suke, ya kalli Lantana yana wani ciccije baki yace” Yawa! kike fa Lantana, Ehh wannan da kuke gani fa tafi karfin wulakanci a gurinku, kune mutsiya ta daga ke har ita Uwa!din, kudin gasarar banza da wofi, kullum da take baku kudin ai babu wanda ya taba gode mata, sai dai kullum ku bita da zagi! To wallahi kukayi wasa zan k’ona kudin da aka bani in baku, banzaye fattararru kawai!!
ya karashe maganar yana wani tangadi kamar zai buge Lantanar, da ssuri ta matsa gefe guda, Cikin mamaki tace”Ni kake zagi ko Walidi”

“Kinga Lantana”!
Walidi yafada yana nuna ta da yatsa
Ya cigaba da cewa” nifa a kan wannan zan iya kaddamar miki, gwara ki kauce kawai, Eh! ni dai na fada miki”

Shiru Lantana tayi tana zare ido, shi kuwa Sallau ko a jikinsa, duk irin rashin mutumci da Walidi yakewa mahaifiyar sa, a cewarsa ai itace ta jawo wa kanta,
Washe baki yayi yana kallon Balaraba yace” “yar Albarka, sannu da kokari, kinji ko ki cigaba da hakuri damu, ni dai nasan ban miki wani laifi ba, sabuda haka zan tafi gurin me shayi, yanzu”
Balaraba ta gane munufar sa, sabuda haka sai tace” Kawu kai ma yau sai dai kayi hakuri, domin bani da kudin da zan baka yau da gobe kayan Allah”

Murtuke fuska yayi, ya hau zuba mata ruwan ashar, yace”wato nima karyar zakiyi min kenan, in da gaske kike ki matsa in shiga cikin dakin naki in duba kaji ni da ja’irar yarinya ko”
Ya karashe maganar yana gyara babbar rigar shi

“Haba Baba, wannan ba yi bane, kai yanzu a kace ka shiga dakin sai ka shiga,gaskiya kai Lusari ne wallahi” Hahahahaha
Walidi ya karashe maganar yana kyalkyala dariya, ya zira hannu cikin aljihun wandon dake jikinshi wanda yayi dau’da sosai duk jirwaye, gudar dubu daya ya futo da ita ya mika masa yana cigaba da dariya kamar wani mahaukaci, ganin Walidi ya futo da Dubu daya sabuwa dal! ya bawa Sallau yasa jikin Lantana kyarma, washe baki tayi ta matso kusa da Walidi, tace”Ashe da gaske ka keyi yaron nan, ai nace dama jarina yayi kasa, kaga yau sai in shiga kasuwa in siyo kuli-kuli, Allah dai yayi maka albarka d’an nan

Walidi yasa dariya yana nuna Lantana da hannunshi yace”ke dai Lantana in kika ga kudi duk sai ki shiririce, dube ki don Allah”
yafada yana dariya, ya cigaba da cewa”wannan kudin sun futo daga gurin mijin Balaraba insha’Allah in kin kwantar da kai,kullum zan dinga baki dari biyu, yanzu dai ga dubu daya ke ma sai kira jari kamar yadda kika fada,

Warce wa tayi daga hannusa, tana washe baki tace”da gaske kake dan nan”?

“Da gaske nake mana,ke dai ki dai na takurawa Balaraba a gidan nan”

“Yo ni dama ai bana takura mata,sai kaje ka nemi masu takura mata, to kaj! in kaji ina mata fada to fadan gaskiya ne, ko ba haka bane Balaraba”
tafada tana kallonta
Girgiza kai kawai Balaraba tayi tana kokarin komawa daki

Jin hayaniya tayi yawa a tsakar gida yasa Uwa! futowa daga dakinta, yau ta makara bata tashi da wuri ba dalili jiya sun dade ita dasu Shamsiyya,da Maburuka suna lissafin kudi, har Sallau ya dawo daga mahadarsu ya taddasu suna lissafi,yayi-yayi su bashi dari biyu Uwa! ta hana shi “yayan nashi kuwa sai dariya suke masa, Shamsiyya ce me cewa” Baba zuciyar ka ta mutu, wallahi Allah ya wadaran Halinka” nan ya mike ya barsu ya shige daki yana ta zaginsu,su kuma sai dariya suke masa.

Ganin kudi tayi hannun mijinta cikin mamaki, ta bi bayanshi ganin yana kokarin futa daga gidan, yasa ta kwala masa kira”Sallau”

Da sauri ya juyo yana hararar ta, ta karaso gurin kanta babu dankwali daga ita sai daurin kirji tace”me nake gani a hannun ka kamar gudar dubu daya”

Da sauri ya zira ta a aljuhu yace”Kwarai kuwa menene”?

“Kamar yaya menene, a gidan ubanwa ka samu kudi,haka kuma kake kokarin futa batare da ka bamu kudin karin kummalo ba,tunda Allah yasa ka samu”

Banza yayi mata kawai ya kama hanya zai futa a karo na biyu, da sauri ta je ta tari gabanshi, tana hura hanci tace”karya kake wallahi, ka bani ko yanzu in tara maka mutane,domin na gaji da muguntar ka, wato sai da kasamu kudin kaje kaci banza kaci wofi,to baza ta sabuba,wai bunda a ruwa”
Tafada tana dukan cinyar ta

Sanin halin jarabar Uwa!yasa Sallau kallo inda Walidi yake tsaye yace”Zo kara bani da wannan mutsiyaciyar Uwar taka, mayyar kudi”

Dariya Walidi yake sosai ya karaso gurin yana wata irin tafiya yace”ai duk halinku daya da ita Baba, dubu daya ya ciro ya mika mata yace”kema gashinan kici albarkacin Balaraba”
Da sauri Uwa ta karbi kudin daga hannun Walidi tace”karya kake inci albarkacin wata banza yarinya, wallahi”

“Ke dai kika sani, zaki iya yaga kudin yanzu, ai tunda kince karya ne”

Tafiyar ta tayi tana surutai gami da fadar bakaken magan-ganu ga Balaraba,
Sallau ma fucewa yayi ya bar gidan, Lokacin Balaraba ta samu ta futo ta shiga bandaki, domin tayi wanka ganin rana tafara yi,
jan ruwa take a rijiya, Maburuka ta futo hannuta rike da bokiti, da kutto wande ke dauke da sabulu da soso, daga ita sai daurin kirji,wani irin kallo ta watsawa Balaraba, taja tsaki, yaje ta dangwarar da bokitin saura kadan ya fada kafar Balaraba, tayi saurin kaucewa, kawai bata saurare ta ba, ta dauki ruwan da taja cikin wani bokiti irin na roba ta shiga bandaki, nan ta jiyo Mabaruka na cewa, banza kawai, kina dauke da najasa kina shigarwa mutane,ban daki dole ne ma in kin futo in wanke bandakin domin bazan je in kwashi cuta ba”

Ranta ya ba’ci sosai jin abunda Marubuka take cewa a kanta, sauri-sauri take ta futo daga bandakin taci Uwarta, ta lura idan bata, tasar musu tsaye ba,zasu hanata shan ruwa a gidan,
Mabaruka na zaune a kan rijiya tana wake-wake cikin rashin kamun kai,
Balaraba ta futo daga bandakin, tayi kamar zata wuce, sai tai sauri ta dawo da baya,ta damki! wuyan Maburuka ta rike tamau, ta jawota sosai suka matsa daga jikin rijiyar, had’a ta da bango tayi ta makure ta sosai tace”wa kike zagi ne, mara kunya”

Kakari! Mabaruka take sosai tana son tayi magana takasa, idanunta sunyi jajazir,
Wani wawan mari Balaraba ta tsinka mata,wanda yasa jinta da ganin ta suka dauke na wucin gadi, tace”Ke baki kira kanki da najasa ba, zaki kira wani, bari kiji dan uwarki, duk irin iskancin da kikeyi a unguwar nan nasani, shegiya me bakin uwa, duk sharrin ku sai ya koma kanku,ni nafi karfin ku wallahi”
Hawaye ne, kawai yake zuba a idanun Mabaruka, jikinta sai kyarma! yake yau ta tsorata da Balaraba sosai,ashe haka take da karfi,sai kace me aljanu,
Cikin ikon Allah har yanzu babu wanda ya futo daga daki cikin mutan gida,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button