GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kasa da muryar ta tayi tace”bani hakuri dan Uwarki ko in cire miki makogwaro yanzu-yanzu
Bakinta na rawa tace”Allah ya baki hakuri”
Sakinta tayi tana hararar ta tace”karyar rashin kunya kike yi yarinya,wallahi kika duk ranar da kika kara zagina sai naci miki uwa”!
Shiru Mabaruka tayi tana kallonta Har ta shige dakinta,
Cikin sauri-sauri take shiryawa ta tashi su Sadiya da Shamsu ta shiryasu cikin uniporm kamar kullum, ruwan tea ta dafa musu,dake tanada kayan shayi a dakinta nan ta hada musu suka karya,suka futo a tare,a gurguje ta leka dakin Iya suka gaisa, tace”yau baki futo ba”
“Wallahi na tashi da zazzabi ne, tun dazu nake jin hayaniya a gidan, lafiya in ce ko”?
“Lafiya kalau”
Balaraba tafada ta cigaba da cewa” amma kin sha magani ko”?
“Ai cikin dare zazzabin ya rufe ni”
Iya tafada tana kara rufe jikinta,
“Insha Allahu zandawo da wuri sai muje chamis a duba ki”
“To sai kin dawo,kinji Allah yayi miki albarka”
“Ameen Iya nagode, in su Sadiya sundawo su zauna a gurin ki tunda babu isilamiyya yau”
“To shikkenan sai kin dawo”
Balaraba na futa taci karo da Walidi shida abokansa, da sauri ya taso ya zo ya karbi jakar hannunta, sai washe baki yakeyi, suka jera,har inda me Napep dinta yake, tsayuwa in yazo daukar ta
Tunda ta futo matasan dake unguwar suke kallonta wasu su fadi alkairi,wasu su fadi sharri a kanta, babu abunda ya dame ta, ta shiga Napep, Walidi ya mika mata jakar ta, yana mata adawo lafiya
Suna futa daga unguwar ta kunna wayarta, ko minti biyu ba ai ba kira ya shigo, sai da ta kusa katsewa sannan ta daga,
Ajiyar zuciya ya sauke, muryar shi kasa-kasa yace”Allah ya taimaki Gimbiya ta”
Shiru tayi bata ce komai ba,
“Tuba nake gani tun misalin bakawai ina nan ina zaman jiran ki nazo in baki hakuri bisa laifin dan uwana yayi miki jiya”
Ajiyar zuciya tayi, tace “Yusuf halinka daban da kai da dan uwanka”
Murmushi yayi kamar yana kusa da ita, yace”Halinmu daya da dan uwana,shima dan dai baku fahimci juna bane, ta wani gefan ma yafi ni kyawun hali”
“Hummm, yanzu dai ina kan hanya, ganin zuwa sai muyi maganar” bata saurari abunda zai ce ba ta kashe wayar,
Tunani take wace hanyar zata bi domin ta dauki fansar abunda Sarki! yayi mata
Muje zuwa My Fans????
Comment
Vote and Share
[11/07, 20:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®REAL BINTU BATULA????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
Zamani Writes Association????????
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
????46
Bisimillahir-rahamanir-rahim
Tun kafin ta futo daga Napep din ta zuge jakarta ta futo da niqabi ta rufe fuskarta sabuda ganin kasuwar ta soma cika da jama’a wataran har kusan faduwa take sabuda idanun jama’a
Sai da takara jaddadawa Ashiru akan kar ya wuce shida da rabi na yamma, bai zo ya dauke ta ba,domin bata so ta dinga kai wa Magariba a waje.
Duk da niqab din dake sanye a fuskarta hakan bai hana wasu gane ta ba, sabuda yanayin tafiyar ta, wasu suke gane ta, shiyasa bayan wucewar ta suka kama yi da ita,
Wani Alhaji Musa yace”wallahi na rasa yadda zanyi in tunkari yarinyar can, sabuda mugun kwarjinin da take min,gashi Allah ya jarrabe ni da sonta kamar me”
“Ai ba kai kadai ba”
wanda yake kusa dashi ya fada, ya cigaba da cewa”ni kaina kwarjini take min,wallahi ina mutukar son tsarin jikinta, da yanayin tafiyar ta, yarinyar fa tayi sosai, matsalar kawai “yar talakawa ce”
“Duk wannan ba matsala bace a gurina mutukar zan samu fuska a gurinta”
Alhaji Musa ya fada, yana jan numfashi, yace”kwanaki da muke zancan ta da Alhaji dan Yaro, yake fadamin, wai Yusuf Maddibo ne yake neman ta,kasan Abokin Buba ne,shi kuma Buba kasan tare suke harkokinsu dashi,shine yake fada masa”
“Ai kaji abunda nake fada maka,wallahi yarinyar matar manya ce,sosai amma in kaga zaka iya shiga bisimillah,amma fa zaka sha wulakanci, domin shi ma Yusuf din, dan kore ne a gurinta har yanzu bata karbe shi ba”
“Duk wannan baya damuna,indai zan samu biyan bukata”
Alhaji Musa ya fada, nan suka cigaba da tattauna maganar,
Kafin ta shiga gurin nata sai da ta tsaya suka gaisa da Me kosai cikin mutumci, ta futo da dari biyar ta mika mata tace”gashi a rabawa yara kosai sadaka”
Almajiran dake zaune gurin suka dinga murna da farin ciki, dama dakon zuwanta sukeyi sabuda sun saba kullum tana sawa a raba musu kosai, nan suka dinga godiya gami da fatan alkairi
Anutse ta shiga ciki inda ta tarar da Su Hauwa’u suna ta kai wa da kawo wa komai tsaf duk wani costomas an bashi abunda yake bukata, sama-sama suka gaisa da su, fuskarta babu walwala, kullum haka takeyi sabuda bata son wani ya kawo wargi a cikinsu,can gefe guda ta hango Yusuf zaune cikin kujera, ya zuba mata ido,kamar zai cinye ta,fuskarsa dauke da wani kayataccan murmushi, da sauri ta dauke kanta, ta nai wa Hauwa magana,
Reciptoin ta futo ta zauna kan kujerar ta, kamar ko da yaushe, tana kallon masu shige da fuce, a gurin.
Ganin ta futa yasa Maddibo mikewa a nutse ya bi bayanta, mutanan dake gurin suka bishi da kallo, ganin dukaninsu a gurin suka taddashi,gashi ya mike ya futa batare da yaci komai ba.
Zama yayi kujerar dake fuskantar ta fuskar shi dauke da murmushi har ila yau, yace”Ranki ya dade,barka da zuwa”
Sakin fuskarta tayi tace”kai ma ranka ya dade,fatan ka tashi lafiya”?
Bai yi tsammanin zata sakko da wuri haka ba, ganin yadda ranta ya ba’ci jiya, amma abin mamaki ko a fuska bata nuna masa ba,asali ma yau tafi kowane lokaci sakar masa jiki.
Yace”Lafiya kalau, na tashi ke fa”?
“Nima lafiya kalau”
tafada tana yi masa wani kayataccan murmushi.
“Hakuri nazo na bawa Gimbiya sarauniyar zuciya ta”
Yafada yana wani karyar da kai, gwanin tausayi
“Humm Yusuf kenan, wane hakuri zaka bani, ai kai ba kayi min laifin komai ba,wanda yayi laifi shi ya kamata yazo ya bada hakuri in ana so in huce, fushina”
Ta karashe maganar tana wani fari da ido.
Shiru yayi yana binta da kallo,cikin so da kauna, yace”Ayi masa afuwa,Gimbiya na ari bakinsa naci masa albasa, abunda yayi shi, shine yayi ni, A yafe masa”
Girgiza kai tayi tana tabe baki tace”in kaga na hakura to sai dai idan ka dauko shi ka kawo min shi nan yazo gurina a karo na biyu,wannan zuwan nasa ya zama na bada hakuri ne, a gurinshi, shine kawai zai sa na hakura,
Murmushi yayi yana gyada kai cikin zuciyar sa yace”lallai na kara tabbatar da cewar sarauta a jinin yarinyar nan yake,wato ta na nufi yaje ya dauko Sarki! a karo na biyu ya kawo mata cikin kasuwa, lallai lamarin Balaraba ya shallake tunanin sa, ko mutuwa zai yi baya tunanin Sarki! zai yadda yazo kasuwa gurin ta da zumar bata hakuri, sai dai idan zai rufe masa yaki fada masa gaskiya, amma domin ya nuna mata son ta dake cikin zuciyar sa na gaske ne, yasa yace”duk wannan me sauki ne, mutumi na zai iya zuwa ya baki hakuri kamar yadda kike bukata,sabuda dan uwana yana mutukar son abunda nake so”
Harararsa tayi tana fari da ido tace”ni dashi wa kafi so”?
Dariya yasa yana kallonta yace”matsayin ki daban, nashi daban, a zuciya ta, amma bari ki fara ganin naki matsayin a gurina”
ya karashe maganar yana kokarin futo da wayarsa aljihu,
A nutse tace”me zakayi naga ka futo da waya”?