GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tofa menene zai biyo baya, bayan wannan?
Muje zuwa my fans????
Comment
Vote and Share
[14/07, 22:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadijaYaro da kudiGimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????49
A nutse Jakadan Maimarta ba ya karasa inda Sarki! yake kishingid’e kanshi a kasa yace”barka da hutawa ranka, ya dad’e.
Cikin k’asaita ya dago kanshi yana kallon Jakadan yace”barka kadai”
“Allah shi taimake ka Mainasara, dama Maimartaba ne yace” yana son ganin ka yanzu”
Shuru gurin na tsawan minti biyu, ya kara dago kanshi a karo na biyu,yace”kaje kace ganinan zuwa”
“To a tashi lafiya, ranka ya dad’e ko in tsaya mu tafi tare ne”?
Girgiza kai yayi kawai, hankalinshi na kan wayarshi, cikin nutsuwa Jakadan ya mike ya bar gurin,yana baza babbar rigar dake jikinshi,
Tsawan mintu goma yayi yana kallon cigaba da kallon hotunan Balaraba dake wayarsa,bayan zuwan Jakadan Maimartaba, wani hotono duk cikin hotunan ya d’auki hankalinsa wanda ta sanya hannuwan ta ta rufe fuskar ta dasu, hoton ya dauk’i hankalin shi sosai sab’anin wanda fuskarta ta futo a ciki, sabuda haka kawai sai d’ora shi a fuskar wayar tashi,ba tare da yayi tunanin komai ba, ya jima yana k’arewa yatsun hannuta kallo wasu zara-zara dasu, inda suka yi wani jazir sakamakon k’unshin da tayi musu, ajiyar zuciya ya dinga saukewa, a kasalance ya mik’e tsaye ya sanya takalmansa, ya nufi fada, domin amsa kiran mahaifin nashi.
Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga, ya nemi guri ya zauna, ya kai gaisuwa ga mahaifin nasa,sannan d’aya bayan d’aya ya gaida su Waziri.
Shiru fad tayi kowa yana sauraron yaji abunda yasa Mamairtaba kiran Sarki!
Gyaran murya yayi yace”Munyi magana da baban ka Waziri, d’azu da safe, nace masa ya aika ai masa kiran ka ya nemi yaddar ka, a kan abun da yazo dashi, naji mutukar farin ciki a busa amincewar da akayi,ba tare da kaga yarinyar ba,kuma kayi k’okari gurin ganin ka kare martabar d’an uwana, naji dad’i da bin umarnin sa da kayi, yanzu abunda ya rage mana shine a sanya lokacin daurin aure domin baza mu tsayw jira ba, ga d’an uwanka ma yazo da maganar aure ya samu mata, amma dole za muyi bunkice akanta, ya fad’a mana yarinyar ba tada alak’a da sarauta, duk wannan bazai hana mu hanashi auran ta, sabuda haka na yanke hukunci a kan zaka zama jagora gurin bunkito mana Asalin yarinyar kafin magana tayi k’arfi, yanzu dai na bashi damar yaje ya cigaba da neman ta, Allah yasa za’ayi damu”
Maimartaba ya karashe maganar Cikin nutsuwa da dattako.
Shiru na tsawan minti biyu fada tayi shiru, Sarki! ya kasa cewa komai, tabbas mahaifin nasa ya d’ora masa nauyin mai wahala, wanda kuma yake ganin bazai tab’a bujere wa Umarnin shi, dole kamar yadda yake Umartar shi da yayi abu,wannan ma dole ya je ya cika Umarnin da ya bashi,
Wannan zan iya cewa sarar, Sarki! ce in kuna magana dashi, kafin ya baka amsa zai tsaya ne, yayi nazarin maganar da kafad’a masa daga bisani sai ya yanke hukunci,sam! baya yanke hukunci kai tsaye.
A nutse yace”insha Allahu zan iya bakin k’okarina gurin ganin na bunkita Asalin Yarinyar da Nasabarta, sannan da tarbiyar ta, Allah ya bani ikon bin Umarni, Allah ya taimake ka”
Murmushi ne kwance a fuskar Maimartaba, abunda d’an nashi yafad’a ya sashi farin ciki sosai, domin ya zaci zai bujire masa a kan Umarnin da ya bashi, duk da dai ya san d’an nashi yana masa biyyaya a kan duk abunda ya Umarce shi, ya san wannan abun da ya sashi mai tsauri ne, a matsayin sa na Yarima mai jiran gadon mulki, sabuda haka babu abunda zai cewa d’anshi sai dai yayi masa fatan alkairi a rayuwarsa,shima yana masa addu’a Allah ya bashi “yaya masu biyyaya kamarshi.
Nan suka cigaba da zama a fada, suna sauraron masu k’orafe-k’orafe daga jama’ar gari.
Wannan kenan
Yau da Wuri ta dawo gida, sabuda rashin lafiyar Iya, haka ta wuce Shamsiyya a k’ofar gida yara duk sun yanyame! ta kamar ko da yaushe, haka ta kewaye su ta shiga cikin gidan, karo suka kusa yi da Iro, tayi saurin bashi hanya, domin ya wuce, sai yaja ya tsaye yana mata wani kallo irin na ” yan iska,
Kauda kanta tayi tana k’okarin shigewa cikin gidan, in ba zata manta ba sai tace yau tafi sati uku rabon da ta sanya shi a idon ta, yana can yawace-yawacen shi,
Tare mata hanya yayi ya wani zura hannu a cikin aljihun wandon jins dake jikinshi, wai shi lallai saurayi sai ya burge ta, abun sai ya so ya bata dariya, ta maze batai ba, k’ara had’e fuskar ta tayi tamau! tace”meye haka Iro zaka tare min hanya,don Allah kauce ka bani guri”
tafad’a tamkar itace take gaba da shi ba shi ba,
“Ank’i abaki hanya ki wuce ” yar rainin hankali, ni zaki dinga yiwa yawo da hankali, ranar nan nace inaso muyi magana dake, sabuda tsabar kin mai dani albada! wanda bai san abun da yake ba, kika shanya ni a waje ina ta jiran ki futo ki kak’i, Ehh!! har na tsaga bulle na, na shigo cikin gidan, nan ma kika rufe k’ofar ki, sabuda kinga dodo, zai cinye ki, to bari kiji duk irin k’ina da kike to baki da miji sama dani, sabuda haka duk guje-gujen da kike zakiyi ki gama, maganar auranmu dake tayi nisa kece baki sani ba.
Ya karashe maganar yana matsowa kusa da ita.
Da sauri ta matsa gefe guda tana toshe hancin ta, domin tunda ya fara magana wani irin wari yake surnanowa yana futowa daga bakinshi, sam! bata son kallon fuskarshi sabuda yadda tayi bak’ikk’irin da ita, leb’anshi har da d’inki da goshin sa, gashi babu hakora uku a bakin shi, lokacin da ya matso kusa da ita kuwa wani irin tsami! taji me hawa ka, lokaci guda taji zuciyar ta wani irin mungun tashi,
Da kyar! tace”Iro bani hanya in wuce dan girman Allah kar kasani in a mayar da “yayan hanjina”
“Ke!! dan Uwarki me kike nufi? “
Yafad’a yana kara kusantar ta,
Ya cigaba da cewa”Lallai ma kin raina min hankali wato kina nufin wari nake shiyasa kike toshe hancin ki ko”?
Shiru Balaraba tayi har yanzu hannunta na hancin ta,
Wata irin raruma! ya kai mata ta goce! da sauri, yaje ya daki! karyayyar k’ofar gidan, dotsen da akasa a ka tokare ta yayi nasa guri, k’ofar ta rufe, yayi kanta gadan!gadan!
Ganin yayo kanta yasa da sauri ta nufi cikin gidan, sai ya sanya kafarsa ya tad’e ta tafadi! kasa, ya kai mata raruma! ta mike zumbur! ta ingije shi ta nufi k’ofar futa, da gudu, sai ya k’ara sanya kaf’arsa ya tad’o ta a karo na biyu, nan Allah bai bashi nasarar kada ita ba, hannushi ya sanya ya tokare ta yana mata wani kallon irin na sha’awa hannu ya sanya ya fuzge mata mayafin ya jefar k’asa, a gigice ya kai hannusa jikinta, inda ita kuma Allah ya bata sa’a tayi nasarar fuzgo wata k’aramar wuk’a dake soke a k’ugunshi, hannushi ta daka! da ita cikin zafin nama! nan take Iro ya zube a gurin jini na futa a hannunshi sosai da sosai, saura kad’an d’an ya tsan shi k’arami ya guntule, ihu! yake kurmawa, wanda yasa mutanan Cikin gidan futowa da gudu suka nufi inda suke jiyo Ihun!
Da Sauri Walidi ya bud’e k’ofar soran dalili shima yaji ihun, dama dawowar shi kenan,ya tsaya yana raba wasu yara fad’a wanda suka zo siyan a wara,



