GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ihu! Iri yake sosai kamar wani k’aramin Yaro, ga Balaraba a tsaye, babu mayafi babu d’ankwali, ga hannunta rik’e da wuk’a
Da yake a kwai sauran haske a garin bai duhu ba, yasa kowa ya fahimci abunda yake faruwa, Uwa! ce ta kurma wani uban ihu! gami da d’ora hannu a ka tana fad’in na shiga uku! na Lalace, ni Uwande! shikkenan zata kashe min yaro na wanda nake hutawa dashi, wallahi Balaraba sai na d’auki fansa a kanki”
Kafin kowa ya ankara tayi kan Balaraba da gudu ta danne ta tana duka ko ita, da yake Uwa! irin matan nan ne masu k’iba, kowa ya kasa daga ta daga kan Balaraba sai duka take, Lantana ko tana gefe d’aya tana k’ara ingiza Uwa!,kan taci uban Balaraba, a cewar ta abunda Balaraba takeyi musu samun guri ne,
A fusace!Walidi yayi kan mahaifiyar tasa wacce take k’okarin kwatar k’aramar wuk’ar dake hannun Balaraba wai lallai sai ta cire mata ya tsa kamar yadda tayi wa iro,
Cikin tsawa! yace”Wallahi Uwa! in baki d’agata kin daina dukanta ba sai nayi miki aski da wannan askar dake, hannuna, kin san dai zan iya, ko, dan tsabar mugunta da kawai ki danne ta, kina duka, kamar baki san halin d’an iskan d’anki ba, saunawa nake kamashi ke kanki yana lek’a ki a band’aki in kina wanka, wallahi naji dad’in abunda Gimbiya tayi masa, shege dan iska”
Ya karasa maganar yana dukan k’afar iro wanda yake kwance a k’asa rik’e da dan ya tsa yana jale-jale sura kad’an ya cire, amma sabuda tsabar son mata, yana can yana kallon jikin Balaraba, wanda Uwa! ta tattare mata zani, duk rabin cinyoyin ta a waje, ji yake kamar ya shafa jikin ko yaji sauk’in Sha’awar dake damunshi
Ganin Walidi yana masifa yasa Lantana tayi k’us! da bakin ta, sabuda tana k’ula fucin d’ari biyun da yace zai bata gobe da safe, tasan tayi magana zai iya hana ta,
Itama Uwa! mikewa tayi daga kan Balaraba, tana wani irin huci! sai zaginta take ta Uwa ta Uba, tana nema mata bala’i gami da jafa’i,
Abunda yasa ta daina dukan Balaraba shine tasan tsaf! Walidi zai aikata abunda yace, shiyas ta d’agata badan ta hak’ura ba,
Cikin borin kunya Iro ya mike tsaye yana nuna Walidi dan ya tsa yace”ban tab’a sanin kai shege bane sai yau, ina matsayin d’an uwanka, wannan tayi yunk’urin kasheni ka goyi da bayan ta, to bari kaji wallahi da kai da ita duk ban kyaleku ba, sai nasa an tsaga min ku gida biyu,zakaci uwarka! k’aryar daba!! kake tawa dabar!! tafi taka”
A zafafe! Walidi yace”wa kake zagi! in ka isa kai wani ne k’ara zagina ka gani”
Cikin gadara Iro yace”Uwarka!! Ehh gshi na zage ka me zaka iya ne”!!
Da gudu Walidi yayi kanshi ya yar k’asa ya dinga dukanshi, Sai da yayi masa laga!laga sannan ya d’aga shi yana huci! ya tsaya kusa da Balaraba wacce ke tsaye kawai ta rasa ma wane irin tunani zataiyi wannan masifa har ina!
Yace”in ka isa ka k’ara shiga hurimin Balaraba, sai dai Uwarka ta haifi wani, ya karasa maganar yana cije baki!
Ihu! Uwa! take kurmawa tana tsinewa Walidi, Iro ta kallah wanda yake kwance bai san in da hankalin shi yake ba, jini ne kawai yake futa ta hancinsa da bakins, da gudu ta karasa gurin da Lantana take tsaye, tace”Lantana a gabanki za’ayi kisan kai, sabuda ke butulo ce wato kin manta alkairin da yaron nan yake miki,kullum ya dawo daga tafiya kin dinga k’arb’e masa kud’adan sa, babun abunda zance dake sai dai ince Allah ya isa tsakanina dake Lantana” tana gama fad’ar haka ta shige cikin gidan da gudu domin ta d’ebo ruwa wanda zata zubawa Iro da alama suma yayi
Tana barin gurin Lantana tace”Yo ni me zan tsinana miki, kaji masharanciyar mace, ko zatai min sharri, yashe nake ganin Iro ma balle ya bani kud’i o ni Lantana Allah ya had’ani da suruka wacce bata k’auna ta”
Banza Walidi yayi mata,hankalin sa na kan Balaraba yana tausar ta, kawai sai saukar mai soyayye yaji a k’afafun shi ya waiwaya a zabure! Shamsiyya a tsaye a bakin k’ofar shigowa hannuta rik’e da abunda take tsamo a wara, sai muzurai! take sam! bashi taso mai ya sama ba Balaraba tayi niyyar watsa wa sai ya sauka a k’afarshi.
Muje zuwa
Comment
Vote and Share
[15/07, 22:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????50
Da sauri Balaraba ta sunkuya tana duba k’afarta guda wacce soyyayan mai yayi nasarar zuba lokaci guda ya tsun kafarta suka tashi, sabuda nan mai ya zuba Walidi kuwa ko ta kan kafarshi bai yi ba, yayi kan Shamsiyya, da wani mahaukacin duka, da gudu tayi cikin gidan, domin tasan zai iya ji mata ciwo,
Duk suna tsaye a tsakar gidan ta shigo a guje ta nufi d’akinsu ta kulle kof’a tana zagin Walidi tace”dan Uwarka, ka manta ranar da ka k’onani akanta, wallahi naso ita man ya sama shegiya mai sufar aljanu”
K’wafa Walidi yayi kawai yace”sai dai in baza ki kara futowa ba amma billahillazi sai na k’one miki wannan bak’ar fuskar taki,wacce ta gaji da bilitin” d’akin Balaraba ya nufa yana k’okarin bude mata,
Lokacin da ta shigo cikin gidan kai tsaye d’akin Iya ta nufa, duk mutan gidan babu mai kula da ita, gwara ma matar Kawu wato Sadiya,ita kuma, bata zama,kusan kullum tana hanyar gidansu, tana jinyar mahaifiyar ta, Iya na kwance kan wata ya mutsetstsiyar kafita jikinta a rufe,da zani sai rarar d’ari take, Sadiya da Usuman suna zaune sun zabga uban tagumi, suna tsoran su futa Lantana ta dakesu domin haka take musu kullum shiyasa in suka dawo daga makaranta, har indai yayarsu bata dawo ba, to sai suyi zamansu gurin Iya, jikinsu yayi sanyi da rashin lafiyar Iya.
Shiga tayi d’akin cikin sallama Sadiya ta amsa, tace” Yayarmu sannu da zuwa”
“Sannu Sadiya, kuna zaune ku kad’ai Iya bacci take ne”?
” Yanzu ta tashi taje tayi alwala ko sallah batai ba ta koma ta kwanta”
Sadiya tafad’a tana kallon yayar tata.
” Yayarmu kin dawo lafiya”?
Usuman yafada, hankalinshi na kan ta
“Lafiya lou Usuman, kayi karatu a makaranta ko”?
” Eh nayi yau ma an karb’i haddar da aka bamu”
“To ka dage da karatu ni kuma nayi maka alk’awarin zan siya maka keken hawa”
Murna yake sosai ya mik’e ya karaso inda take ya rik’e hannunta yace”nagode Yaya Allah ya biya miki bukatun ki”
“Ameen” Balaraba tace ta mayar da hankalin ta kan Iya, tace”Iya sannu da jiki”
Kai kawai Iya ta iya d’agawa “Bari in d’auko miki hijab muje Chamis kinji”
D’aga kai ta kuma yi a karo na biyu.
da taimakon Balaraba Iya ta mike tasa mata hijab d’in ta rok’ota suka futo, Su Sadiya nan suka zauna jiran dawowar su
Kasancewar Walidi ya futa daga gidan yasa Lantana yi musu wani kallo shek’ek’e tace”munafurcin banza da wofi, zaki lanjare kice baki da lafiya, duk kuje ku gama munafurcin naku ku dawo ku same ni nice dai Lantana ban can zaba
Babu wanda ya kulata cikinsu Uwa! lokacin tana band’aki, sai ita kad’ai a zaune a tsakar gidan, suna futa suka ci karo da Sallau ya dawo,tun daga bakin lungu a kasanar dashi abunda ya faru a gidan, cikin tashin hankali ya shigo gidan,
Yaji dad’in ganin ta a sabuda haka sai ya ja tsaya yana surfa mata ashar yace”bantab’a sanin ke “yar daba bace sai yau, duk ikirarin da mutane suke a kan ” yayana cewa suna harkar Daba! a she ba haka bane, duk abunda ya faru d’azu ina da labarin sa, to bari kiji wani abu da baki sani ba, duk k’iyayyar da kike wa Iro shine dai mijin ki ko kink’i ko kinso sabuda haka dole ne zakije har d’akinshi ki bashi,hakuri idan kuma kink’i sai dai kije ki nemi wasu iyayan bamu ba, domin ni nan da kika ganni sharri na yafi kala dubu,wallahi duk inda kika shiga,sai naje na b’ata miki suna”
Ya karashe maganar a zafafe!