GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kyar! Iya ta bud’e baki tace” haba Sallau bai kamata kafad’i wannan maganar ba,kamata yayi kabi ba’asi kafin ka yanke hukunci, me Iro yayi mata har ta d’auki mataki a kanshi, ni duk da akwance nake a d’aki bana jin dad’i hakan bai hanani na jiyo abunda yake faruwa ba, da Iro da Balaraba duk naka ne, in dai adalci ake”

“Ke Iya rufe min baki, bana son hauka, me zai yi mata kuwa? wanda har zata d’auki wuka ta cire masa d’an yatsa, wallahi sai kin biya kud’in magani yanzu-yanzu, domin yana can Chamis za’ai masa d’inki, duk abunda ya faru shi Iro da kanshi yaje ya fad’a min komai, ni sam banga wani laifi a nan ba, dan yayi yunkurin tab’a jikin ki sabuda shine mijinki, dama kuma addini ya hallata cewar namiji zai iya tab’a jikin matar da zai aura kafin auren domin ya san wace iri ce matar gudun abunda zai je ya dawo, sabuda haka bayan kin biya kud’in maganin shi zakije ki bashi hakuri har shagonshi, kamar yadda na fad’a a farko”

Cikin mamaki Balaraba take kallonshi, jin abubuwan da yake fad’a bata tab’a yadda Kawu Sallau mugun jahili ne ba irin yau, a wace mazahabar a ka yadda namiji ya kusanci mace kafin auransu, itakam bata tab’a jin wannan k’aulin ba,

Iya tace”to kayi hakuri mu dawo sai mu yi maganar in sha Allahu zata bi umarnin ka kamar yadda kake so”

Kaucewa yayi ya basu hanya yace”kuje ku dawo ku taddani ina nan ina jiran ku”

Suna futa shi kuma ya shige gidan yana zage-zage kamar wani mahaukaci, Lantana ta mik’e zaune tana taya shi zage-zage tace”ashe kaji abunda ya faru ko?

“E naji ai shi Iron yaje ya fad’amin, duk abunda ya faru,kuma ina shigowa unguwar ake ta tarata ana fad’amin”

“Hummm! kagani ai sai ka d’auki mataki akan ta in ba haka ba kuwa sai dai kazo ka tarar ta kashe mu,a gidan dan yarinyar ta zama abunda ta zama, a duniyar nan”
Nan Sallau ya zauna kusa da mahaifiyar tashi suna k’ara maimaita maganar,

Uwa!ce ta futo daga band’aki hannunta rik’e da buta, aje butar da sauri ganin d’akin Balaraba a bud’e tun dazu Walidi ya bud’e mata, lokacin da zata shigo,gidan sam ta manta bata kulle ba suka futa, kai tsaye d’akin ta nufa, Lantana ta mik’e da sauri tabi bayanta, shima Sallau d’in mikewa yayi ya rufa musu baya,

Bunkice suke mata sosai a cikin d’akin sunyi mata filla-filla da kayan sawar ta sun jefo waje, Lantana tace” yawwa Uwa! d’aga katifar nan ko anan take b’oye k’udi ki kwasa maganin dukan d’anki da tayi, aikuwa kafin Lantana ta rufe baki, Sallau ya d’aga katifar da sauri, babu komai k’asan katifar, ya mayar da ita ya aje, dama Balaraba bata wani ajiyar k’udi duk in ta samu na b’ukata ne shiyasa basa taruwa, mafi a kasari ma tafi ajiya cikin jakarta,kuma tana jikinta a rataye, haka suka k’araci bunkucen su basu ga komai ba, suka futo suna ta zagin ta,kamar mahaukata

Babu abunda yake damun Iya illa zazzab’i na maleria nan me chamis din ya had’a mata magani yace”dole za’ai mata allura ta kwana uku, Balaraba duk ta biya kud’in me chamis din yace”Iya kinci abunci in ce ko”?
“Eh to ba sosai naci ba”
Iya tafad’a da kyar! yace “babu damuwa dama illar guda d’aya ce ayi miki allura bakici abunci ba, tunda kinci ko yaya ne shikkenan, nan ya had’a allura yayi mata, suka kamo hanya suka tawo gida,gurin wani mai balango da gurasa suka tsaya Balaraba ta sai mata gurasa da balangu,suka wuce gida, suna shiga soran gidan suka dinga jin hayaniya tana tashi a gidan, Iya tace” wannan masifa ta gidan nan Allah kayi mana maganinta,
“Humm Iya ki kyalesu suyi su gama insha Allahu na kusa barin gidan sai kowa ya huta tunda nice basa buk’ata, duk kuma wanda ya zalunce ni Allah zai saka min”
Balaraba tafada lokacin da suke shiga gidan, kayanta tafara cin karo dasu a watse a tsakar gida wasu a gurin rijiya wasu a kusa da shara, Cikin mamaki ta tsaya tana binsu da kallo, dawowar Mabaruka kenan daga talla, tana tsaye ita da Shamsiyya tana wassafa mata abunda ya faru, tsalle ta buga tayo kan Balaraba tace”Allah nagode maka,kullum mu ake kira karuwai, yau gashi yau Allah ya nuna mana karuwa a gidanmu,,zatayi zina da d’an gida, Huuuuuuuuu!!! tir dake da halinki shegiya karuwa”
tak’arashe maganar cikin ihu! dama hanya take nema wacce zata ci mutumcin Balaraba sabuda mak’ure ta da tayi a bango kwanaki,
kayanta dake watse tabi tana tumurmusawa da k’afafunta, babu abunda Balaraba tace, takama hannun Iya ta shigar da ita d’akinta,sannan ta futo su Sadiya na biye da bayanta, suka shiga d’aki, zama tayi gefan katifa ta zabga tagumi hannu bibbuyu, tunani take yaya zatayi da rayuwar ta da ta k’annenta, sai yanzu tafara jin rad’adi a kafarta, kallon k’afar tayi taga ta kara tasawa alamun k’ona, ita ba wannan ne abund ya dame ta ba yadda za’ayi su futa daga wannan jarabar itada “yan uwanta, shawarar da ta yanke kawai shine ta nemi gidan haya su bar gidan, shine mafuta duk wanda zai yi zargin ta, ya dad’e bai yi ba,dama kuma a cikin zargin mutane take, kullum, tun tana jiyo motsin da hayaniyar su Lantana ta a tsakar gida, taji shiru da alama kowa ya shiga d’akinshi, buta ta dauka ta futo tsakar gidan domin ta daura alwala, suka ci karo da Sallau ya shigo gidan afujajan, gabanta ne ya fad’i sai tafara karanta innalillahi a zuciyar ta, tsayawa yayi yace” yawwa dama d’azu gajiya nayi na futa sabuda abokai na suna jirana a waje gashi baki dawo ba, sabuda haka yanzu me ake ciki, ki kawo kud’in da nace ki bayar domin za a sai wa Iro magani yanzu”

“Kawu ina takkadun gida da shago na wanda Maimartaba da yaron shi ya bani gurin saukata”?

Gabanshi ne ya fad’i sosai sabuda tun lokacin da ya karb’i takaddun daga hannunta yaje ya sanya su a caca lokaci guda a ka cinye shi cikin inda-inda yace” wannan maganar ki aje ta gefe guda domin bazan baki a hannun ki ba, sunan na adana miki”

“Kawu kaje na bar maka su, kayi hakuri ni a yanzu bani da wani k’udi da zan baka, wallahi”
tafad’a tana k’okarin shiga band’aki sabuda tasan tunda ta ganshi ya shigo afujajan tasan daga gurin caca yake, watakila an cinye shi ne ya tawo yana neman kud’i ruwa a jallo,tasan ko ta bashi k’udin gurin caca zai koma baba wani magani da zai sai wa Iro, tana jinshi yana zaginta ta shigewar ta band’aki, bayan ya gama zage-zagen nasa d’akin Lantana ya nufa sai kace zararre, cikin ikon Allah duk ya taddasu suna bacci, nan ya tsallake su ya shige k’uryar d’akin ya fara laluben inda, Uwa! take ajiyar kud’i Allah ya bashi sa’a ya ga wani k’aton banki, batare da b’ata lokaci ba ya fasa shi ya kud’i ne a ciki kimanin dubu bakwai, ya lissafa dubu biyar ya bar sauran dubu biyu, a watse a gurin ya tsallake yayi ficewar sa daga gidan.

Muje zuwa

Shin Balaraba in ta bar gidan ina zata koma?

Idan Uwa! ta wayi gari taga bankin ta a fashe wace irin masifa ce zata biyo baya?

Ta yaya Sarki! zai fara bunkican Asalin Balaraba?

Menene a zuciyar Sarki!dangane da Balaraba?

Maddibo ne mijin Balaraba ko Sarki!?

Duk wannan amsoshin suna gaba, ku cigaba da bina domin ganin wace irin waina za’a toya

Comment
Vote and Share
[16/07, 21:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button