GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????

Bisimillahir-rahamanir-rashim

????51

Bayan ta idar da sallahr tayi addu’oin ta kamar yadda ta saba, Usuman ne ya farka daga bacci ya fara kuka, ” Yaya yunwa nakeji, abunda yaron ya fad’a, Sadiya ta hau tashi daga bacci,sam ta manta bata basu abunci ba suka kwanta bacci, Sadiya ta mik’e zaune tana mutsike ido, Balaraba tace”tashi kuci abunci,kinga Usuman ya tashi yana kuka,maza jeki dakin Iya ki dauko kular abuncin ku,da sauri Sadiya ta mike, ta nufi d’akin Iya, Iya na kwance kan dadduma bayan ta idar da sallah wani bacci ne me dad’i yake fuzgarta, zazzab’in ya sauka domin har wani gumi take, Sadiya tayi sallama, d’akin Iya ta mik’e zaune tace”Lafiya Sadiya”?

Iya kular abuncin mu zan dauka”
Iya ta koma ta kwanta,tana cewa “in kin futa ki ja min k’ofar, nan Sadiya ta d’auki kular ta futa daga d’aki,

Bud’e kular Balaraba tayi tana duba abuncin, babu abunda yayi duk da yake dafa duka ce, har yanzu da zafinsa, nan ta zuba musu suka fara ci pure watar ta dauko musu guda biyu, Usuman yace” Yayarmu ke bazaki ci abuncin ba”?

“Zanci mana Usuman kai da kuci ku koshi” tafad’a cike da tausayin yaran, bayan sun gama ta rakasu suka wanke hannuwan su, suka dawo ta gyara musu kwanciya suka kwanta, nan ita kuma ta cigaba da had’a “yan kayanta da suka rage tana sakawa cikin a kwatu, domin taci alwashin barin gidan gobe daga yau ta bar kwana a gidan,

Sai wajan karfe d’aya saura na dare sannan ta kwanta, cikin ikon Allah a subar fari ta tashi daga bacci ta futo ta d’aura alwala ta koma d’aki da sauri ganin ana iska sosai hadari ya had’u har an fara yayyafi, tanaji massalacin bayan gidansu sun tayar ta bisu sallah, bayan an idar da sallahr rayi addu’onta, ta cigaba da zama kan dadduma tana jan carbi kamar yadda ta saba, wajan karfe shida, ta fara jin motsin mutanan gidan, sun fara futowa, bacci ne yake fuzgar ta kad’an-kad’an sai taji hayaniyar Uwa! tana buga kyauran d’akinta ta tare wa Sallau hanyar wucewa tana kunzuma masa ashar! “Wallahi tallahi babu wanda zai yi min wannan d’anyan aikin sai kai,domin dama kasha auna fasa min asusu na,ina kama ka,shine jiya ka faki idona, sai da kabari nayi bacci kafasa ka kwashe min kud’i ,wallahi Sallau ko ni ko kai a gidannan domin bazan sha wahalar neman kud’i na ba,ka dinga bin dare kana sacewa, eheee! ba zata sab’uba bunduga a ruwa!
Ta karasa maganar tana tattaro wuyan rigarsa ta cukume shi,

” Shikkenan daga kin ga an fasa miki banki an kwasar miki kud’i sai kice nine sabuda kin raina ni duk b’arayin “yayanki bakya tuhumar kowa sai ni, to komai masifar ki dole ne ki sake ni,inje inyi alwala inyi sallah tunda ke baza kiyi ba, baza ki hanani yi ba”

“Kai dallah! rufe min baki”
tafada tana kai hannuta dai-dai bakinsa kamar zata gwab’e ta cigaba da cewa”kai har kana da bakin da zaka fad’i wata magana a kan sallah, akwai babban makiyin Allah irinka, ai Sallau in kaga na cika ka agurun nan to tabbata ka futo min da kud’ina”
Tafad’a tana k’ara tattaro wuyan rigar sa, k’arfi yasa ya angije ta, tafad’i k’asa ragwajab! ya futo daga d’akin da sauri, ya nufi k’ofar futa daga gidan, da gudu ta biyo bayanshi tana huci! cikin tashin hankali da masifa tace” ni ka tunkud’e ko, har kasa na fad’i a gaban yara na, to yau zanga yanda za’ayi ka futa daga gidan nan mutukar ba kud’ina ka bani ba”

Mutan gidan duk sun futo suna kallon ikon Allah, Uwa! ta shak’e wuyan Sallau sai huci take, dama d’azu shammatar ta yayi ya ingije ta d’azu domin Uwa tana da mugun k’arfi sai kace doki haka take,

K’ifta ido yake kamar b’era a ruwan zafi, bakin sai karkarwa yake,ya rasa abun cewa, duk alamu na rashin gaskiya ya bayyana a tattare da shi.

“Ke dan ubanki sakar min wuyan d’ana kar ki kashe min shi ki cuce ni”
Lanatana tafad’a lokacin da ta karaso inda suke, cikin tashin hankali take k’okarin b’anbare hannun Uwa!daga wuyan Sallau, doke hannun Uwa tayi, cikin rashin kunya tace”kinga Lantana, matsa dan Allah sam baki iya komai ba sai munafurci da kwad’ayi, in kinga na sake shi to sai ya futo min da k’udina ehee!”

Gefe guda Lantana ta matsa tana rik’e hannun ta domin taji zafin buge mata hannu da tayi
tace”shikkenan,to kashe shi ki huta mara kunyar yarinya kawai, a gidan ubanwa naje nayi k’wadayi da har kike kirana da haka”

“Sai kiyi kuma kanki a keji”
Uwa! tafad’a tana k’ara matse Sallau jikin garo

Walidi ne ya shigo gidan, tashin sa kenan daga bacci ya fara jiyo hayaniya sabuda haka a fusace ya shiga gidan, cikin mamaki yake bin iyayen nasa da kallo,

“Ke!dallah, wai menene haka, kuke sai kace wasu yara,k’ananu, ke Uwa! sakar masa wuya” yafad’a cike da bada umarini kamar shine Ubansu,

“Walidi in kaga na saki wannan mutumin to sai ya futo min da kud’ina, da ya fasa min banki jiya da daddare ya kwashe min”

Sallau duk yayi tsuro-tsuro, gwanin tausayi

Wani irin kallo yayi wa mahaifin nasa yace”Kai! ya akai ka fasa mata banki ka kwashe mata k’udi? wallahi baba zuciyarka ta mutu, eh! ka cuce mu daka haife mu, ina tur! da futowa ta tsatstson ka!!

Kasa cewa komai Sallau yayi duk ya muzanta, jikinshi yayi sanyi k’alau sai ya sunkuyar da kai k’asa

“Walidi”
da sauri ya daga kai yana kallon inda yaji kiran
Balaraba ce tsaye k’ofar d’akinsu, hannu ta d’aga masa alamun yazo inda take, da sauri ya nufi inda take, ” ya akayi Gimbiya”?
yafad’a yana murumshi,

“Nawa ne k’udin?

” Wane k’udin kike tambaya”?

“Na Uwa! mana,sai a biya ta ta sakar masa wuya”
tafad’a tana kallon inda suke tsaye, tana k’ara mamakin rashin mutumcin Uwa!

Wata mahaukaciyar dariya Walidi ya kwashe da ita, yace”kinga Gimbiya kar kishiga wannan cakwakiyar babu ruwanki sunfi kusa, tunda ki kaga yayi shiru to ya aikata ne”

“Ai ba cewa nayi zan shiga ba, a dai biya ta ta sake shi, tun misalin shida na safe suke abu d’aya yanzu har bakwai da rabi, yanzu kuma zaka ga yara sun fara shigowa siyan a wara, wannan ba mutumci ba ne”

Tab’e baki yayi yace”dubu biyar ne”

“Shikkenan zan futa yanzu, zanje banki zan ciro k’udi ka f’ada mata in nadawo zan bata magana ta wuce”

“Shikkenan Gimbiya, tunda kince zakiyi amma ni da dan tani ne da kin rabu dasu, ai gwara da tayi masa haka,gaba bazai kara aikata wa ba”

Lantana idonta a kansu, sai tab’e baki take tana cewa”munafukar banza da wofi kawai, kinibabbiya” kasa-kasa take maganar sabuda batason Walidi yaji

“Ke Uwa! sake shi za’a biya ki”
Walidi ya fad’a yana cije baki!

Hannu daya ta mik’a masa tace”bani in rik’e a hannuna tukkuna”

“Dallah! ki sake shi za’a baki an fad’a miki”
yafad’a kamar zai kai mata duka,
Sakin sa tayi ta matsa gefe tana huci!
tace”ina kud’in suke, kai ma zan iya tsine maka akan k’udin wallahi”

Dariya yake mata yace” Yo ke Uwa! ai ko kin tsine min tsiniwar ki baza ta kamani ba, sabuda kema, baki bi naki iyayen ba, duk abunda kai sai am maka,Hahahahahahaha!
Ya karashe maganar yana wata dariya kamar shashasha.

Ya cigaba da cewa, “Gimbiya zata bayar a baki an jima”

Jin yace Balaraba zata bayar a bata yasa ta kwantar da hankalin ta ta wuce d’aki tana huci!

Sallau kuwa tunda ya samu ta sakeshi sai ya sulale ya futa daga gidan kafin kowa ya ankara,haka ya futa baiyi sallah ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button