GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kyar bushira ta hangi Sarki! Daga can nesa sai ta riqa mamakin ganinshi jin Balaraba nace da ita ae yaro ne Lallai Balaraba da son girma take cikin zuciyarta tace gaskiya yana da kyau wai!! Dole yaji dakanshi duk da cewa bai fiye haske ba amma kalar fatarshi abin kwatance ce ga wani uban saje da yabi ya kewaye fuskarshi a tsare hade da mitsitsin bakinshi idonshi Manya farare tas dasu sun Dan risina kadan bazaka taba gane girmansu ba sai ya bude masu duka Amma idan ka kalli saman fatar idonshi zaka gane yana da Manyan idanuwa a sabila da dimun’da’iman idan nashi a lumshe yake ba yadda ya bude su sabida shi kanshi yasan Allah yayi masa baiwarsu .
Tun kan ta karaso gurin Balaraba take zabga mata harara tace”wallahi Sam Sam ba kuyi ba kun zubar mana da qima kuna mata kuriqa rububin zuwa kallon wancan waishi Dan sarki Mtssss Wallahi babu da Namijin da zanyiwa wannan rawar jikin ba’a haifeshi ba tafada a zafafe tanaji tamkar taje ta gaggaurawa matan dake rububin zuwa ganin shi.
Kallonta Bushira tayi tana Mamakin Balarabar da yadda ta dauki kanta ita ba “yar kowa ba I dillalin kashi.
Tace”laifi ne Dan munje ke tunda bazaki ba ae shikkenan ,humm gaskiya ya hadu duk da banganshi sosai ba tabbas nasan yana da mugun kyau.
Tsaki Balaraba taja tace kyawunshi din baza bai dameni ba ni nan Sam Sam kyauwun wani Namji bazai rude ni ba ko wata sarautarsa tafada tana girgiza jiki gami da ji da kanta
Dariya Bushira tayi kadan tace” Wallahi wannan Abinda kekeyi yana mutukar bani Mamaki wai ko Dan kinga kina da kyau ne?
Banza Balaraba tayi mata tana hura hanci!
Bushira tacigaba dacewa Dan kinsan bazaki taba samun kamarshi bane a matsayin Miji shiyasa kike ta wannan Abin”
“Wani kallon Tara shaura kwata Balaraba tayiwa bushira tana ya mutse Fuska tace ” Billahillazi kika sake yimin wannan Furucin sai na fasa miki baki ae kin San zan iya ko”!
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????????
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????Written by
Binta Umar
~MAMAN ABDUL WAHABU~
~MRS AHAMAD GWADABE~
WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN
08089965176
????6
Bushira tace”idan baki fasa basa min baki ba kya tsoran Allah Mtss ke daga anyi magana sai kiriqa nunawa mutane gadara Aikin kawai!
Shiru Balaraba tayi mata ganin rantaya baci Sam bata son bacin ran Bushiran sabida ita kadai ce ta iya zama da ita take jure halinta ,tace”Ai sai ki shige mutafi ni wallahi nagaji da tsayuwar gurin nan wai sai yaushe za’a tashi tunda dai Maimartaba ya tafi ba shikkenan ba kowa sai ya yi nasa guri” Tafada tana wani daga kai!
“Sai dai ke kiyi tafi Amma ni bazan biki ba ke kullum ba kya gudun Abin Magana duk da halinki Amma haka A ka karramaki gurin nan gashi kina nema ki watsawa mutane qasa a ido”Bushiran tafada tana dauke kai daga kanta
Gaba tayi kawai ta kyaleta tsaye a gurin tace “Sai kin tawo ae wallahi bazan zauna ina bata lokaci Na ba kinsan su Sadiya nacan A takure babu Mai basu Abinc……kafin ta karasa Sallau ya tari gabanta Cikin yaqe yace”diyata yarinyar Albarka ina Alfahari dake”
Gabanta ya fadi!! Sai ta dake tace”Kawu Ashe kazo gurin saukar banganka ba sai yanzu”
Washe hakoransa yayi yace”ae nazu tuntuni a gaban idona Maimartaba ya fito duk ina kallonshi har ya koma cikin gida yafada yana ta dariya Mara dalili domin kana ganin yadda yakeyi kasan karfin hali kawai yake
“Allah sarki Kawu wato kazo Ashe Amma kanajin lokacin da Maimartaba yake fadin ina waliyyina yake yafito domin ya karbar min kyautittika Na kayi shiro ko? Tana sane tayi mashi Magana domin taga Halin da zai shiga sanin da tayi basu da Makiyi sama dashi da iyalinshi duk da yana Amatsayin wan Mahaifinta.
Duk sai ya diririce Sabida yasan yarinyar “yar zafin kai ce duk da cewar bata masa rashin kunya Amma yana shakkar ta yasan kallonsa kawai takeyi gashi shi kullum nuna mata yake Ubanta ne shi tunda ba ran Mahaifinta, Amma duk wani hakkinta yakasa daukewa Asali ma da hadin bakinsa A ke muzguna musu a gidan ita da “yan Uwanta.
Sai ya hau dudduba jikinsa yace”dube ni fa Balaraba babu sutturar Arziqi kunya nakeji shiyasa ban fito ba”yafada bakinshi na rawa kai daganin yadda ya yi maganar kasan tsari ne kawai da Rashin gaskiya
Bata ce komai ba kawai ta hau duba kayan jikinshi.
Tace”Kawu kenan kowa ae da sandar hannunsa yake kai duka maye laifin tufafinka yanzu gaskiya banji dadi ba wallahi ni kai dai a guri kowa da “yan Uwanshi da iyayenshi ban dani duk su Kawu Habu da Kawu Maman da Kawu Salisu babu Wanda yazo gurin
Harsu Safiya da Mabaruka ma haka ai shikkenan tafada tana daga kafada ,
Duk sai ya rasa Abin fada Sabida babu gaskiya yace”kin San wa “yan nan basa son Zumunchi kowane shege sai yace kasuwa zai tafi su kuma su Safiya da kike magana a kan su kin sansu da shegen son kudi kamar jaraba suna can suna Aikin A wara da kulelensu kamar ko da yaushe”
“To Kawu ina Uwa da Iya su mai yasa basu zo ba? Tafada domin taji mai zai ce domin tasan bata bakinta takeyi sabida tasan bazuwa zasuyi ba Lokacin da sukaji Labarin saukar cewa suka dinga yi ae saukar zuqu ce wannan.
Yace “ke ma dai Balaraba kin san wa”yannan tsinannun Matan baza su zo ba su Neman kudinsu ya fiye musu komai ki rabu da waddanan “yan hassadar ,yafada yana kokarin karbar Allon hannunta gami da kyautitikan hankalinshi na kan Mukkalan gidan da shagon sai faman washe baki yakeyi
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????Written by
Binta Umar
~MAMAN ABDUL WAHABU~
MRS AHAMAD GWADABE
WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN
08089965176
????7
Bissimillahi
Sakar mishi tayi tana bin shi da kallo ganin yadda jikinshi yake rawa Humm Kawu kenan tariga ta Fahimchi Abinda yake wa
Yace”Diyar Albarka gaskiya ina Alfahari dake da Dan Uwana Ayuba da ya hafeki Allah yajikanshi ya gafarta masa
“Ameen Balaraba tace taci gaba dacewa Kawu Naji kayiwa babanmu Addu’a banda Mamana”
Bata Fuska Kawu yayi yace “Allah yajikanta itama daga haka yaja bakinshi yayi shiru ita tarasa wace irin qiyyaya Kawu yakewa Mama ta duk da bata raye.
Yace”ae sai mutafi ko gaskiya naji Farin ciki sosai Balaraba zakije Makka Aikin Hajji mu Na zaune,
Dariya tayi tace “Kawu kenan kar kadamu Nabar maka kaje kai kawai Tafada babu damuwa tattare da’ita.
Wani farin ciki ne ya ziyarce shi A zucci yace “ja’ira mai kama da tsohowar Karuwa ae ko baki bani ba baki isa kije Makka ba in dai INA raye a doran duniyar nan.
A zahiri kuwa yariqa washe baki tamkar me sai shi mata Albarka yake kamar babu gobe.
Jin shi kawai Balaraba takeyi domin tafi kowa sanin waye Kawu.
Haka suka ran kaya suka nufi gida Kawu sai hirarraki yake mata Na babu gyara babu dalili.
Wani gida Nafara hangowa cikin wani surqoqin lungu Wanda kwatoci sukayi wa yawa gasunan duk sun bi hanya babu kyawun gani gefe ga tarin bola da tarkace da wata tsiya ce yara duk sun Tara kayan gwangwan da Alama yaran Layin suna fita Sana’ar gwangwan domin ga Alamu nan tarin robobin qarafuna da buhunhuna.