GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

To duk irin wadan nan abubuwa suna faruwa, a cikin gidan, duk abunda Allah ya nuna mata irin wanda ake kullawa a gidan tana k’okarin ganin ta kare Uwar d’akin nata,
Wannan shine karamacin Jakadiya shafa’atu a gurin Mama Fulani
Da sallama ya shiga d’akin.
“Barka da shigowa Magajin Sarki Allah ya ja zamanin Uban d’akina”
Jakadiya Shaf’atu ta fad’a kanta a k’asa,
A nutse ya zauna gefan mahaifiyar tashi, yace”barka kadai, fatan kun tashi lafiya”?
“Lafiya lou alhamdulilahi”
tafad’a tana kokarin mikewa da niyyar futa dama indai ya shigo takan basu guri ne su gaisa, sosai sai bayan ya futa take dawowa,
Cikin sakewa suka gaisa da mahaifiyar tashi, tace” nasan da akwai abunda ya kawoka tunda naganka yanzu da safe, ina sauraron ka”
Fuskar shi a sake, yace”Mama lafiya lau, na shigo mu gaisa ne”
Harararsa tayi kad’an tace”yayi kyau, yau an tuna dani kenan, ai ina lissafawa, yau kwananka uku, rabon da ka shigo min nan tun sanda nayi maka maganar Halisa”
“Mama ba haka bane, wallahi Moddibo ne yake zuwa yana takura min shine yake hanani futowa”
“Babu ruwan Maddibo yaron arzik’i kullum sai ya shigo da safe mun gaisa, kwanaki ma da yaje can gurin yarinyar da zai aura,har abu ta bashi ya kawo min, kai ka tsaya muskilanci, in anyi maka maganar aure sai ka tsiri kauracewa mutane”
“Mama kiyi hakuri maganar Halisa ta wuce, tunda na amunce,bayan itama Baba Waziri jiya mun zauna dashi, akan Maganar Azima” yar abokinshi Sarkin Yalwa, na kuma amunce zan aureta domin na faranta muku rai”
Sakin fuska tayi sosai tace”naji dad’in wannan abu, Allah yayi maka albarka, ya taya ka rik’o”
“Ameen, ya rabbi”
Yafad’a ya da cewa, Mama har yaushe kuka saba da budurwar Moddibo da har take miki aike, haka”?
“Tun ranar da Moddibo ya fara sonta, nake da labarin ta a gurinshi, kuma itama tana da labarina, mutukar yaje, gurin sai ta bada abu an kawo min”
Shiru yayi na munti biyu yana nazarin maganar da tayi, A nutse yace”na lura kema kin yaba da yarinyar tunkafin ki ganta, Maimarta ba ma na lura ya son al’amarin, Moddibo ya b’oye muku wani abu wanda baya son ku sani a kan ta, yanzu halin da ake ciki Maimartaba ya turani bunkice a kanta”
“Gaskiya banaji yarinyar tana da wani aibu, domin har waya munayi da ita wani lokacin in yaje gurinta, ya kan kira waya ya bata yace mu gaisa,ko ga muryar ta nasan yarinya ce me kamun kai”
Shiru yayi, daga bisani yace”Mama yanzu ace kamar d’an nan gidan yaje ya auro “yar bakin kasuwa mai sai da abunci a titi, Mama wai Moddibo ya rasa yarinyar da zai so sai wannan yarinyar ni nafi kowa sanin wacece ita”
Murmushi fulani tayi tana girgiza kai tace”ta yaro kyau take bata k’arko, meye laifin ta ai ya fad’amin komai a kanta, yarinyar neman na kanta take, kaga na d’aya dai bata sata bata maita, bata zina, yanzu babban abunda za’a bunkita a kanta shine asalin ta Shikkenan, ai duk inda mutum yake yana tare da baiwar shi”
Tab’e baki yayi yace”gaskiya Mama yarinyar nan tana da fada! a gurinku, ke da Maimarta ba, shima lokaci guda ya amunce da maganar, ni kam banawa Moddibo sha’awar auran yarinyar”
Da murmushi a fuskar ta tace”D’a duk na kowa ne, kai dai kayi masa fatan alkairi kawai”
“To me nace yanzu, tunda yaji ya gani yana son ta a haka, Allah ya sanya alkairi”
“Ameen, abunda zakace kenan”
Hira sukayi irin ta tsakanin d’a da uwa sannan yayi mata sallama ya futa,
Karf’e takwas da rabi na dare, ya shirya tsaf cikin k’ananun kaya, riga da wandon jins, masu kyau ya sanya farin galashi a idonshi, sai a gogo daya d’aura a hannushi na silvar ya tsunsa uku sanya da wasu manya-manya azurfa masu kyau da tambari irin na sarauta, wani bak’in takalmi ya sanya a kafarshi mai kyau da tsada, yayi wani mugun kyau sosai, duk wanda ya ganshi bazai gane Sarki! bane sabuda yadda k’uruciyar shi ta futo sosai d’an gemunshi ya kwanta yayi luf a fuskar shi sai shek’i yakeyi, babu wanda zai ganshi yace, shine sai wanda yayi masa farin sani, Turaranshi ya fesa wanda yake amfani dashi me suna (pure love) nan take d’akin ya d’ume gurin da k’amshi a nutse ya futa.
Buba Direba na jingine jikin mota, Sarki! ya futo sai yayi sauri ya b’ude masa motar tun kafin ya karaso, Cikin yanayin muryar shi yace”Malam buba, ba da wannan motar
zamu futa ba”
“Allah ya taimake ka, da wacce zamu futa”?
Wata bak’ar toyota ya nuna masa da hannunsa yace” muje a waccan”
Da sauri Buba Direba ya nufi inda motar take, yana buge ta, duk da tsaf take babu wata kurar arzki a jikinta nan ya bud’e masa ya shiga ya zauna cikin nutsuwa Buba yaja motar suka futa daga gidan.
Comment
Vote and Share
[18/07, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????53
Sai bayan sun futa daga gidan ne, Buba ya d’an waiwayo A hankali yana kallon Sarki! dake kishin gid’e a bayan motar,yace”Allah ya taimake ka,ina muka nufa ne”?
A nutse yace”muje wannan unguwar da mukaje tare da Moddibo kwana uku da suka wuce, Maimartaba ya umarce ni da bunkicen wani abu”
“To masha Allah ranka ya dad’e Allah ya bada sa’a”
Buba ya fad’a yana cigaba da tuk’in mota, a nutse.
Yau da wutar nepa a unguwar sabuda haka ko ina da akwai haske tar, can gefe guda Buba yayi parking din motar, yace”Yallab’ai gamu munzo”
A nutse ya dago kanshi yana bin gurin da kallo, wasu gugun! matasa ya hango sunfi su a shirin a bakin wani kanti, wasu na shan rake wasu na cin gyad’a mai b’awo, yayin da wasu suke cikin a wara, a wata k’atuwar takkada, sai hira ake suna dariya, cike da rashin kamun kai, ya dad’e yana nazirinsu, kafin ya bud’e mota ya futo a nutse, ya gyara zaman gilashin dake fuskarsa, Buba yayi saurin futowa shima, a nutse ya kalleshi yace”ka koma ka zauna cikin mota,Buba bana buk’atar rakiya”
Hannu ya d’aga alamun jinjija yace”a futo lafiya, ranka ya dad’e” ya koma cikin mota kamar yadda a ka umarce shi,
A hankali ya rik’a tsallake kwatoci masu d’auke da dagwalo na k’azanta, har ya k’arasa gurin wad’an nan matasan.
“Assalamu alaikum”
sallama ya fara yi musu, cikin muryarshi mai dad’in sauraro.
Hannu ya mik’a wa na kusa dashi yace”barka da dare abokina”
“Barka kadai” Salihu ya fad’a lokacin da yake mik’a masa hannun sukai gaisa, wani irin taushi yaji lokacin da hannusa ya had’u dana Sarki!
da sauri ya d’ago kanshi yana kallon fuskar Sarki!
gefe guda kuma wani mugun k’amshi ne ya cika musu hanci, shiyasa duk sukayi d’if! suka bar hayaniyar da suke suna kallo Sarki! dake tsaye,hannusa cikin na Salihu,
Gyaran murya yayi yace”Abokina in babu damuwa ina son in maka wasu tambayoyi”
Duk da Sarki! yayi basaja,domin kar a ganeshi, amma muryarshi taso ta tona masa asiri sabuda duk wanda yake cikin garin har in yana sauraron kafofin sadarwa,to muryarshi ba b’oyayyi b’ace mussaman da azimi,da lokacin aikin hajji, akwai wani Maudi’i yake gabatarwa na addini wanda kafafan sadarwa suke sawa kullum, wannan Maudi’i kuwa shi kad’ai yake gabatar dashi sai dai kawai, a tura shi Media, shiyasa Salihu ya furgita jin kamar Muryar Sarki! magajin Sarki, yace”babu komai in sha Allahu zan baka amsar abunda zaka tambaye ni mutukar na sani”